72 Bible Verses About God's Forgiveness

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Forgiveness
  1. 9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

    “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

    a tsarkake sunanka,

    10 mulkinka yă zo

    a aikata nufinka a duniya

    kamar yadda ake yi a sama.

    11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

    12 Ka gafarta mana laifofinmu,

    kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

    13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

    amma ka cece mu daga mugun nan. ’

    14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

  2. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

    8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  3. 5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.”

    6 To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, 7 “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

    8 Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? 9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? 10 Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, 11 “Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 12 Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”

  4. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta.

  5. 29 Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta. 30 Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa. 31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  6. 37 Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”

    38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. 39 Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”

  7. 18 Wane ne Allah kamar ka,

    wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?

    Ba ka zama mai fushi har abada

    amma kana marmari ka nuna jinƙai.

    19 Za ka sāke jin tausayinmu;

    za ka tattake zunubanmu a ƙarƙashin sawunka

    ka kuma tura dukan kurakuranmu zuwa cikin zurfafan teku.

    20 Za ka yi wa Yaƙub aminci,

    ka kuma nuna jinƙai ga Ibrahim,

    kamar yadda ka yi alkawari da rantsuwa ga kakanninmu

    tun a kwanankin dā.

  8. 15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. 16 Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’ 17 In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

    18 “Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.

    19 “Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku. 20 Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”

    21 Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”

    22 Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.

  9. 8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri,

    mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.

    9 Ba zai yi ta zargi ba

    ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;

    10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu

    ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.

    11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya,

    haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

    12 kamar yadda gabas yake daga yamma,

    haka ya cire laifofinmu daga gare mu.

    13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

    haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

    14 gama ya san yadda aka yi mu,

    ya tuna cewa mu ƙura ne.

  10. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

  11. 25 “Ni kaɗai ne na shafe

    laifofinku, saboda sunana,

    ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba.

    26 Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce,

    bari mu yi muhawwara wannan batu tare;

    ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.

  12. 33 Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34 Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

  13. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”

  14. Ta Dawuda. Maskil ne.

    1 Mai farin ciki ne shi

    wanda aka gafarta masa laifofinsa,

    wanda aka shafe zunubansa.

    2 Mai farin ciki ne mutumin

    da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa

    wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.

    3 Sa’ad da na yi shiru,

    ƙasusuwana sun yi ta mutuwa

    cikin nishina dukan yini.

    4 Gama dare da rana

    hannunka yana da nauyi a kaina;

    an shanye ƙarfina ƙaf

    sai ka ce a zafin bazara. Sela

    5 Sa’an nan na furta zunubina a gare ka

    ban kuwa ɓoye laifina ba.

    Na ce, “Zan furta

    laifofina ga Ubangiji.”

    Ka kuwa gafarta

    laifin zunubina. Sela

    6 Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka

    yayinda kake samuwa;

    tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,

    ba za su kai wurinsa ba.

    7 Kai ne wurin ɓuyata;

    za ka tsare ni daga wahala

    ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela

  15. 3 In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,

    Ya Ubangiji, wa zai tsaya?

    4 Amma tare da kai akwai gafartawa,

    saboda haka ake tsoronka.

  16. 35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. 36 Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.

    37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.

  17. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  18. 5 Sa’an nan Ubangiji ya sauko a cikin girgije ya tsaya can tare da shi, ya kuma yi shelar sunansa. 6 Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci, 7 nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”

  19. 16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.

    Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;

    Ku daina aikata mugunta.

    17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.

    Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.

    Ku ba wa marayu hakkinsu,

    ku taimaki gwauruwa.

    18 Ubangiji ya ce,

    “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,

    Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,

    za su zama fari kamar ƙanƙara;

    ko da sun yi ja kamar mulufi,

    za su zama kamar ulu.

    19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya,

    za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;

    20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa,

    za a kashe ku da takobi.”

    Ni Ubangiji na faɗa.

  20. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. 14 Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. 15 Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. 16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  21. 31 “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,

    “sa’ad da zan yi sabon alkawari

    da gidan Isra’ila

    da kuma gidan Yahuda.

    32 Ba zai zama kamar alkawarin

    da na yi da kakanni kakanninsu ba

    sa’ad da na kama su da hannu

    na bishe su daga Masar,

    domin sun take alkawarina,

    ko da yake na zama miji a gare su,”

    in ji Ubangiji.

