81 Bible Verses About Joy

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Joy
  1. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  2. Waƙar haurawa.

    1 Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona,

    mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

    2 Bakunanmu sun cika da dariya,

    harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.

    Sai ana faɗi a cikin al’ummai,

    “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

    3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,

    mun kuwa cika da farin ciki.

    4 Ka maido da wadatarmu, ya Ubangiji

    kamar rafuffuka a Negeb.

    5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye

    za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

    6 Shi da ya fita yana kuka,

    riƙe da iri don shuki,

    zai dawo da waƙoƙin farin ciki,

    ɗauke da dammuna.

  3. 7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

    9 “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.

  4. 20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku. 23 A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana. 24 Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.

  5. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.

  6. 8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

    9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;

    jikina kuma zai zauna lafiya,

    10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,

    ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

    11 Ka sanar da ni hanyar rai;

    za ka cika ni da farin ciki a gabanka,

    da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  7. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.

  8. 13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

  9. 4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  10. 3 Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali ya ce, 4 “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, sa’an nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasa’in da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba? 5 In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna, 6 ya dawo gida. Sa’an nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’ 7 Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.

    8 “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba? 9 In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’ 10 Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”

  11. 44 “Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.

  12. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  13. 17 Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki, 18 duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.

  14. 17 Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”

    18 Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya. 19 Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku. 20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”

    21 A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.

    22 “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”

  15. 8 Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare. 9 Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai. 10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11 Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.

  16. 6 Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar. 7 Ta haka kuwa kuka zama gurbi ga dukan masu bi a Makidoniya da Akayya.

  17. 1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  18. 13 “Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu. 14 Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne. 15 Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

  19. 12 Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.

  20. 1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.

  21. 17 Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba,

    ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi,

    ko da yake zaitun bai ba da amfani ba,

    gonaki kuma ba su ba da abinci ba,

    ko da yake babu tumaki a garke,

    ba kuma shanu a turaku,

    18 duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji,

    zan yi murna da Allah Mai Cetona.

    19 Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina;

    yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa,

    yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi.

    Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.

  22. 11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  23. 52 Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

  24. 4 Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.

  25. 1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne. 2 Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki. 3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,

  26. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.

  27. 11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;

    bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.

    Ka buɗe kāriyarka a bisansu,

    domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.

  28. 3 Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. 4 A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. 5 Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. 6 Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, 7 da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, 8 ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, 9 mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, 10 cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

  29. 5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  30. 3 Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4 A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

  31. 6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”

    Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.

    7 Ka cika zuciyata da farin ciki

    sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.

    8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,

    gama kai kaɗai, ya Ubangiji,

    kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.

  32. 18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”

    ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

    19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,

    ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

  33. 25 Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa,

    “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannuna na dama,

    ba zan jijjigu ba.

    26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,

    jikina kuma zai kasance da bege,

    27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,

    ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

    28 Ka sanar da ni hanyoyin rai,

    za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’

  34. 15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.

  35. 12 Ka mayar mini farin cikin cetonka

    ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

    13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,

    masu zunubi kuma za su komo gare ka.

  36. 15 Ka gane, ya Ubangiji;

    ka tuna da ni ka kuma lura da ni.

    Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini.

    Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni;

    ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.

    16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;

    suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,

    gama ana kirana da sunanka,

    Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.

  37. 24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

  38. 11 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;

    ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!

  39. Zabura ce. Don yin godiya.

    1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

    2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

    ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

  40. 7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.

  41. 10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;

    raina yana farin ciki a cikin Allahna.

    Gama ya suturce ni da rigunan ceto

    ya yi mini ado da rigar adalci,

    yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist

    kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.

  42. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  43. 22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,

    suka ware ku, suka zage ku,

    suna ce da ku mugaye,

    saboda Ɗan Mutum.

    23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.

  44. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

  45. 41 Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. 42 Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

  46. 1 Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

  47. 17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

  48. 7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;

    zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.

    Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki

    zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

  49. 23 Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai,

    kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!

  50. 2 Mutanen da suke tafiya cikin duhu

    sun ga babban haske;

    a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa

    haske ya haskaka.

    3 Ka fadada al’umma

    ka kuma ƙara farin cikinsu;

    suna farin ciki a gabanka

    yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,

    kamar yadda mutane sukan yi farin ciki

    sa’ad da suke raba ganima.

    4 Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi,

    kuka ji tsoro

    nauyin da ya nawaita musu,

    sandar da yake a kafaɗunsu,

    sandar masu zaluncinsu.

    5 Kowane takalmin jarumin da aka yi amfani da shi a yaƙi

    da kuma kowane rigar da ka naɗe cikin jini

    zai kasance an ƙone shi

    zai kuma zama abin hura wuta.

