76 Bible Verses About God's Love

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Love
  1. 7 Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8 Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. 9 Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu, Allah ya aiki makaɗaici Ɗansa zuwa duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10 Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. 11 Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12 Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

    13 Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa.

  2. 14 Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”

    16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  3. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

    6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

    9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! 11 Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.

  4. 16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

    Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

    19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko. 20 Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. 21 Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa.

  5. 7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

    9 “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.

  6. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

    an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”

    37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  7. 1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.

  8. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

    4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

    8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare. 9 Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. 10 Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe. 11 Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata. 12 Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.

    13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  9. 36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”

    37 Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40 Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”

  10. 14 Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. 15 Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.

    16 Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. 17 In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? 18 ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

    19 Ta haka muka san cewa mu na gaskiya ne, kuma za mu iya tsaya a gaban Allah ba tare da rawar jiki ba. 20 Idan zuciyarmu ta nuna mana muna da laifi, mun san cewa Allah ya fi zuciyarmu, ya kuma san dukan kome.

  11. 41 In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. 42 Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.

    43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  12. 1 Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba. 2 Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

  13. 11 Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji

    kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

    12 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  14. 21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”

  15. 23 Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.

  16. 15 Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?”

    Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

    Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”

    16 Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?”

    Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.”

    Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”

    17 Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?”

    Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.”

    Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18 Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”

  17. 3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.

  18. 34 “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”

  19. 8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

  20. 3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

    4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

    saboda kuma ina ƙaunarku,

    zan ba da mutane a maimakonku,

    al’umma kuma domin ranku.

    5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;

    zan kawo yaranku daga gabas

    in kuma tattara ku daga yamma.

  21. 17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

    mai iko ne don ceto.

    Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

    zai rufe ki da ƙaunarsa,

    zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

    18 “Zan cire taƙaici daga gare ki

    a ƙayyadaddun bukukkuwa;

    su kaya ne da kuma zargi a gare ki.

    19 A wannan lokaci zan jijji wa

    waɗanda suka danne ku;

    zan kuɓutar da guragu

    in kuma tattara waɗanda suke a warwatse.

    Zan sa a yabe su a kuma girmama su

    a kowace ƙasar da aka kunyatar da su.

    20 A wannan lokaci zan tattara ku;

    a wannan lokaci zan kawo ku gida,

    zan sa a yabe ku a kuma girmama ku

    a cikin dukan mutanen duniya

    a sa’ad da na maido da arzikinku

    a idanunku,”

    in ji Ubangiji.

  22. 14 Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, 15 wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. 16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

  23. 1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

  24. 3 Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa,

    “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna;

    na janye ku da ƙauna marar iyaka.

  25. 27 Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito.

  26. 15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

    ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

    Mai yiwuwa ta manta,

    amma ba zan taɓa manta da ke ba!

    16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;

    katangarki kullum suna a gabana.

  27. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

    31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?

  28. 5 Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,

    “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,

    kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

    6 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

    7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba.

  29. 20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.

  30. 9 Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.

  31. 1 “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi,

    daga Masar kuma na kira ɗana.

    2 Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila

    haka nesa da ni da suke ta yi.

    Suka miƙa hadaya ga Ba’al

    suka kuma ƙona turare ga siffofi.

    3 Ni ne na koya wa Efraim tafiya

    ina kama su da hannu;

    amma ba su gane

    cewa ni ne na warkar da su ba.

    4 Na bishe su da linzamin alheri da tausayi,

    da ragamar ƙauna;

    Na cire karkiya daga wuyansu

    na kuma rusuna na ciyar da su.

  32. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

  33. 22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

    25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani.

  34. 4 Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, 7 wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.

  35. 10 Ko da duwatsu za su girgiza

    a kuma tumɓuke tuddai,

    duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba

    ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,”

    in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.

  36. 23 Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.

  37. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  38. 1 Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2 Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3 Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.

  39. 20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.

  40. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”

  41. 5 Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai,

    amincinka har sararin sammai.

    6 Adalcinka yana kama da manyan duwatsu,

    hukuncinka kamar zurfi mai girma.

    Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.

    7 Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa!

    Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.

