108 Bible Verses About Praising God

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Praising God
  1. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;

    yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

    2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;

    yabe shi saboda mafificin girmansa.

    3 Yabe shi da ƙarar kakaki,

    yabe shi da garaya da molo,

    4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,

    yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

    5 yabe shi da kuge mai ƙara,

    yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

    6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji.

  2. Ta Dawuda.

    1 Yabi Ubangiji, ya raina;

    dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

    2 Yabi Ubangiji, ya raina,

    kada kuma ka manta dukan alheransa,

    3 wanda yake gafarta dukan zunubai

    yake kuma warkar da dukan cututtuka,

    4 wanda ya fanshi ranka daga rami

    ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,

    5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau

    domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.

  3. 15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.

  4. Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi.

    1 Zan gode wa Ubangiji kullayaumi;

    yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.

    2 Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji;

    bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.

    3 Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni;

    bari mu ɗaukaka sunansa tare.

    4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;

    ya cece ni daga dukan tsoro.

  5. 6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi.

    A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,

    “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki

    shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’

    wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

    9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,

    11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

    ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

    domin ka halicci dukan abubuwa,

    kuma ta wurin nufinka aka halicce su

    suka kuma kasance.”

  6. 6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,

    gama ya ji kukata na neman jinƙai.

    7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;

    zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.

    Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki

    zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

  7. 3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,

    leɓunana za su ɗaukaka ka.

    4 Zan yabe ka muddin raina,

    kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

    5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;

    da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.

    6 A gadona na tuna da kai;

    ina tunaninka dukan dare.

  8. Zabura ce. Don yin godiya.

    1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

    2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

    ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

    3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

    Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

    mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

    4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya

    filayen gidansa kuma da yabo;

    ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

    5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;

    amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

  9. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.

  10. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

    21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

  11. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji daga sammai,

    yabe shi a bisa sammai.

    2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,

    yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

    3 Yabe shi, rana da wata,

    yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

    4 Yabe shi, ku bisa sammai

    da kuma ku ruwan bisa sarari.

    5 Bari su yabi sunan Ubangiji,

    gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  12. 22 Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. 23 Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. 24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

    25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.

  13. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

    15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

  14. 1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;

    ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.

    2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;

    ku yi shelar cetonsa kowace rana.

    3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

    manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

    4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;

    tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

    5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

    amma Ubangiji ne ya yi sammai.

    6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

    ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.

    7 Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai

    ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.

    8 Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;

    ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.

    9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;

    ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.

  15. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi sunan Ubangiji;

    yabe shi, ku bayin Ubangiji,

    2 ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji,

    cikin filayen gidan Allahnmu.

    3 Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne;

    rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.

    4 Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa,

    Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.

  16. 3 Suka sāke tā da murya suka ce,

    “Halleluya!

    Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”

    4 Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce,

    “Amin, Halleluya!”

    5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,

    “Ku yabi Allahnmu,

    dukanku da kuke bayinsa,

    ku da kuke tsoronsa,

    babba da yaro!”

    6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,

    “Halleluya!

    Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

    7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna

    mu kuma ɗaukaka shi!

    Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,

    amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

  17. 33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,

    za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,

    gama ya zo don yă hukunta duniya.

    34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;

    ƙaunarsa madawwamiya ce.

    35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;

    tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,

    don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,

    don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”

    36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    daga madawwami zuwa madawwami.

    Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”

  18. 5 Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.”

    “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo. 6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

    7 “Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim. 8 Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne.

  19. 1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;

    daidai ne masu gaskiya su yabe shi.

    2 Ku yabi Ubangiji da garaya;

    ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.

    3 Ku rera masa sabuwar waƙa;

    ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.

    4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;

    yana da aminci cikin kome da yake yi.

    5 Ubangiji yana ƙaunar adalci

    duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.

  20. 1 Yabi Ubangiji.

    Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji,

    ku yabi sunan Ubangiji.

