41 Bible Verses About Discipline

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Discipline
  1. 5 Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,

    “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,

    kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

    6 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

    7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9 Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10 Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

    12 Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi! 13 “Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke.

  2. 24 Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. 25 Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. 26 To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. 27 A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  3. 11 Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji

    kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

    12 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  4. 4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

  5. 15 Sandar gyara kan ba da hikima,

    amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.

    16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa,

    amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.

    17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;

    zai ba ka farin cikin da kake so.

  6. 24 Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,

    amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.

  7. 15 Wauta tana da yawa a zuciyar yara,

    amma sandar horo zai kore ta nesa da su.

  8. 13 Kada ka bar yaro ba horo;

    in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.

    14 Ka hukunta shi da sanda

    ka ceci ransa daga mutuwa.

    15 Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce,

    to, zuciyata za tă yi murna;

    16 cikin cikina zai yi farin ciki

    in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.

  9. 6 In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. 7 Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. 8 Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa. 9 Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. 10 Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

  10. 1 Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,

    amma duk mai ƙin gyara wawa ne.

  11. 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

  12. 5 Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.

    6 Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.

  13. 20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

    21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;

    ka ɗaura su kewaye da wuyanka.

    22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;

    sa’ad da kake barci, za su lura da kai;

    sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.

    23 Gama waɗannan umarnai fitila ne,

    wannan koyarwa haske ne,

    kuma gyare-gyaren horo

    hanyar rayuwa ce,

  14. 6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  15. 17 “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure;

    saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

    18 Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon;

    ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.

  16. 12 Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji,

    mutumin da ka koyar daga dokarka;

    13 kana ba shi sauƙi a lokacin wahala,

    sai har an haƙa rami wa mugaye.

    14 Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba;

    ba zai taɓa yashe gādonsa ba.

  17. 18 Ka hori ɗanka, gama yin haka akwai sa zuciya;

    kada ka goyi baya lalacewarsa.

  18. 1 Ana ba da labari cewa ana lalata a cikinku, irin da ba a ma samu a cikin masu bautar gumaka. Har mutum yana kwana da matar mahaifinsa. 2 Har ya zama muku abin taƙama! Ashe, bai kamata ku cika da baƙin ciki ku kuma daina zumunci da mutumin da yake aikata wannan ba? 3 Ko da yake ba na nan tare da ku cikin jiki, ina tare da ku a cikin ruhu. Na riga na yanke wa wanda ya aikata wannan hukunci, kamar dai ina tare da ku. 4 Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku. 5 Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.

  19. 14 In wani bai yi biyayya da umarninmu a wannan wasiƙa ba, sai fa ku lura da shi. Kada ku haɗa kai da shi, don yă ji kunya. 15 Duk da haka kada ku mai da shi abokin gāba, sai dai ku gargaɗe shi a matsayin ɗan’uwa.

  20. 19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.

  21. 18 Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau, 19 kana riƙe da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu. 20 Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.

  22. 19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. 21 Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.

    22 Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.

  23. 6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,

    kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

  24. 15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

  25. 2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

    don ganewa kalmomi masu zurfi;

    3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

    kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

    4 don sa marar azanci yă yi hankali,

    yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

    5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

    bari masu tunani kuma su sami jagora,

    6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,

    kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

    7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

    amma wawaye sun rena hikima da horo.

    Gargaɗi don a rungumi hikima

    8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  26. 1 Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,

    amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.

  27. 18 Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya,

    amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.

  28. 31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. 32 Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.

  29. 1 ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. 2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. 3 In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. 4 Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, 5 gama kowa zai ɗauki kayansa.

  30. 10 Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su

    su tuba daga muguntarsu.

  31. 17 Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai,

    amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

  32. 2 Ku tuna a yau, cewa ’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko; 3 alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba; 4 ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba. 5 Ba ’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba, 6 ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram, ’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba. 7 Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.

  33. 75 Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne,

    kuma cikin aminci ka hore ni.

  34. 23 Zai mutu saboda rashin ɗa’a

    yawan wawancinsa zai sa yă kauce.

  35. 32 Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan,

    amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.

  36. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  37. 17 Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18 Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.

  38. 9 Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata. 10 Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. 11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. 12 Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta. 13 Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”

  39. 1 Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.” 2 Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan,

  40. 10 Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. 11 Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.

  41. 17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.