37 Bible Verses About School
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
4 Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 5 Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. 6 Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. 7 Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 8 Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. 9 Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
-
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
-
14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
-
6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
-
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
-
9 Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. 10 Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. 11 Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
-
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
4 Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
za mu faɗa wa tsara mai zuwa
ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,
ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
5 Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila,
wadda ya umarce kakanni-kakanninmu
su koya wa ’ya’yansu,
6 don tsara na biye su san su,
har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba,
su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
7 Ta haka za su dogara ga Allah
ba kuwa za su manta da ayyukansa ba
amma za su kiyaye umarnansa.
8 Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,
masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa,
waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba,
waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
-
7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
-
23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
-
9 Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku. 10 Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”
-
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
-
24 Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba sauran zamanmu a ƙarƙashin Doka.
-
12 Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.
-
2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.
-
9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
-
17 Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.
-
10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
-
6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
-
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
-
11 Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji
kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
12 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,
mutumin da ya sami fahimi,
14 gama ta fi azurfa riba
tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15 Ta fi lu’ulu’u daraja;
ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;
a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,
dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;
waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
-
11 Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda. 12 Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan.
Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki.
-
16 Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17 Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
-
3 “Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.
-
33 Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
-
14 Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, 15 wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. 16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.
-
15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
-
5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi.
-
7 Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
-
20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
-
31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.
-
1 To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.
-
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
-
1 Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali’u da sanyin hali na Kiristi, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” a cikinku, amma “mai matsawa” sa’ad da nake rabe da ku! 2 Ina roƙonku cewa sa’ad da na zo kada ku tilasta ni in matsa muku, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha’anin duniya ne. 3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.
-
11 Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13 yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14 wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.
15 Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka.
Shows Read in context, Share and Copy.