    2 Bari a yabi sunan Ubangiji,

    yanzu da har abada kuma.

    3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa,

    a yabi sunan Ubangiji.

  21. Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.

    1 Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;

    zan yabi sunanka har abada abadin.

    2 Kowace rana zan yabe ka

    in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

    3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo

    girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

    4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;

    za su yi magana game da manyan ayyukanka.

  22. 15 Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana,

    bakina kuwa zai furta yabonka.

  23. 1 Yabi Ubangiji, ya raina.

    Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai;

    kana saye da daraja da ɗaukaka.

  24. 10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. 11 Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. 12 Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”

    13 Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,

    14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,

    a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”

  25. 30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa

    in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.

    31 Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya,

    fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.

  26. 33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;

    zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.

    34 Bari tunanina yă gamshe shi,

    yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.

    35 Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya

    mugaye kuma kada a ƙara ganinsu.

    Yabi Ubangiji, ya raina.

    Yabi Ubangiji.

  27. 1 Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka,

    gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki,

    abubuwan da aka shirya tun da.

  28. 1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;

    bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.

    2 Bari mu zo gabansa da godiya

    mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

    3 Gama Ubangiji Allah mai girma ne,

    babban Sarki a bisa dukan alloli.

    4 A hannunsa ne zurfafan duniya suke,

    ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.

    5 Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,

    da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

    6 Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,

    bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;

    7 gama shi ne Allahnmu

    mu mutanen makiyayansa ne,

    garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

    Yau, in kuka ji muryarsa,

  29. 9 Suka rera sabuwar waƙa,

    “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin

    ka kuma buɗe hatimansa,

    domin an kashe ka,

    da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,

    daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.

    10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,

    kuma za su yi mulki a duniya.”

    11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,

    “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,

    don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi

    da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”

    13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,

    “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon

    yabo da girma da ɗaukaka da iko,

    sun tabbata har abada abadin!”

    14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.

  30. Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda.

    1 Zan girmama ka Ya Ubangiji,

    gama ka tsamo ni daga zurfafa

    ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

    2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako

    ka kuwa warkar da ni.

    3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;

    ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

    4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;

    ku yabi sunansa mai tsarki.

    5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  31. 5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,

    ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

    6 Daga haihuwa na dogara gare ka;

    kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.

    Kullayaumi zan yabe ka.

    7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,

    amma kai ne katangata mai ƙarfi.

    8 Bakina ya cika da yabonka,

    ina furta darajarka dukan yini.

  32. 8 A cikin alloli babu kamar ka, ya Ubangiji;

    babu ayyukan da za a kwatanta da naka.

    9 Dukan al’umman da ka yi

    za su zo su yi sujada a gabanka, ya Ubangiji;

    za su kawo ɗaukaka ga sunanka.

    10 Gama kai mai girma ne kana kuma aikata ayyuka masu banmamaki;

    kai kaɗai ne Allah.

    11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,

    zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;

    ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,

    don in ji tsoron sunanka.

    12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;

    zan ɗaukaka sunanka har abada.

    13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni;

    kai ka cece ni daga zurfafa,

    daga mazaunin matattu.

  33. 1 Yabi Ubangiji.

    Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata

    a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.

    2 Ayyukan Ubangiji da girma suke;

    dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.

    3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne,

    adalcinsa kuma zai dawwama har abada.

    4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;

    Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.

    5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa;

    yakan tuna da alkawarinsa har abada.

  34. 9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  35. 1 Yabi Ubangiji.

    Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi;

    ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

    2 Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji

    ko yă furta cikakken yabonsa?

  36. 8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa

    da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,

    9 gama yana shayar da masu ƙishirwa

    yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.

  37. 10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

    ku yi yabonsa daga iyakar duniya,

    ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,

    ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.

    11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;

    bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.

    Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;

    bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.

    12 Bari su ɗaukaka Ubangiji

    su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.