  42. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

  43. 15 Amma kai, ya Ubangiji, kai Allah mai tausayi ne da kuma mai alheri,

    mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna da aminci.

  44. 16 Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa. 17 Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”

  45. 26 Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu.”

  46. 14 Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. 15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

    16 Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. 17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!

  47. 1 Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,

    2 “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

    3 “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

    4 Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. 5 Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, 6 amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  48. 8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

    mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

  49. 20 Na tuna su sosai,

    sai kuma na ji ba daɗi a raina.

    21 Duk da haka na tuna da wannan

    na kuma sa bege ga nan gaba.

    22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

    25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,

    ga kuma wanda yake neman shi;

  50. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  51. 7 Ba don kun fi sauran al’ummai yawa ne ya sa Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma zaɓe ku ba, gama ku ne mafi ƙanƙanta cikin dukan al’ummai. 8 Amma ya zama haka domin Ubangiji ya ƙaunace ku, ya kuma kiyaye rantsuwar da ya yi wa kakanninku da ya fitar da ku da hannu mai ƙarfi, ya kuma cece ku daga ƙasar bauta, daga ikon Fir’auna sarkin Masar.

  52. 10 Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11 Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, 12 ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.” 13 Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”

  53. 14 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.

  54. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.

  55. 26 Ku yi godiya ga Allah na sama.

    Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  56. 2 “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji.

    “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’

    “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, 3 amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”

  57. 9 Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni. 10 Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina.

  58. 17 Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne

    cewa in sha irin wahalan nan.

    Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni

    daga ramin hallaka;

    ka sa dukan zunubaina

    a bayanka.

  59. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  60. 9 Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu,

    mala’ikan da yake gabansa ya cece su.

    Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su;

    ya kuma ɗaga su ya riƙe su

    dukan kwanakin dā

  61. 31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,

    “sa’ad da zan yi sabon alkawari

    da gidan Isra’ila

    da kuma gidan Yahuda.

    32 Ba zai zama kamar alkawarin

    da na yi da kakanni kakanninsu ba

    sa’ad da na kama su da hannu

    na bishe su daga Masar,

    domin sun take alkawarina,

    ko da yake na zama miji a gare su,”

    in ji Ubangiji.

    33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

    bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.

    “Zan sa dokata a tunaninsu

    in kuma rubuta ta a zukatansu.

    Zan zama Allahnsu,

    za su kuma zama mutanena.

    34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

    ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’

    domin duk za su san ni,

    daga ƙaraminsu har zuwa babba,”

    in ji Ubangiji.

    “Gama zan gafarta muguntarsu

    ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

    35 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya kafa rana

    don tă yi haske a yini

    shi da ya sa wata da taurari

    su yi haske da dare,

    shi da yake dama teku

    don raƙuman ruwansa su yi ruri

    Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  62. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  63. 9 Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

    11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. 12 Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. 13 Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.

    14 “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, 15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin. 16 Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma. 17 Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. 18 Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”

  64. 11 A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.

  65. 16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege,

  66. 5 da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya.

    Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa,

  67. 5 Ubangiji yana ƙaunar adalci

    duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.

  68. 28 Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai

    kuma ba zai yashe amintattunsa ba.

    Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,

    ’ya’yan mugaye za su hallaka.

  69. 26 Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna;

    ka cece ni bisa ga ƙaunarka.

  70. 8 Cikin fushi mai zafi

    na ɓoye fuskata daga gare ki na ɗan lokaci,

    amma da madawwamin alheri

    zan ji tausayinki,”

    in ji Ubangiji Mai Fansarki.

  71. 8 “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;

    na ƙi fashi da aikata laifi.

    Cikin adalcina zan sāka musu

    in kuma yi madawwamin alkawari da su.

  72. 13 Ku kyakkece zuciyarku

    ba rigunanku ba.

    Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

    gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

    mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

    yakan kuma janye daga aika da bala’i.

  73. 5 Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

  74. 10 Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya. 11 Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.”

  75. 21 Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, 22 Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”

  76. 15 Gama ya ce wa Musa,

    “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,

    zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”

    16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah.