104 Bible Verses About Fear of the Lord
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;
fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;
ya cece shi daga dukan wahalarsa.
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,
ya kuwa cece su.
8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;
mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa,
gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
10 Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
11 Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
zan koya muku tsoron Ubangiji.
12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa
yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta
da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
14 Juyo daga mugunta ku yi alheri;
nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
-
7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
-
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai
yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
-
26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
-
9 Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima;
ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
11 Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa,
za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
-
12 To wane ne mai tsoron Ubangiji?
Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
13 Zai ci kwanakinsa a wadace,
kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa;
yakan sa su san alkawarinsa.
15 Idanuna kullum suna a kan Ubangiji,
gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
-
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.
-
12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali;
ina da sani da iya rarrabewa.
13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta;
ina ƙin girman kai da fariya,
halin mugunta da kuma muguwar magana.
14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne;
ina da fahimi da kuma iko.
15 Ta wurina sarakuna suke mulki
masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
16 ta wurina sarakuna suke mulki,
da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata,
kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa,
dukiya da wadata masu dawwama.
-
16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.
Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.
19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.
-
7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
takan wartsakar da rai.
Farillan Ubangiji abin dogara ne,
suna mai da hikima da sauƙi.
8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne,
suna ba da farin ciki ga zuciya.
Umarnan Ubangiji haske ne
suna ba da haske ga idanu.
9 Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya,
zai kasance har abada.
Farillan Ubangiji tabbatattu ne,
kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
10 Sun fi zinariya daraja,
fiye da zalla zinariya nesa;
sun fi zuma zaƙi
fiye da zuma daga kaki.
11 Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka;
a kiyaye su akwai lada mai girma.
-
13 Yanzu an ji kome;
ga ƙarshen magana.
Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,
gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,
har da waɗanda aka yi a ɓoye,
ko nagari ne, ko mugu.
-
23 Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai.
Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
-
28 Ya kuma ce wa mutum,
‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,
kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”
-
11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro
ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
-
31 Sa’an nan ikkilisiya ko’ina a Yahudiya, Galili da kuma Samariya ta sami salama. Ta yi ƙarfi; ta kuma ƙarfafa ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ta ƙaru sosai tana rayuwa cikin tsoron Ubangiji.
-
18 Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa 19 suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”
20 Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
21 Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake.
-
8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,
mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
9 Ba zai yi ta zargi ba
ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu
ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,
haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
12 kamar yadda gabas yake daga yamma,
haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,
haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
-
16 Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji
da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
-
6 Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi;
ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
-
28 Saboda haka, da yake muna karɓar mulkin da ba ya jijjiguwa, sai mu yi godiya, ta haka kuwa mu yi wa Allah sujada yadda ya kamata, tare da bangirma da kuma tsoro, 29 gama “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.”
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
-
27 Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai,
amma akan gajartar da shekarun mugaye.
28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki,
amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
29 Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai
amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
-
13 Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14 ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15 Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16 Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17 Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.
-
12 Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, 13 ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?
14 Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.
-
1 Yabi Ubangiji.
Mai albarka ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,
wanda yakan sami farin ciki mai girma a umarnansa.
2 ’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.
3 Wadata da arziki suna a cikin gidansa,
adalcinsa zai dawwama har abada.
-
11 Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji,
shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
12 Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu.
Zai albarkace gidan Isra’ila,
zai albarkace gidan Haruna,
13 zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji,
manya da ƙanana duka.
14 Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru,
da ku da ’ya’yanku.
15 Bari Ubangiji yă albarkace ku,
shi Mahalicci sama da ƙasa.
-
1 Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
-
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
-
Waƙar haurawa.
1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
2 Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
4 Ta haka mai albarka yake
wanda yake tsoron Ubangiji.
-
4 “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.
-
5 Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar. 6 Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a. 7 Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
-
11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji,
zan kuwa yi tafiya cikin gaskiyarka;
ka ba ni zuciya wadda ba tă rabu ba,
don in ji tsoron sunanka.
12 Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata;
zan ɗaukaka sunanka har abada.
-
12 “Kada ka kira wani abu makirci
game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci;
kada ji tsoron abin da suke tsoro,
kada kuma ka firgita game da shi.
13 Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki,
shi ne wanda za ka ji tsoro,
shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
14 zai kuwa kasance a wuri mai tsarki;
amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama
dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe
dutse kuma da zai sa su fāɗi.
Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama
tarko da raga.
-
14 “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki? 15 A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”
16 Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
17 “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. 18 Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
-
26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. 28 Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29 Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30 Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” 31 Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
-
6 Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. 7 Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
-
17 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi,
amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
18 Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
-
3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,
Ya Ubangiji, wa zai tsaya?
4 Amma tare da kai akwai gafartawa,
saboda haka ake tsoronka.
-
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
-
18 Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
19 Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
-
38 Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. 39 Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu. 40 Zan yi madawwamin alkawari da su. Ba zan taɓa barin aikata musu alheri ba, zan kuma iza su su ji tsorona, don kada su ƙara juya daga gare ni.
-
9 Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan. 10 Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
11 To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku. 12 Ba ƙoƙari muke mu yabe kanmu a gare ku ba ne, sai dai muna ba ku damar yin taƙama da mu ne, don ku sami amsar da za ku ba wa waɗanda suke taƙama da abin da ake gani ne, a maimakon abin da yake cikin zuciya. 13 In hankalinmu a taɓe yake, ai, saboda Allah ne, in kuwa cikin hankalinmu muke, ai, saboda ku ne. 14 Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. 15 Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
-
10 Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki,
balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;
11 Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa,
waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
-
20 Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,
tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku
wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 Da a ce kun saurari tsawatata,
da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata
in kuma sanar da ku tunanina.
24 Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira
ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,
25 da yake kun ƙi dukan shawarata
ba ku kuma yarda da tsawatata ba,
26 Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku,
zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,
27 sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri,
sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa,
sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.
28 “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;
za su neme ni amma ba za su same ni ba.
29 Da yake sun ƙi sani
ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,
30 da yake ba su karɓi shawarata ba
suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,
31 za su sami sakayyar abubuwan da suka yi
su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.
-
50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,
daga zamani zuwa zamani.
-
9 To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. 10 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;
11 babu wani mai fahimta,
babu wani mai neman Allah.
12 Duk sun kauce gaba ɗaya,
sun zama marasa amfani;
babu wani mai aikata nagarta,
babu ko ɗaya.”
13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,
harsunansu suna yin ƙarya.”
“Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”
14 “Bakunansu sun cike da la’ana da ɗacin rai.”
15 “Ƙafafunsu suna saurin kai su zuwa ga zub da jini;
16 hallaka da baƙin ciki suna ko’ina a hanyoyinsu,
17 ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
-
23 Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa. 24 Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
-
33 Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima,
kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
-
4 Sauƙinkai da tsoron Ubangiji
sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
-
5 Ubangiji da girma yake, gama yana zaune a bisa;
zai cika Sihiyona cikin gaskiya da adalci.
6 Zai zama tabbataccen harsashi na koyaushe,
ma’ajin ceto da hikima da sani a yalwace;
tsoron Ubangiji shi ne mabuɗin wannan dukiya.
-
6 Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. 7 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?”
Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.”
8 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.”
9 Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? 10 Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina.
-
23 Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi!
Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi!
Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
-
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19 don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
-
10 Sa’an nan kuma, na ga an binne masu mugunta, waɗanda suke shiga da fita daga tsattsarkan wuri suke kuma samun yabo a birnin da suka yi wannan. Wannan ma ba shi da amfani.
11 In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba. 12 Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah. 13 Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.
-
1 Toho zai fito daga kututturen Yesse;
daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.
2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,
Ruhun hikima da na fahimta,
Ruhun shawara da na iko,
Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
3 zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
4 amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,
da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.
Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;
da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
5 Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
-
7 Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana. 8 Saboda haka suka tambaye shi suka ce, “Yanzu, gaya mana, dalilin da ya sa wannan masifa ta zo mana? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Ina ne ƙasarka? Daga wacce kabila ce ka fito?”
9 Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”
10 Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” (Sun gane cewa yana gudu ne daga wurin Ubangiji, domin ya riga ya faɗa musu.)
11 Sai tekun ya daɗa rikicewa. Sai suka tambaye shi, “Me za mu yi da kai domin tekun yă daina hauka?”
12 Ya amsa musu ya ce, “Ku ɗauke ni ku jefa a cikin teku, tekun zai kwanta. Na san cewa laifina ne ya jawo wannan babban hadirin da ya auka muku.”
13 Maimakon mutanen su yi haka, sai suka yi ƙoƙari su tura jirgin ruwan zuwa bakin teku. Amma ba su iya ba, saboda iskar ta sa tekun ya yi ta ƙara hauka. 14 Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.” 15 Sa’an nan suka ɗauki Yunana suka jefar da shi daga jirgin, sai tekun ya kwanta. 16 Ganin haka sai mutanen suka cika da tsoron Ubangiji, suka kuma miƙa wa Ubangiji hadaya, suka yi wa’adi da shi.
-
13 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa shi kaɗai, ku kuma yi alkawaranku da sunansa. 14 Kada ku bi waɗansu alloli, allolin mutanen da suke kewaye da ku; 15 gama Ubangiji Allahnku, wanda yake cikinku, Allah ne mai kishi, fushinsa kuma zai yi ƙuna gāba da ku, zai kuma hallaka ku daga fuskar ƙasar.
