77 Bible Verses About Missions
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
16 Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17 Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
-
1 A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. 2 Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3 Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
4 Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. 5 Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.
-
11 Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” 12 Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, 13 gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
14 To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? 15 Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”
-
4 A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5 Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
6 Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”
7 Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. 8 Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”
-
15 Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta. 16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka. 17 Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna. 18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”
-
44 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”
45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. 46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49 Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”
-
2 Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya. 3 Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. 4 Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. 5 Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. 6 Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.
-
1 Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga. 2 Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3 Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai.
-
35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. 37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”
-
19 Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” 20 Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.
21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”
-
36 Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.” 37 Barnabas ya so Yohanna, wanda ake kira Markus ya tafi tare da su, 38 amma Bulus bai ga ya kyautu ya tafi da shi ba, domin ya yashe su a Famfiliya bai kuwa ci gaba tare da su a aikin ba. 39 Suka sami saɓanin ra’ayi tsakaninsu har suka rabu. Barnabas ya ɗauki Markus suka shiga jirgin ruwa zuwa Saifurus, 40 amma Bulus ya zaɓi Sila suka kuwa tashi, bayan ’yan’uwa suka danƙa su ga alherin Ubangiji. 41 Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.
-
8 Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”
Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
9 Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,
“ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;
Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
10 Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;
kunnuwansu su kurunce,
idanunsu kuma su makance.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta da zuciyarsu,
su kuma juyo a kuma warkar da su.”
11 Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?”
Ya kuma amsa,
“Sai an lalatar da biranen
ba kowa a ciki,
sai an mai da gidaje kangwaye
ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,
12 sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa
aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.
-
6 Saboda haka mutanena za su san sunana;
saboda haka a wannan rana za su san
cewa ni ne wanda ya faɗa wannan.
I, ni ne.”
7 Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu
a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi
waɗanda suke shelar salama,
waɗanda suke kawo labari mai daɗi,
waɗanda suke shelar ceto,
waɗanda suke ce wa Sihiyona,
“Allahnki yana mulki!”
8 Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu;
tare sun yi sowa ta farin ciki.
Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona,
za su gan shi da idanunsu.
9 Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,
kangonki na Urushalima,
gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,
ya fanshi Urushalima.
10 Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili
a idanun dukan al’ummai,
da kuma dukan iyakokin duniya za su gani
ceton Allahnmu.
-
19 To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai. 20 Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu. 21 Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.
22 Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok. 23 Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.
-
14 Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
-
5 Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya. 6 Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni. 7 Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda. 8 Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos, 9 domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
-
7 A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa. 8 Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai. 9 Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa. 10 Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
-
7 Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.
8 Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9 Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10 Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11 In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”
-
14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba. 17 Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka. 18 Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.
19 Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku. 20 Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.
-
17 Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
18 Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. 19 Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. 20 Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
-
18 Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata 19 ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. 20 Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. 21 Sai dai kamar yadda yake a rubuce,
“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,
waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”
-
1 Bayan haka, Bulus ya bar Atens ya tafi Korint. 2 A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su, 3 da yake shi ma mai ɗinkin tenti ne kamar su, sai ya zauna ya yi aiki tare da su. 4 Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.
-
1 Ubangiji ya ce wa Abram, “Tashi ka bar ƙasarka, da mutanenka, da iyalin mahaifinka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.
2 “Zan mai da kai al’umma mai girma,
zan kuma albarkace ka;
zan sa sunanka yă zama mai girma,
ka kuma zama sanadin albarka.
3 Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka,
in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka,
dukan mutanen duniya
za su sami albarka ta wurinka.”
-
1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
-
13 “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
14 “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15 Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16 Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
-
1 Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. 2 Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3 Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu. 4 Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin. 5 In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 6 Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.
-
37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40 Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” 41 Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
42 Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.
-
4 Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi. 5 Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6 Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7 Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8 Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
-
47 Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,
“ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai,
don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”
-
26 Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu. 27 Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.
-
4 Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye. 5 Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.
6 Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya. 7 Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. 8 Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. 9 Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” 10 Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.
-
12 “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci. 13 Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata. 14 Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’
15 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’
“Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’
-
18 Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, 19 wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. 20 Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. 21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
-
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;
bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.
Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;
bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
12 Bari su ɗaukaka Ubangiji
su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
-
1 Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai;
ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa.
Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni;
tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
2 Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi,
cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni;
ya sa na zama kamar kibiya mai tsini
ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.
3 Ya ce mini, “Kai bawana ne,
Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”
4 Amma na ce, “Na yi aiki a banza;
na kashe duk ƙarfina a banza da wofi.
Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji,
ladana kuma tana a wurin Allahna.”
5 Yanzu fa Ubangiji ya ce
ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa
don in dawo da Yaƙub gare shi
in kuma tattara Isra’ila gare shi,
gama an girmama ni a gaban Ubangiji
Allahna kuma ne ƙarfina
6 ya ce,
“Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana
don ka maido da kabilar Yaƙub
ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye.
Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai,
don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
-
1 Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu. 2 “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”
-
23 Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
1 Ina fata za ku yi haƙuri da ’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri. 2 Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla. 3 Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. 4 Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai. 5 Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba. 6 Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.
7 Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta? 8 Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima. 9 Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama ’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka. 10 Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa. 11 Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!
12 Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su. 13 Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. 14 Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. 15 Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
-
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
-
1 Maganar Ubangiji ta zo wa Yunana ɗan Amittai cewa, 2 “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”
3 Amma Yunana ya gudu daga Ubangiji ya nufi Tarshish. Ya gangara zuwa Yaffa, inda ya sami jirgin ruwa mai shirin tashi daga tashar. Bayan ya biya kuɗin tafiya, sai ya shiga jirgi ya kama hanya zuwa Tarshish don yă tsere wa Ubangiji.