    6 Gama a gare mu an haifa mana yaro,

    a gare mu an ba da ɗa,

    gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa.

    Za a ce da shi

    Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki

    Uban Madawwami, Sarkin Salama.

    7 Game da girmar gwamnatinsa da salama

    babu iyaka.

    Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa,

    zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya,

    tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani.

    Ubangiji Maɗaukaki ne

    ya yi niyyar aikata wannan duka.

  51. 10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.

    Za su shiga Sihiyona da rerawa;

    matuƙar farin ciki zai mamaye su.

    Murna da farin ciki za su sha kansu,

    baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  52. 14 Ki rera, ya Diyar Sihiyona;

    ki tā da murya, ya Isra’ila!

    Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki,

    Ya Diyar Urushalima!

    15 Ubangiji ya ɗauke hukuncinki,

    ya mai da abokan gābanki baya.

    Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke;

    ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.

    16 A wannan rana za su cewa Urushalima,

    “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;

    kada ki bar hannuwanki su raunana.

    17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

    mai iko ne don ceto.

    Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

    zai rufe ki da ƙaunarsa,

    zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

  53. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

  54. 21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

  55. 27 Ga wannan zancen Yohanna ya amsa ya ce, “Mutum yakan karɓi kawai abin da aka ba shi ne daga sama. 28 Ku kanku za ku shaida cewa na ce, ‘Ba ni ne Kiristi ba, sai dai an aiko ni ne in sha gabansa.’ 29 Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu. 30 Dole ne yă yi ta ƙaruwa, ni kuma in yi ta raguwa.

  56. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau.

  57. 3 Na yi farin ciki ƙwarai sa’ad da waɗansu ’yan’uwa suka zo suka yi zance game da yadda kake da aminci ga gaskiyan nan da kuma yadda kake cin gaba cikin gaskiyan nan. 4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.

  58. 1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

    bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

    2 Bari mu zo gabansa da godiya

    mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

  59. 28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki,

    amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.

  60. 24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

    duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

    25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;

    bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!

  61. 12 Za ku fita da farin ciki

    a kuma bi da ku da salama;

    duwatsu da tuddai

    za su ɓarke da waƙa a gabanku,

    dukan itatuwan jeji kuma

    za su tafa hannuwansu.

    13 A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro,

    a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro.

    Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi,

    madawwamiyar alama ce,

    wadda ba za a datse ba.”

  62. 46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

  63. 6 Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. 7 Suna rawa suna cewa,

    “Shawulu ya kashe dubbansa,

    Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”

  64. 6 Sa’an nan kaina zai ɗaukaka

    a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni;

    a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki;

    zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

  65. 11 Ka mai da kukata ta zama rawa;

    ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

    12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba.

    Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

  66. 10 Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba;

    ban hana zuciyata wani jin daɗi ba.

    Zuciyata ta yi murna da dukan aikina,

    wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.

    11 Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana,

    da abin da na yi fama don in samu,

    sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai;

    babu wata riba a duniya.

  67. 9 Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.

  68. 111 Farillanka su ne gādona har abada;

    su ne farin cikin zuciyata.

  69. 46 Sai Maryamu ta ce,

    “Raina yana ɗaukaka Ubangiji

    47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

    48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.

    Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

    49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,

    sunansa labudda Mai Tsarki ne.

  70. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  71. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

  72. 17 Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18 Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.

  73. 8 Amma game da Ɗan ya ce,

    “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin,

    adalci kuma zai zama sandan mulkinka.

    9 Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;

    saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka,

    ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”

  74. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

    1 Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka.

    Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!

  75. 1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;

    daidai ne masu gaskiya su yabe shi.

    2 Ku yabi Ubangiji da garaya;

    ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.

    3 Ku rera masa sabuwar waƙa;

    ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.

  76. 8 Bari in ji farin ciki da murna;

    bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

  77. 23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki

    sa’ad da na rera yabo gare ka,

    ni, wanda ka fansa.

  78. 22 Zabura Dutsen da magina suka ƙi

    ya zama mai amfani;

    23 Ubangiji ne ya yi haka,

    kuma abu mai daraja ne a idanunmu.

    24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;

    bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.

  79. 8 Kome tsawon rayuwar mutum,

    bari yă more su duka.

    Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu,

    gama su ma za su yi yawa.

    Duk abin da zai faru ba shi da amfani.

    9 Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,

    bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.

    Ka bi shawarar zuciyarka

    da kuma duk abin da idanunka suka gani,

    amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan

    Allah zai shari’anta ka.

  80. 7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

  81. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.