  38. 68 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

    69 Ya tā mana ƙahon ceto

    a gidan bawansa Dawuda

  39. 9 Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10 Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,

    “Ceto na Allahnmu ne,

    wanda yake zaune a bisan kursiyi,

    da kuma na Ɗan Ragon.”

    11 Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12 suna cewa,

    “Amin!

    Yabo da ɗaukaka,

    da hikima da godiya da girma

    da iko da ƙarfi

    sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.

    Amin!”

  40. Zabura ta Dawuda.

    1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya,

    ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

    2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa;

    ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

  41. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura.

    1 Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

    2 Ku rera ɗaukaka ga sunansa;

    ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

    3 Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke!

    Ikonka da girma yake

    har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

    4 Dukan duniya sun rusuna a gabanka

    suna rera yabo gare ka,

    suna rera yabo ga sunanka.” Sela

  42. Ta Dawuda.

    1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;

    a gaban “alloli” zan rera yabo.

    2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki

    zan kuma yabi sunanka

    saboda ƙaunarka da amincinka,

    saboda ka ɗaukaka a bisa kome

    sunanka da kuma maganarka.

  43. 1 Yabi Ubangiji.

    Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,

    abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!

  44. 37 Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,

    38 “Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”

    “Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”

  45. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

    1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;

    ya juya wurina ya kuma ji kukata.

    2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,

    daga laka da taɓo;

    ya sa ƙafafuna a kan dutse

    ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.

    3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,

    waƙar yabo ga Allahna.

    Da yawa za su gani su tsorata

    su kuma dogara ga Ubangiji.

  46. 4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,

    ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;

    5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,

    da garaya da ƙarar rerawa,

    6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,

    ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.

  47. 3 Suna kiran juna,

    “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;

    duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

  48. 19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. 20 Ya ce,

    “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;

    hikima da iko nasa ne.

    21 Yana sāke lokuta,

    yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.

    Yana ba da hikima ga masu hikima

    kuma ilimi ga masu basira.

    22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;

    ya san abin da yake cikin dare,

    haske kuwa yana zaune tare da shi.

    23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.

    Kai ka san hikima da iko,

    ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

  49. 2 Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,

    “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,

    ya Ubangiji Maɗaukaki.

    Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,

    ya Sarkin zamanai.

    4 Wane ne ba zai ji tsoronka,

    yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?

    Gama kai kaɗai ne mai tsarki.

    Dukan al’ummai za su zo

    su yi sujada a gabanka,

    gama an bayyana ayyukan adalcinka.”

  50. 9 Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.

    10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa,

    “Yabo gare ka, ya Ubangiji,

    Allah na mahaifinmu Isra’ila,

    har abada abadin.

    11 Girma da iko

    da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,

    gama kome a sama da ƙasa naka ne.

    Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;

    an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.

    12 Wadata da girma daga gare ka suke;

    kai ne mai mulkin dukan abubuwa.

    A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke

    don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.

    13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka,

    muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.

  51. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda.

    1 Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;

    zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.

    2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;

    zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.

  52. 13 Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka;

    za mu rera mu kuma yabi ikonka.

  53. 3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan;

    kai ne yabon Isra’ila.

  54. 28 Harshena zai yi zancen adalcinka

    da kuma yabonka dukan yini.

  55. 7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,

    zuciyata tana nan daram;

    zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.

    8 Ka farka, raina!

    Ku farka, garaya da molo!

    Zan sa safe yă farka.

    9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

    zan rera game da kai a cikin mutane.

    10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;

    amincinka na kaiwa sarari.

    11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;

    bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.

  56. 19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama,

    masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.

    20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,

    ku jarumawa masu yi masa aiki,

    waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

    21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,

    ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.

    22 Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa

    ko’ina a mulkinsa.

    Yabi Ubangiji, ya raina.

  57. 47 Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu,

    ka kuma tattara mu daga al’ummai,

    don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya

    mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.

    48 Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    daga madawwami zuwa madawwami.

    Bari dukan mutane su ce, “Amin!”