4 Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.
-
1 Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah. 2 An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa,
“Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka,
wanda zai shirya hanyarka,”
3 “muryar mai kira a hamada tana cewa,
‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,
ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”
4 Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5 Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun. 6 Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji. 7 Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba. 8 Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
-
35 Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ 38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
-
16 Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!
-
14 Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. 15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
-
11 Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. 12 Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.
13 Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta. 14 Na ci gaba a cikin Yahudanci fiye da yawancin Yahudawan da suke tsarana, na kuma yi ƙwazo ƙwarai ga bin al’adun kakannina. 15 Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi 16 yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba. 17 Ban kuma tafi Urushalima domin in ga waɗanda suka riga ni zaman manzanni ba, sai dai na hanzarta na tafi ƙasar Arabiya, daga baya sai na koma Damaskus.
18 Bayan shekara uku, sai na haura zuwa Urushalima domin in sadu da Bitrus, na kuwa zauna tare da shi kwana goma sha biyar. 19 Ban ga wani a ciki sauran manzanni ba, sai dai Yaƙub ɗan’uwan Ubangiji. 20 Ina tabbatar muku a gaban Allah cewa abin da nake rubuta muku ba ƙarya ba ne.
21 Daga baya sai na tafi Suriya da Silisiya. 22 Ikkilisiyoyin da suke cikin Kiristi da suke a Yahudiya ba su san ni ba tukuna. 23 Sun dai sami labari ne kawai cewa, “Mutumin da dā yake tsananta mana yanzu yana wa’azin bangaskiyar da dā ya yi ƙoƙari yă hallaka.” 24 Sai suka yabi Allah saboda ni.
-
9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. 10 Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.
-
1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. 5 Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6 wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
-
11 Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12 Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.
-
17 Sama’ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra’ila ba? Ubangiji ya shafe ka ka zama sarkin Isra’ila. 18 Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’ 19 Me ya sa ba ka bi umarnin Ubangiji ba? Me ya sa ka sa hannu a ganima, ka kuma yi mugun abu a gaban Ubangiji?”
20 Shawulu ya ce, “Amma na bi umarnin Ubangiji. Na bi saƙon da Ubangiji ya ba ni. Na hallaka Amalekawa, na kuma kamo Agag sarkinsu. 21 Sojoji suka kawo tumaki da shanu mafi kyau daga cikin ganimar domin a miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”
22 Amma Sama’ila ya ce,
“Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya
fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?
Yin biyayya ta fi hadaya
a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.
23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba,
girman kai kuma yana kama da bautar gumaka.
Saboda ka ƙi maganar Ubangiji,
shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
-
38 Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” 39 Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.
-
26 “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.
-
18 Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
19 Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 20 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
21 Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”
22 Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”
23 Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24 Yesu ya kalle shi ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25 Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”
26 Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?”
27 Yesu ya amsa ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”
28 Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!”
29 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30 da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”
-
26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28 Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29 domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”
-
16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
14 Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
-
27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
-
18 “Ni kuwa, saboda ayyukansu da kuma tunaninsu, ina dab da zuwa in tattara dukan al’ummai da harsuna, za su kuma zo su ga ɗaukakata.
19 “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.
-
18 “Ruhun Ubangiji yana kaina,
domin ya shafe ni,
in yi wa matalauta wa’azin bishara.
Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,
in kuma buɗe idanun makafi,
in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.
19 In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”
-
18 Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”
-
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
-
10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.
-
1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,
domin Ubangiji ya shafe ni
domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.
Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,
don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru
in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu
2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji
da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,
don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,
3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,
in maido musu rawani mai kyau
a maimako na toka,
man murna
a maimako na makoki,
da kuma rigar yabo
a maimako na ruhun fid da zuciya.
Za a ce da su itatuwan oak na adalci,
shukin Ubangiji
don bayyana darajarsa.
4 Za su sāke gina kufai na dā
su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa;
za su sabunta biranen da aka rurrushe
da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.
-
5 Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa, “Kada ku je cikin Al’ummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa. 6 A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Isra’ila. 7 Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’ 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
-
16 “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi. 17 Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu. 18 Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai. 19 Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa, 20 gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.
21 “Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 22 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto. 23 Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.
24 “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa. 25 Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?
-
42 Da gari yana wayewa, sai Yesu ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa, da suka zo inda yake, sai suka yi ƙoƙari su hana shi barinsu. 43 Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”
-
30 Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace. 31 Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila. 32 Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”
-
30 Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana 31 ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta. 32 Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’ 33 Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”
34 Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai 35 amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai. 36 Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa. 37 Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi, 38 yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
39 “Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace, 40 amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. 41 Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. 42 Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. 43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
44 Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon. 45 Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai. 46 Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah.
Sai Bitrus ya ce, 47 “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.” 48 Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki.
-
21 Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, 22 suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.” 23 Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
-
10 To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”
-
7 Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. 8 Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji.
9 Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka.
-
12 Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa. 13 Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.
-
3 Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau. 4 Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’
-
3 Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, 4 “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”
5 Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. 6 Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 7 Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. 8 Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.
9 “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10 Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11 Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12 “Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13 Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
-
27 Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.
-
10 A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!”
Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.”
11 Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a. 12 Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.”
13 Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. 14 Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.”
15 Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila. 16 Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.”
17 Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” 18 Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma,
-
19 Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 20 Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. 21 Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. 22 Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
Shows Read in context, Share and Copy.