84 Bible Verses About Morning

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Morning
  1. 2 Ka saurare kukata na neman taimako,

    Sarkina da Allahna,

    gama gare ka nake addu’a.

    3 Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

    da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

    in kuma jira da sa zuciya.

    4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;

    gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

    5 Masu fariya ba za su iya tsaya

    a gabanka ba.

    Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

    6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.

    Masu kisankai da mutane masu ruɗu

    Ubangiji yana ƙyama.

    7 Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma,

    zan shiga gidanka;

    da bangirma zan durƙusa

    ga haikalinka.

    8 Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka

    saboda abokan gābana,

    ka fayyace hanyarka a gabana.

  2. 21 Duk da haka na tuna da wannan

    na kuma sa bege ga nan gaba.

    22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

  3. Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda.

    1 Zan girmama ka Ya Ubangiji,

    gama ka tsamo ni daga zurfafa

    ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

    2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako

    ka kuwa warkar da ni.

    3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari;

    ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

    4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa;

    ku yabi sunansa mai tsarki.

    5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  4. 8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

    gama na sa zuciyata a gare ka.

    Ka nuna mini hanyar da zan bi,

    gama a gare ka na miƙa raina.

    9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,

    gama na ɓoye kaina a gare ka.

    10 Ka koya mini in yi nufinka,

    gama kai ne Allahna;

    bari nagarin Ruhunka

    yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

  5. 16 “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”

  6. 35 Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a. 36 Siman da abokansa suka fita nemansa. 37 Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!”

    38 Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” 39 Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.

  7. 16 Amma zan rera game da ƙarfinka,

    da safe zan rera game da ƙaunarka;

    gama kai ne mafakata,

    kagarata a lokacin wahala.

    17 Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka;

    kai, ya Allah, kai ne kagarata,

    Allah mai ƙaunata.

  8. 12 Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,

    don mu sami zuciyar hikima.

    13 Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba?

    Ka ji tausayin bayinka.

    14 Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa,

    don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.

    15 Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba,

    kamar yawan shekarun da muka ga wahala.

    16 Bari a nuna ayyukanka ga bayinka,

    darajarka ga ’ya’yansu.

    17 Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;

    ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,

    I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

  9. 76 “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;

    gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

    77 don ka sanar da mutanensa ceto,

    ta wurin gafarar zunubansu,

    78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,

    hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,

    79 don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,

    da kuma cikin inuwar mutuwa,

    don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

    80 Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.

  10. 12 “Ko ka taɓa ba safiya umarni

    ko kuma ka sa asuba ta fito,

    13 don ta kama gefen duniya

    ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?

  11. 26 Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. 27 ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’ kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. 28 Zan kuma ba shi tauraron asubahi.

  12. 1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

    3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.

  13. 19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa.

  14. 13 Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji;

    da safe addu’ata kan zo gabanka.

  15. 4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?

    Gaya mini, in ka sani.

    5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!

    Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?

    6 A kan me aka kafa tushenta,

    ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,

    7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare

    dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

  16. 24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;

    bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.

  17. 4 Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,

    don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye.

    Ya farkar da ni da safe,

    ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.

    5 Ubangiji Mai Iko Duka ya buɗe kunnuwana,

    kuma ban yi tayarwa ba;

    ban ja da baya ba.

  18. 3 Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.

  19. 16 Sa’ad da Yaƙub ya farka daga barci, sai ya yi tunani ya ce, “Tabbatacce Ubangiji yana a wannan wuri, ban kuwa sani ba.” 17 Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”

    18 Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa. 19 Ya kira wannan wuri Betel ko da yake dā ana kiran birnin Luz ne.

  20. 8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka;

    inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe

    kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.

  21. 147 Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako;

    na sa zuciyata a maganarka.

  22. 5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,

    kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

    6 Raina na jiran Ubangiji

    fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,

    fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

    7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,

    gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa

    kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

    8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila

    daga dukan zunubansu.

  23. 38 “Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana. ’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. 39 Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma. 40 Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.

  24. 6 Ka shuka irinka da safe,

    da yamma kuma kada ka janye hannunka,

    gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,

    ko wannan ko wancan,

    ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

  25. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

    31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?

  26. 8 Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.

  27. 27 Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji. 28 Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.

  28. 13 Kashegari, Musa ya zauna domin yă yi wa mutane shari’a, sai suka tsaya kewaye da shi daga safe har yamma. 14 Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”

  29. 4 “Me zan yi da kai Efraim?

    Me zan yi da kai Yahuda?

    Ƙaunarku tana kamar hazon safiya,

    kamar raɓar safiya da takan ɓace.

  30. 1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

    2 Ya amsa ya ce, “Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’ 3 da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta. 4 Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.