    Yabo ga Ubangiji.

  58. 23 Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka;

    ku yi shelar cetonsa kowace rana.

    24 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,

    ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

    25 Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;

    dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.

    26 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,

    amma Ubangiji ya yi sammai.

    27 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;

    ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.

    28 Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,

    ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,

    29 ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.

    Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa;

    ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.

  59. Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.

    1 Yana da kyau a yabi Ubangiji

    a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

    2 don a yi shelar ƙaunarka da safe

    amincinka kuma da dare,

    3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma

    da kuma ƙarar garaya.

  60. 20 Namun jeji suna girmama ni,

    diloli da mujiyoyi ma haka,

    domin na tanada musu ruwa a hamada

    da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa,

    don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,

    21 mutanen da na yi saboda kaina

    don su furta yabona.

  61. 10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;

    raina yana farin ciki a cikin Allahna.

    Gama ya suturce ni da rigunan ceto

    ya yi mini ado da rigar adalci,

    yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist

    kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.

    11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu

    lambu kuma ya sa iri ya yi girma,

    haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo

    su tsiro a gaban dukan al’ummai.

  62. 11 sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa,

    “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki,

    gama Ubangiji mai alheri ne;

    ƙaunarsa za tă dawwama har abada.”

    Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.

  63. 34 A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada.

    Mulkinsa dawwammamen mulki ne;

    sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani.

    35 Dukan mutanen duniya

    ba a bakin kome suke ba.

    Yakan yi abin da ya gamshe shi

    da ikokin sama

    da kuma na mutanen duniya.

    Babu mai hana shi

    ko yă ce masa; “Me ka yi?”

    36 A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. 37 Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.

  64. 52 Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai. 53 Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

  65. 42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. 43 Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. 44 Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. 45 Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. 46 Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, 47 suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

  66. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.

  67. 24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

  68. 21 Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.

  69. 4 “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,

    na kuwa tsira daga abokan gābana.

  70. 46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena!

    Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona!

    47 Shi ne Allah mai sāka mini,

    wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina,

    48 wanda yakan cece ni daga abokan gābana.

    Ana girmama ka bisa abokan gābana;

    daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni.

  71. 22 Zan furta sunanka ga ’yan’uwana;

    cikin taron masu sujada zan yabe ka.

    23 Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!

    Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!

    Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!

  72. 16 Amma zan rera game da ƙarfinka,

    da safe zan rera game da ƙaunarka;

    gama kai ne mafakata,

    kagarata a lokacin wahala.

    17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;

    kai, ya Allah, kai ne kagarata,

    Allah mai ƙaunata.

  73. 5 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

    ku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;

    shi mai tsarki ne.

    6 Musa da Haruna suna cikin firistocinsa,

    Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa;

    sun kira ga Ubangiji

    ya kuwa amsa musu.

    7 Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije;

    ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.

    8 Ya Ubangiji Allahnmu,

    ka amsa musu;

    ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa,

    ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.

    9 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmu

    ku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki,

    gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.

  74. 1 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi;

    ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

    2 Bari Isra’ila yă ce,

    “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

    3 Bari gidan Haruna yă ce,

    “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

    4 Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce,

    “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  75. 1 Yabi Ubangiji.

    Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,

    yabonsa a cikin taron tsarkaka.

  76. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  77. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.

  78. 20 Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka

    wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.”

    Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.

  79. 56 “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.

  80. 13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera,

    “Yana da kyau;

    ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

    Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije, 14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.

  81. 21 Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa,

    “Ku yi godiya ga Ubangiji,

    gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

  82. 10 Da masu ginin suka aza harsashin ginin haikalin Ubangiji, sai firistoci suka sa kayansu na firistoci suka riƙe ƙahonin busa, Lawiyawa (’ya’yan Asaf) kuwa suka riƙe kuge, suka yi shiri domin su rera yabo ga Ubangiji kamar yadda Dawuda Sarkin Isra’ila ya ba da umarni. 11 Suka rera waƙar yabo da godiya ga Ubangiji, suna cewa,

    “Shi nagari ne;

    ƙaunarsa kuwa ga Isra’ila har abada ce.”

