49 Bible Verses About Trusting God
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya
yă kuma adana ƙasusuwanka.
-
1 Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. 2 Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan.
3 Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.
-
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19 don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
20 Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
-
4 Amma gumakansu azurfa da zinariya ne,
da hannuwan mutane suka yi.
5 Suna da bakuna, amma ba sa magana,
idanu, amma ba sa gani;
6 suna da kunnuwa, amma ba sa ji,
hanci, amma ba sa jin ƙanshi
7 suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome,
ƙafafu, amma ba sa iya tafiya;
ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.
8 Masu yinsu za su zama kamar su,
haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.
9 Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
10 Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
11 Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
12 Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu.
Zai albarkace gidan Isra’ila,
zai albarkace gidan Haruna,
13 zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji,
manya da ƙanana duka.
14 Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru,
da ku da ’ya’yanku.
-
23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
-
16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.
-
5 Ku miƙa hadayun da suka dace
ku kuma dogara ga Ubangiji.
-
Ta Dawuda.
1 A gare ka Ya Ubangiji,
na miƙa raina.
2 A gare ka na dogara, ya Allahna.
Kada ka bari in sha kunya,
ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
-
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai yi mini?
7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.
Zan yi nasara a kan abokan gābana.
8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga sarakuna.
-
5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,
wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi
wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;
ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.
Za su zauna a busassun wuraren hamada,
a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.
Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;
ganyayensa kullum kore suke.
Ba shi da damuwa a shekarar fări
ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah.
-
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
-
17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.
-
30 Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce;
maganar Ubangiji marar kuskure ne.
Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
-
15 Idanuna kullum suna a kan Ubangiji,
gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
16 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
gama na kaɗaice ina kuma wahala.
17 Damuwoyin zuciyata sun ninka;
ka ’yantar da ni daga wahalata.
18 Ka dubi wahalata da kuma azabata
ka ɗauke mini dukan zunubaina.
19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru
da kuma yadda suka ƙara ƙina!
20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
-
3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,
waƙar yabo ga Allahna.
Da yawa za su gani su tsorata
su kuma dogara ga Ubangiji.
4 Mai albarka ne mutumin
da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,
wanda ba ya kula da masu girman kai,
waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
-
48 Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.
-
6 Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi), 7 “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu). 8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. 9 Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka.
-
8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.
-
15 Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.
16 Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, 17 yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
-
17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.
-
23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
-
2 Ya ce,
“Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;
3 Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.
Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.
Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa tsira daga abokan gābana.
5 Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;
raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
-
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
-
5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;
zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
6 Zan rera ga Ubangiji
gama ya yi mini alheri.
-
5 Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara
mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu.
Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
6 Yanzu na san cewa,
Ubangiji yakan cece shafaffensa.
Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki
da ikon ceto na hannun damansa.
7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,
amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
-
3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda.
1 Ka ji kukata, ya Allah;
ka saurari addu’ata.
2 Daga iyakar duniya na yi kira gare ka,
na yi kira yayinda zuciyata ta karai;
ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.
3 Gama kai ne mafakata,
hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.
4 Ina marmari in zauna a tentinka har abada
in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
-
5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
dogarata kan zo daga gare shi ne.
6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,
shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,
gama Allah ne mafakarmu. Sela
-
ו Waw
41 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji,
cetonka bisa ga alkawarinka;
42 sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina,
gama na dogara ga maganarka.
43 Kada ka ƙwace maganarka daga bakina,
gama na sa zuciyata a dokokinka.
44 Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka,
har abada abadin.
45 Zan yi ta yawo a sake
gama na nemi farillanka.
-
3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna,
ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.
4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa;
a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.
5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,
wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.
6 Mahaliccin sama da ƙasa,
teku, da kome da yake cikinsu,
Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.
7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne
ya kuma ba da abinci ga mayunwata.
Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,
-
22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
-
4 Ku dogara ga Ubangiji,
gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
-
10 Wane ne a cikinku yake tsoron Ubangiji
yana kuma yin biyayya ga maganar bawansa?
Bari wanda yake tafiya cikin duhu,
wanda ba shi da haske,
ya dogara a sunan Ubangiji ya kuma dogara ga Allahnsa.
-
36 Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
-
22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah.
-
43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
-
31 Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”
-
8 Kirisbus, shugaban majami’a, da dukan iyalinsa suka gaskata Ubangiji; Korintiyawa masu yawa kuwa da suka ji shi suka gaskata, aka kuwa yi musu baftisma.
-
16 Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai. 17 Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
-
20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?
-
14 To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? 15 Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”
16 Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?” 17 Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.
-
9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
-
7 Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. 8 Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi 9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. 10 Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, 11 yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
-
6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
-
10 Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
-
7 Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8 Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
-
6 In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
-
10 Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.
Shows Read in context, Share and Copy.