    33 “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

    bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.

    “Zan sa dokata a tunaninsu

    in kuma rubuta ta a zukatansu.

    Zan zama Allahnsu,

    za su kuma zama mutanena.

    34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

    ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’

    domin duk za su san ni,

    daga ƙaraminsu har zuwa babba,”

    in ji Ubangiji.

    “Gama zan gafarta muguntarsu

    ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  22. 39 “Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace, 40 amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. 41 Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. 42 Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. 43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”

  23. 21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.

  24. 6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;

    ku yi kira gare shi tun yana kusa.

    7 Bari mugu ya bar irin halinsa

    mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

    Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

    ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

  25. 26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”

    27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

  26. 47 “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”

    48 Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”

    49 Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”

    50 Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”

  27. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

  28. 19 Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, 20 don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan. 21 Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.

  29. 17 Sai ya ƙara da cewa,

    “Zunubansu da kurakuransu

    ba zan ƙara tunawa da su ba.”

    18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.

  30. 1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

  31. 5 Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji,

    cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

  32. 38 “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. 39 Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.

  33. 8 Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce,

    “Ina gaya muku lokaci yana zuwa,

    sa’ad da zan yi sabon alkawari

    da gidan Isra’ila

    da kuma gidan Yahuda.

    9 Ba zai zama kamar irin alkawarin

    da na yi da kakanni-kakanninsu

    sa’ad da na kama hannunsu

    don in fitar da su daga Masar ba,

    domin ba su yi aminci da alkawarina ba,

    sai na juya musu baya,

    in ji Ubangiji.

    10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila,

    bayan lokacin nan,

    in ji Ubangiji.

    Zan sa dokokina a cikin zukatansu,

    in kuma rubuta su a kan zukatansu.

    Zan zama Allahnsu,

    su kuwa za su zama mutanena.

    11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,

    balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’

    domin dukansu za su san ni,

    daga ƙaraminsu zuwa babba.

    12 Gama zan gafarta muguntarsu

    ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  34. 23 “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa. 24 Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma. 25 Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.

    26 “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’ 27 Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

    28 “Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’

    29 “Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’

    30 “Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin. 31 Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.

    32 “Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni. 33 Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’ 34 Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.

    35 “Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”

  35. 9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,

    amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.

  36. 13 Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

    amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

  37. 21 Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”

  38. 14 in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

  39. 44 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”

    45 Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. 46 Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu. 47 Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48 Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

  40. 22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.

  41. 17 “Yanzu bari Ubangiji yă nuna ikonsa, kamar dai yadda ka furta. 18 ‘Ubangiji mai jinkiri fushi ne, mai yawan ƙauna, mai gafarta zunubi da tawaye. Duk da haka ba ya ƙyale mai laifi, babu horo. Yana horin ’ya’ya saboda zunubin iyayensu har tsara ta uku, da ta huɗu.’ 19 Bisa ga ƙaunarka mai girma, ka gafarta zunubin mutanen nan, kamar dai yadda ka gafarta musu daga lokacin da suka bar Masar har zuwa yanzu.”

    20 Ubangiji ya amsa ya ce, “Na gafarta musu, yadda ka roƙa. 21 Duk da haka, muddin ina raye, kuma muddin ɗaukakar Ubangiji ta cika dukan duniya, 22 ko ɗaya daga cikinsu da suka ga ɗaukakata da mu’ujizai da na yi a Masar, da kuma a cikin hamada, da suka ƙi yin mini biyayya, suka kuma gwada ni har sau goma, 23 ba ko ɗayansu da zai gan ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa zan ba wa kakanninsu. Ba ko ɗaya da ya rena ni, da zai taɓa ganinta.

  42. 20 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

    21 Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

    22 Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku? 23 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’? 24 Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” 25 Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.

  43. 13 Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu. 14 Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye. 15 Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

    16 Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci. 17 Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu.

  44. 23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

  45. 31 Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. 32 Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

  46. 31 Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.

  47. 17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!

  48. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba.

    1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

    bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

    bisa ga tausayinka mai girma

    ka shafe laifofina.

    2 Ka wanke dukan kurakuraina

    ka tsarkake ni daga zunubina.

