77 Bible Verses About Singing
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
-
16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. 17 Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
-
1 Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2 Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.
-
24 Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
25 Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. 26 Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
-
8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,
“Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin
ka kuma buɗe hatimansa,
domin an kashe ka,
da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,
daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,
kuma za su yi mulki a duniya.”
11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,
“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,
don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi
da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,
“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon
yabo da girma da ɗaukaka da iko,
sun tabbata har abada abadin!”
14 Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
-
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai;
daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya;
ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa;
ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
-
13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.
-
1 Yabi Ubangiji.
Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
yabonsa a cikin taron tsarkaka.
2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;
bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.
3 Bari su yabi sunansa tare da rawa
suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.
-
1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;
ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.
2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
-
2 Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su 3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,
“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
4 Wane ne ba zai ji tsoronka,
yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?
Gama kai kaɗai ne mai tsarki.
Dukan al’ummai za su zo
su yi sujada a gabanka,
gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
-
17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”
-
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
-
5 Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;
zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.
6 Zan rera ga Ubangiji
gama ya yi mini alheri.
-
Zabura ce.
1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
gama ya yi abubuwa masu banmamaki;
hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki
sun yi masa aikin ceto.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu,
abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
-
16 Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.
-
33 Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
34 Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.
-
26 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
-
11 Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito. 12 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. 13 Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera,
“Yana da kyau;
ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”
Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije, 14 Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.
-
25 Sarki Hezekiya ya ajiye Lawiyawa a cikin haikalin Ubangiji tare da ganguna, garayu da molaye, yadda Dawuda da Gad mai duba na sarki da kuma annabi Natan suka tsara. Ubangiji ne ya umarta wannan ta wurin annabawansa. 26 Saboda haka Lawiyawa suka tsaya a shirye tare da kayan kiɗin Dawuda, firistoci kuma tare da ƙahoninsu.
27 Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila. 28 Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.
29 Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada. 30 Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.
-
6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai;
ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya;
ku rera zabura ta yabo gare shi.
-
22 Zan yabe ka da garaya
saboda amincinka, ya Allah;
zan rera yabo gare ka da molo,
Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki
sa’ad da na rera yabo gare ka,
ni, wanda ka fansa.
24 Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci
dukan yini,
gama waɗanda suka so su cutar da ni
sun sha kunya suka kuma rikice.
-
27 A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo. 28 Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa, 29 daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.
-
16 Amma zan rera game da ƙarfinka,
da safe zan rera game da ƙaunarka;
gama kai ne mafakata,
kagarata a lokacin wahala.
17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;
kai, ya Allah, kai ne kagarata,
Allah mai ƙaunata.
-
4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
-
Zabura ce. Don yin godiya.
1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.
2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;
ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
-
14 Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba. 15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
-
6 Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah.
Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki. 7 Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji. 8 Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.
-
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna;
bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki.
Ka buɗe kāriyarka a bisansu,
domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf.
1 Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu;
ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!
2 Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga,
ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,
daga laka da taɓo;
ya sa ƙafafuna a kan dutse
ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,
waƙar yabo ga Allahna.
Da yawa za su gani su tsorata
su kuma dogara ga Ubangiji.
-
1 Yabi Ubangiji.
Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki;
yabe shi a cikin sammai na ikonsa.
2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko;
yabe shi saboda mafificin girmansa.
3 Yabe shi da ƙarar kakaki,
yabe shi da garaya da molo,
4 yabe shi da ganga kuna taka rawa,
yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,
5 yabe shi da kuge mai ƙara,
yabe shi da kuge masu ƙara sosai.
-
1 Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. 2 Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. 3 Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. 4 Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon.
-
31 Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can. 32 Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
-
27 To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. 28 Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
-
2 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
-
23 Ku rera don farin ciki, ya sammai, gama Ubangiji ya aikata wannan;
ku yi sowa, ya duniya a ƙarƙashi.
Ku ɓarke da waƙoƙi, ku duwatsu,
ku jeji da dukan itatuwanku,
gama Ubangiji ya kuɓutar da Yaƙub,
ya nuna ɗaukakarsa a cikin Isra’ila.