-
24 Amma ku amince za ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da aniya da dukan zuciyarku, kuna da manyan abubuwan da ya yi muku. 25 Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku.
-
3 Allah na Isra’ila ya yi magana,
Dutsen Isra’ila ya ce mini,
‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci,
sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,
4 yana kama da hasken safiya
a safiya marar girgije,
kamar haske bayan ruwan sama
da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’
-
14 Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah,
amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.
-
14 Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah. 15 Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.”
-
6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
-
8 Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. 9 Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10 Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11 Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12 Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13 Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
-
9 Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. 10 Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. 11 Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!”
Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
12 Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”
13 Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa. 14 Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
-
17 Amma daga madawwami zuwa madawwami
ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,
adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
18 tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa
suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
-
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
-
7 Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
-
3 suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa,
“Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki,
ya Ubangiji Maɗaukaki.
Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya,
ya Sarkin zamanai.
4 Wane ne ba zai ji tsoronka,
yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji?
Gama kai kaɗai ne mai tsarki.
Dukan al’ummai za su zo
su yi sujada a gabanka,
gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
-
21 Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.
-
5 Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji,
amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
6 Gama wane ne a sarari za a iya kwatanta da Ubangiji?
Wane ne yake kamar Ubangiji a cikin talikan samaniya?
7 Cikin taron tsarkaka Allah ne aka fi tsoro;
shi ne mafi bantsoro fiye da dukan waɗanda suka kewaye shi.
8 Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka?
Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.
-
1 A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya. 2 Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa. 3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”
4 Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?”
Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah. 5 Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus. 6 Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”
7 Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima. 8 Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa.
-
34 Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai 35 amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai.
-
5 Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,
“Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,
kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,
6 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”
7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9 Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10 Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
-
17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
-
1 Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka, 2 saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.
-
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
2 Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,
ta haka suka kasance?”
In ji Ubangiji.
“Wannan mutum ne nake jin daɗi,
shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,
yana kuma rawar jiki ga maganata.
-
18 A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah.
-
4 Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.
-
1 A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.
-
19 Alherinka da girma yake,
wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,
wanda ka mayar a gaban mutane
a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su
daga makircin mutane;
a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya
daga harsuna masu zagi.
-
25 Jin tsoron mutum tarko ne,
amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
-
19 Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma ramummuka a ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
20 A wannan rana mutane za su zubar wa
jaba da jamage
gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya
da suka yi don su bauta musu.
21 Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma zuwa tsagaggun duwatsu
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
-
17 In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18 kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. 19 To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” 20 Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. 21 Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.
22 Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. 23 In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. 24 Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?
-
22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji.
-
19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
-
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
-
14 “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
-
29 Kash, da a ce zukatansu za su zama masu tsorona, su kuma kiyaye dukan dokokina kullum mana, saboda kome yă zama da lafiya gare su, da kuma ’ya’yansu har abada!
-
20 Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa. 21 Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji.
1 Akwai magana a cikin zuciyata
game da zunubin mugu.
Babu tsoron Allah
a idanunsa.
2 Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne
wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
3 Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu;
ya daina zama mai hikima da yin alheri.
4 Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta;
yakan sa kansa ga aikata zunubi
kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.
-
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
-
14 Na san cewa duk abin da Allah ya yi zai dawwama har abada; ba abin da za a ƙara ko a rage. Allah ya yi haka domin mutane su girmama shi.
-
10 Ku tafi cikin duwatsu,
ku ɓuya cikin ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa!
-
1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;
duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.
5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
-
40 Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?
-
5 Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa,
“Ku yabi Allahnmu,
dukanku da kuke bayinsa,
ku da kuke tsoronsa,
babba da yaro!”
6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,
“Halleluya!
Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna
mu kuma ɗaukaka shi!
Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,
amaryarsa kuwa ta shirya kanta.
8 Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta
ta sanya.”
(Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)
9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”
-
17 Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu.
-
18 Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa. 19 Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali 20 don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.
-
14 “Yanzu, sai ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa da dukan aminci. Ku zubar da allolin da kakanninku suka yi musu sujada a hayin Kogin Yuferites da kuma a Masar, ku bauta wa Ubangiji. 15 Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”
-
14 In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya. 15 Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.
-
9 Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa,
don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
-
19 Muguntarka za tă hukunta ka;
jan bayanka zai tsawata maka.
Sai ka lura ka kuma gane
yaya mugu da kuma ɗaci suke a gare ka
sa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnka
kuma ba ka tsorona,”
in ji Ubangiji Maɗaukaki.
-
22 Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji.
“Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba?
Na sa yashi ya zama iyakar teku,
madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba.
Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba;
za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.
23 Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne;
sun kauce suka kuma rabu da ni.
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,
wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
Shows Read in context, Share and Copy.