  31. 2 Ka shirya da safe, ka hauro kan Dutsen Sinai. Ka gabatar da kanka a gare ni a can kan dutse. 3 Ba wani da zai zo tare da kai, ko a gan shi ko’ina a kan dutsen, kada garkunan tumaki ko na shanu su yi kiwo kusa da dutsen.”

    4 Saboda haka Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na fari, sai ya hau Dutsen Sinai da sassafe, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, yana kuma ɗauke da alluna biyu na dutse a hannuwansa.

  32. 1 Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe.

    “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai,

    abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama.

    Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki,

    wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.

    2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina;

    maganarsa tana a harshena.

    3 Allah na Isra’ila ya yi magana,

    Dutsen Isra’ila ya ce mini,

    ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci,

    sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,

    4 yana kama da hasken safiya

    a safiya marar girgije,

    kamar haske bayan ruwan sama

    da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’

    5 “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba?

    Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni

    shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba?

    Ba zai kawo ga cikar cetona

    yă kuma biya duk bukatuna ba?

    6 Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan

    da ba a tattara da hannu.

    7 Duk wanda ya taɓa ƙaya

    yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi;

    akan ƙone su inda suke a zube.”

  33. 12 Yaya aka yi ka fāɗo daga sama

    Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba!

    An fyaɗa ka da ƙasa,

    kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!

  34. 12 Ya gidan Dawuda ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “ ‘Ku yi gaskiya kowace safiya;

    ku kuɓuta daga hannun mai danniya

    wannan da aka yi wa fashi

    in ba haka ba hasalata za tă sauka ta kuma ci kamar wuta

    saboda muguntar da kuka aikata

    za tă ci babu wanda zai kashe ta.

  35. 1 “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.

  36. 1 Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu. 2 A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3 sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”

    4 Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne. 5 Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.

    6 Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. 7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ”

    8 Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.

  37. 26 Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi.

    Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi.

  38. Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.

    1 Yana da kyau a yabi Ubangiji

    a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

    2 don a yi shelar ƙaunarka da safe

    amincinka kuma da dare,

    3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma

    da kuma ƙarar garaya.

  39. 2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;

    muna marmarinka.

    Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,

    cetonmu a lokacin damuwa.

  40. 1 Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.

  41. 4 Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.

  42. 4 Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,

    ka koya mini hanyoyinka;

    5 ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

    gama kai ne Allah Mai cetona,

    kuma begena yana a kanka dukan yini.

  43. 7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,

    zuciyata tana nan daram;

    zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.

    8 Ka farka, raina!

    Ku farka, garaya da molo!

    Zan sa safe yă farka.

    9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

    zan rera game da kai a cikin mutane.

    10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;

    amincinka na kaiwa sarari.

  44. 2 Da sassafe ya sāke bayyana a filin haikali, inda dukan mutane suka taru kewaye da shi, sai ya zauna don yă koya musu.

  45. 8 Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske.

  46. 25 Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”

  47. 55 Da sassafe kashegari sai Laban ya sumbaci jikokinsa da ’ya’yansa mata, ya sa musu albarka. Sa’an nan ya yi bankwana da su, ya koma gida.

  48. 20 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tashi da sassafe ka sadu da Fir’auna a lokacin da za shi kogi, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, bari mutanena su tafi, don su yi mini sujada.

  49. 13 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada,

  50. 13 “ ‘Kullum za ku tanada ɗan rago bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji; kowace safiya za ku tanada shi. 14 Tare da shi za ku tanada hadaya ta gari kowace safiya, da ya haɗa da kashi ɗaya bisa shida na efa tare da kashi ɗaya bisa uku na mai ga garin da aka cuɗa. Miƙawar wannan hadaya ta gari ga Ubangiji dawwammamiyar farilla ce. 15 Saboda haka za a tanada ɗan rago da hadaya ta gari da kuma mai kowace safiya don hadaya ta ƙonawa ta kullum.

  51. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  52. 1 Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.

  53. 23 Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24 Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25 Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa,

    26 “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,

    “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;

    za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”

    27 Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;

    da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

    sun kuma rufe idanunsu.

    In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

    su ji da kunnuwansu,

    su fahimta a zukatansu,

    su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’

  54. 13 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.

  55. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

  56. 8 Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu.

  57. 15 Ka je wurin Fir’auna da safe, yayinda za shi kogi. Ka jira a bakin Nilu don ka sadu da shi, ka ɗauki sandan nan da ya canja zuwa maciji a hannunka.

  58. 7 Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, saboda ya ji gunaguninku a kansa. Wane mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?” 8 Musa ya kuma ce, “Za ku san cewa shi ne Ubangiji, sa’ad da ya ba ku nama ku ci da yamma, da kuma duk burodin da kuke so da safe, saboda ya ji gunagunin da kuka yi a kansa. Namu a wane? Ai, gunaguninku ba a kanmu ba, amma a kan Ubangiji ne.”

