53 Bible Verses About Fear
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
11 “Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
12 Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,
wanda ya riƙe ka da hannun damana
ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;
zan taimake ka.
-
16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.
Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.
19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.
-
6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
-
6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,
2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,
yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,
3 yakan maido da raina.
Yakan bi da ni a hanyoyin adalci
saboda sunansa.
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
-
9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
-
5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
“Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba.”
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?”
-
12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,
amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
-
26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
-
4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
-
3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.
4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo
ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum mai mutuwa zai yi mini?
-
Ta Dawuda.
1 Ubangiji ne haskena da cetona,
wa zan ji tsoro?
Ubangiji ne mafakar raina,
wane ne zan ji tsoro?
2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini
don su cinye ni,
sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,
sun yi tuntuɓe suka fāɗi.
3 Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,
zuciyata ba za tă ji tsoro ba;
ko da yake ya ɓarke a kaina,
duk da haka zan ƙarfafa.
-
26 Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
-
6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.
-
1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,
shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,
“Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;
na kira ka da suna; kai nawa ne.
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;
na bayar da Masar don fansa,
Kush da Seba a maimakonku.
4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,
saboda kuma ina ƙaunarku,
zan ba da mutane a maimakonku,
al’umma kuma domin ranku.
5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;
zan kawo yaranku daga gabas
in kuma tattara ku daga yamma.
-
7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
-
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.
1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,
kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza
duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa
duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela
-
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
Zan yi nasara a kan abokan gābana.
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
15 Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
-
8 Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. 9 Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10 Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11 Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12 Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13 Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
-
4 ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,
“Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;
Allahnku zai zo,
zai zo domin ya ɗau fansa;
da ramuwar Allah
zai zo don yă cece ku.”
5 Sa’an nan idanun makafi za su buɗe
kunnuwan kurame kuma su ji.
6 Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa,
bebaye kuma su yi sowa don farin ciki.
Ruwa zai kwararo daga jeji
rafuffuka kuma a cikin hamada.
7 Yashi mai ƙuna zai zama tafki,
ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka.
A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama,
ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma.
8 Kuma babbar hanya za tă kasance a can;
za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki.
Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba;
za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce;
mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba.
9 Zaki ba zai kasance a can ba,
balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta;
ba za a same su a can ba.
Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can,
10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.
Za su shiga Sihiyona da rerawa;
matuƙar farin ciki zai mamaye su.
Murna da farin ciki za su sha kansu,
baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
-
4 “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7 Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.
8 “Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah. 9 Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah.
-
18 Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa 19 suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”
20 Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
-
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
-
25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?
28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.
-
35 A wannan rana, da yamma, sai ya ce wa almajiransa, “Mu ƙetare zuwa wancan hayi.” 36 Da suka bar taron, sai suka tafi tare da shi yadda yake, a cikin jirgin ruwa. Akwai waɗansu jiragen ruwa kuma tare da shi. 37 Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. 38 Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?”
39 Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, “Shiru! Ku natsu!” Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.
40 Sai ya ce wa almajiransa, “Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”
41 Suka tsorata, suka ce wa juna, “Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!”
-
32 “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.
-
1 Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
-
1 Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,
“Kada ka ji tsoro, Abram.
Ni ne garkuwarka,
kuma ladanka zai zama mai girma.”
-
9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
-
7 Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;
zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.
8 Zuciyarsa tana da kāriya, ba zai ji tsoro ba;
a ƙarshe zai zama mai nasara a kan maƙiyansa.
-
10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
-
25 Jin tsoron mutum tarko ne,
amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
-
28 Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, 29 gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.”
-
22 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.”
-
12 To wane ne mai tsoron Ubangiji?
Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
13 Zai ci kwanakinsa a wadace,
kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa;
yakan sa su san alkawarinsa.
-
1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8 Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
-
17 Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,
da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”
ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
-
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
-
17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. 18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.
-
13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa. 14 Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku; 15 gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.
-
21 Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana.
-
8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
-
13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,
haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
-
1 Yabi Ubangiji.
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
-
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
-
36 Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
-
18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,
-
26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.
Shows Read in context, Share and Copy.