    3 Gama ina sane da laifofina

    zunubaina kuma kullum suna a gabana.

    4 Kai kaɗai na yi wa zunubi

    na yi abin da yake mugu a idonka,

    ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

    aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

    5 Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa

    mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

  49. 2 Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

    3 Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

    4 Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ 6 Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

  50. 1 Sa’ad da dukan albarku da la’anonin nan da na sa a gabanku suka zo muku, kuka kuma sa su a zuciya, a duk inda Ubangiji Allahnku ya watsar da ku a cikin al’ummai, 2 sa’ad da kuma ku da ’ya’yanku kuka komo ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi biyayya da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, bisa ga kome da na umarce ku a yau, 3 a sa’an nan ne Ubangiji Allahnku zai yi muku jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma sāke tattara ku daga dukan al’ummai inda ya warwatsa ku. 4 Ko da ma an kore ku zuwa ƙasa mafi nisa a ƙarƙashin sammai, daga can Ubangiji Allahnku zai tattara ku, yă dawo da ku. 5 Zai dawo da ku zuwa ƙasar da take ta kakanninku, za ku kuwa mallake ta. Zai sa ku yi arziki, ku kuma yi yawa fiye da kakanninku. 6 Ubangiji Allahnku zai yi wa zukatanku kaciya da kuma zukatan zuriyarku, saboda ku ƙaunace shi da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma rayu. 7 Ubangiji Allahnku zai sa dukan waɗannan la’anoni a kan abokan gābanku waɗanda suke ƙinku, suke kuma tsananta muku. 8 Za ku sāke yi wa Ubangiji biyayya, ku kuma bi dukan umarnan da nake ba ku a yau. 9 Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai mayar da ku masu arziki ƙwarai a cikin dukan aiki hannuwanku, da kuma cikin ’ya’yanku, da ’ya’yan shanunku, da kuma hatsin gonarku. Ubangiji zai sāke jin daɗinku yă sa ku yi arziki, kamar dai yadda ya ji daɗin kakanninku. 10 In dai kuka yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma kiyaye umarnansa da ƙa’idodin da aka rubuta a wannan Littafin Doka, kuka juyo ga Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.

    11 To, abin da nake umartanku a yau, ba mai wuya ba ne gare ku, ba kuma abin da ya fi ƙarfinku ba ne. 12 Ba ya can sama, balle ku ce, “Wa zai hau sama yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?” 13 Ba kuwa yana gaba da teku ba, da za ku ce, “Wa zai haye tekun don yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?” 14 A’a, kalmar tana nan dab da ku, tana cikin bakinku da cikin zuciyarku, don ku yi biyayya.

  51. 7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,

    gama za a nuna musu jinƙai.

  52. 4 Ka gafarta mana zunubanmu,

    kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.

    Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”

  53. 23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  54. 12 Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,

    domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

  55. 16 “Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba. 17 Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba,

  56. 17 Tabbatacce wannan kuwa saboda ribata ne

    cewa in sha irin wahalan nan.

    Cikin ƙaunarka ka kiyaye ni

    daga ramin hallaka;

    ka sa dukan zunubaina

    a bayanka.

  57. 13 Ku kyakkece zuciyarku

    ba rigunanku ba.

    Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

    gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

    mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

    yakan kuma janye daga aika da bala’i.

  58. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  59. 3 Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 4 Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya.

    “Muryar mai kira a hamada,

    ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,

    ku miƙe hanyoyi dominsa.

    5 Za a cike kowane kwari,

    a farfashe kowane dutse da kowane tudu.

    Za a miƙe hanyoyin da suka karkace,

    a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.

    6 Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

  60. 22 Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.

  61. 15 “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’

    “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 16 Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka. 17 Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin 18 ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’

  62. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

    9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa!

  63. 3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu,

    ka gafarta laifofinmu.

  64. 28 Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi. 29 Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”

    30 Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

  65. 1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. 3 Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. 4 Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

  66. 32 Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta.”

  67. 9 Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,

    saboda ɗaukakar sunanka;

    ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu

    saboda sunanka.

  68. 20 Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. 21 Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

  69. 4 Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.

  70. 7 “Masu albarka ne

    waɗanda aka gafarta laifofinsu,

    waɗanda aka kuma rufe zunubansu.

  71. 4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

  72. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.