-
13 Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai;
ki yi farin ciki, ya ke duniya;
ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu!
Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa
zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
-
12 Za ku fita da farin ciki
a kuma bi da ku da salama;
duwatsu da tuddai
za su ɓarke da waƙa a gabanku,
dukan itatuwan jeji kuma
za su tafa hannuwansu.
-
1 A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.
2 “Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora,
sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu,
suna yabon Ubangiji!
3 “Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki!
Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa;
zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
-
33 Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
-
6 Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.
7 Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi. 8 Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.
-
19 Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla. 20 Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot. 21 Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit. 22 Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
-
4 Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa,
ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai;
sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
-
9 Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,
kangonki na Urushalima,
gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,
ya fanshi Urushalima.
-
4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa
kuna mimmiƙe a kan kujerunku.
Kuna cin naman ƙibabbun raguna
da na ƙosassun ’yan maruƙa.
5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi
kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.
6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi
kuna kuma shafa mai mafi kyau,
amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.
7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;
bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.
8 Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,
“Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,
ba na kuma son kagarunsa;
zan ba da birnin
da duk abin da yake cikinta.”
-
6 Yayinda mutane suke dawowa gida bayan da Dawuda ya kashe Bafilistin, mata suka fito daga dukan biranen Isra’ila don su sadu da Sarki Shawulu, suna waƙoƙi da raye-raye masu farin ciki, da ganguna da sarewa. 7 Suna rawa suna cewa,
“Shawulu ya kashe dubbansa,
Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai.”
-
65 ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.
-
Maskil na Etan dangin Ezra.
1 Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada;
da bakina zan sanar da amincinka
a dukan zamanai.
-
Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Zan rera wa ƙauna da adalcinka;
gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.
-
1 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
2 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
-
9 Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah;
a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,
-
17 Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa
zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.
-
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;
ku yabi sunansa mai tsarki.
-
2 Bakunanmu sun cika da dariya,
harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.
Sai ana faɗi a cikin al’ummai,
“Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”
-
5 Gara ka saurari tsawatawar mai hikima
da ka saurari waƙar wawaye.
-
10 kuma fansassu na Ubangiji za su komo.
Za su shiga Sihiyona da rerawa;
matuƙar farin ciki zai mamaye su.
Murna da farin ciki za su sha kansu,
baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
-
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
-
1 “Ki rera, ya ke bakararriya,
ke da ba ki taɓa haihuwa ba;
ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki,
ke da ba ki taɓa naƙuda ba;
domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,”
in ji Ubangiji.
-
2 “Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
ya zama cetona.
Shi Allahna ne, zan yabe shi.
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
-
4 da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab. 5 Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.
-
12 Sarki ya yi amfani da almug don yă yi kayan ado wa haikalin Ubangiji da kuma don fadan sarki, don kuma yă yi molaye, da garayu saboda mawaƙa. Ba a taɓa yin jigilar katakon almug ko a gani irin yawan katakai haka ba har wa yau.)
-
11 Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.)
-
21 Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.
-
11 Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona;
yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
-
7 Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
-
20 Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi,
ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa,
haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki.
-
23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!
Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.
-
19 “To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu.
-
23 Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana.
-
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya ji kukata na neman jinƙai.
7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;
zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.
Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki
zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
-
8 Ka farka, raina!
Ku farka, garaya da molo!
Zan sa safe yă farka.
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;
zan rera game da kai a cikin mutane.
-
32 Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya,
ku rera yabo ga Ubangiji, Sela
-
30 Zan yabe sunan Allah cikin waƙa
in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
-
13 Zan kawo ƙarshen waƙoƙinki masu surutu, ba kuwa za a ƙara jin kaɗe-kaɗen garayunki ba.
-
32 Tabbatacce, gare su ba ka fi mai waƙar ƙauna da murya mai daɗi kana kuma yin kiɗa sosai ba, gama sukan ji maganarka amma ba sa amfani da ita.
Shows Read in context, Share and Copy.