    Dukan jama’a kuwa suka yabi Ubangiji da murya mai ƙarfi, domin an aza harsashin ginin gidan Ubangiji.

  83. 2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

    Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka.

    Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.

    3 Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,

    na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.

  84. 6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;

    ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.

    7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;

    ku rera zabura ta yabo gare shi.

    8 Allah yana mulki a bisa al’ummai;

    Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

  85. 14 Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya;

    zan yabe ka sau da sau.

    15 Bakina zai ba da labarin adalcinka,

    zai yi maganar cetonka dukan yini,

    ko da yake ban san yawansa ba.

  86. Maskil na Etan dangin Ezra.

    1 Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada;

    da bakina zan sanar da amincinka

    a dukan zamanai.

  87. 14 Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki;

    daga yamma sun furta darajar Ubangiji.

    15 Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji,

    a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila,

    a cikin tsibiran teku.

  88. 33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

    Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

    hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

    34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

    Ko kuwa yă ba shi shawara?”

    35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,

    da Allah zai sāka masa?”

    36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

    Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

  89. 11 Wane ne cikin alloli,

    ya yi kamar ka, ya Ubangiji?

    Wane ne kamar ka,

    mai ɗaukaka cikin tsarki,

    mai banrazana cikin ɗaukaka,

    mai aikata al’ajabai?

  90. 10 “Yabo ga Ubangiji wanda ya cece ku daga hannun Masarawa da na Fir’auna, wanda kuma ya cece mutanensa daga hannun Masarawa.

  91. 6 Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.

  92. 17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa

    zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

  93. 13 Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini!

    Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,

    14 don in furta yabanka

    cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona

    a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.

  94. 1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

    ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.

    2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;

    ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.

    3 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki;

    bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.

    4 Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;

    ku nemi fuskarsa kullum.

    5 Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi,

    mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,

  95. 21 Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.

    Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki

    har abada abadin.

  96. 21 Sai Yesu ya ce, “Uwargida, ina tabbatar miki, lokaci yana zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ko a dutsen nan, ko kuwa a Urushalima ba. 22 Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema. 24 Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

  97. 1 Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce,

    “Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka. 2 Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi. 3 Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko. 4 Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni.

  98. 11 Da kuma,

    “Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai,

    ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”

  99. 1 Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,

    “Zan rera waƙa ga Ubangiji

    gama an ɗaukaka shi ƙwarai.

    Doki da mahayinsa

    ya jefa su cikin teku.

    2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,

    ya zama cetona.

    Shi Allahna ne, zan yabe shi.

    Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.

  100. 50 Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai;

    Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.

  101. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce.

    1 Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai;

    ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

  102. 8 Ku yabi Allahnku, ya mutane,

    bari a ji ƙarar yabonsa;

  103. 1 Yabi Ubangiji, dukanku al’umma;

    ku ɗaukaka shi, dukanku mutane.

  104. 164 Sau bakwai a rana ina yabonka

    saboda dokokinka masu adalci.

  105. 19 Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji;

    Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;

    20 Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji;

    ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.

    21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona,

    gare shi wanda yake zama a Urushalima.

    Yabi Ubangiji.

  106. 1 Yabi Ubangiji.

    Yabi Ubangiji, ya raina.

    2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina;

    zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

  107. 31 Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa. 32 In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.

  108. 11 Sane da wannan, kullum muna addu’a saboda ku, don Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ta wurin ikonsa kuma yă cika kowace manufarku mai kyau da kuma kowane aikin da bangaskiyarku ta iza. 12 Muna wannan addu’a don sunan Ubangijinmu Yesu yă sami ɗaukaka a cikinku, ku kuma a cikinsa, bisa ga alherin Allahnmu da na Ubangiji Yesu Kiristi.