  59. 21 A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.

  60. 21 Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi.

  61. 10 Kashegari da sassafe Yoshuwa ya tattara mutanensa, sai shi da shugabannin Isra’ilawa suka sha gaba suka taka zuwa Ai. 11 Dukan sojojin da suke tare da shi suka nufi birnin, da suka kai kuwa sai suka kafa sansaninsu a arewancin Ai. Tsakaninsu da Ai akwai kwari. 12 Yoshuwa ya sa mutum dubu biyar suka yi kwanto tsakanin Betel da Ai, a yammancin birnin. 13 Mutanen suka kafa sansaninsu arewa da birnin, sansani na ’yan kwanto kuwa yana yamma da birnin, amma Yoshuwa ya kwana a kwarin.

    14 Sa’ad da sarkin Ai ya ga haka, shi da duk mutanen birnin suka hanzarta da sassafe don su gamu da Isra’ilawa, su yi yaƙi da su a wani wurin da yake fuskantar Araba. Amma bai san cewa an yi masa kwanto a bayan birnin ba.

  62. 5 Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.

  63. 9 Bari taurarinta na safe su zama duhu;

    bari ranar tă yi ta jiran ganin haske

    amma kada tă gani,

  64. 17 Safe, rana da yamma

    ina kuka da nishi,

    yakan kuwa ji muryata.

    18 Yakan fisshe ni lafiya

    daga yaƙin da ake yi da ni,

    ko da yake da yawa suna gāba da ni.

  65. 8 Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir,

    warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan;

    sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku,

    ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya.

  66. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  67. 15 Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”

  68. 31 Kashegari da sassafe sai mutanen suka yi wa juna rantsuwa. Sa’an nan Ishaku ya sallame su, suka kuwa tafi cikin salama.

  69. 21 Kowace safiya, kowanne mutum yakan tattara daidai bukatarsa, lokacin da rana ta yi zafi, sai ta narke.

  70. 3 Suka karɓa daga wurin Musa dukan kyautai da Isra’ilawa suka kawo don su yi aikin shirya wuri mai tsarki. Mutane suka ci gaba da kawo kyautai yardar rai kowace safiya.

  71. 12 Dole a bar wutar da take bisa bagaden tă yi ta ci; kada tă mutu. Kowace safiya firist zai ƙara itacen wuta, yă shirya hadaya ta ƙonawa a bisa wutar yă kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a kansa.

  72. 5 Sai ya ce wa Kora da dukan waɗannan da suke tare shi, “Da safe, Ubangiji zai nuna wane ne yake nasa, da kuma wane ne yake da tsarki. Zai kuma sa mutumin yă zo kusa da shi. Mutumin da ya zaɓa kuwa zai sa yă zo kusa da shi.

  73. 21 Bala’am ya tashi da safe, ya ɗaura wa jakarsa sirdi, ya tafi tare da dattawan Mowab.

  74. 15 A rana ta bakwai, suka tashi da sassafe suka zaga birnin sau bakwai yadda suka saba. A wannan rana kaɗai ne suka zaga birnin sau bakwai.

  75. 14 “ ‘Da safe ku zo kabila-kabila. Kabilar da Ubangiji ya ware, za tă zo gaba gida-gida; gidan da Ubangiji ya ware, za su zo gaba iyali-iyali. Iyalin kuma da Ubangiji ya ware, za su zo gaba mutum bayan mutum.

  76. 28 Da safe sa’ad da mutanen garin suka tashi, sai suka tarar an rushe bagaden Ba’al, tare da ginshiƙin Ashera da yake kusa da shi, duk an sare, bijimi na biyu kuma aka miƙa hadaya a kan sabon bagaden!

  77. 20 Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.

  78. 18 Numfashinta yana fitar da wuta;

    idanunta kamar hasken zuwan safe.

  79. 10 Rana guda a filayen gidan sun fi

    dubu a wani wuri dabam;

    zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna

    da in zauna a tentunan mugaye.

    11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

    Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

    ba ya hana kowane abu mai kyau

    wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

  80. 11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,

    zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;

    ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,

    don in ji tsoron sunanka.

    12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;

    zan ɗaukaka sunanka har abada.

    13 Gama ƙaunarka da girma take gare ni;

    kai ka cece ni daga zurfafa,

    daga mazaunin matattu.

  81. 5 Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne;

    ba ya yin abin da ba daidai ba.

    Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili,

    kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa,

    duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.

  82. 18 Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.

  83. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.

  84. 13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.