40 Bible Verses About Procrastination

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Procrastination
  1. 6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

    ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

    7 Ba shi da jagora

    ba shugaba ko mai mulki,

    8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

    ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

    9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

    Yaushe za ku farka daga barcinku?

    10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari

    rashi kuma kamar ɗan fashi.

  2. 13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,

    zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”

    14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,

    haka rago yake jujjuya a gadonsa.

    15 Rago kan sa hannunsa a kwano

    ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.

    16 Rago yana gani yana da hikima

    fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

  3. 4 Rago ba ya noma a lokacin noma;

    saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.

  4. 4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci,

    amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.

    5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,

    amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

  5. 24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki,

    amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.

  6. 4 Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome,

    amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.

  7. 59 Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.”

    Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”

    60 Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”

    61 Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”

    62 Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”

  8. 30 Na wuce cikin gonar rago,

    na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;

    31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina,

    ciyayi sun rufe ƙasar,

    katangar duwatsu duk ta rushe.

    32 Na yi tunani a zuciyata

    na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.

    33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

    ɗan naɗin hannuwa don a huta,

    34 sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi

    rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

  9. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

  10. 9 Wanda yake ragwanci a aikinsa

    ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.

  11. 13 Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!”

    Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”

  12. 19 An tare hanyar rago da ƙayayyuwa,

    amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.

  13. 13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce;

    ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.

  14. 25 Marmarin rago zai zama mutuwarsa,

    domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.

    26 Dukan yini yana marmari ya sami ƙari,

    amma mai adalci yakan bayar hannu sake.

  15. 13 Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14 Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. 15 A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” 16 Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne.

  16. 27 Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta,

    amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.

  17. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  18. 7 Gama ku kanku kun san yadda ya kamata ku bi gurbinmu. Ba mu yi zaman banza sa’ad da muke tare da ku ba, 8 ba mu kuwa ci abincin kowa ba tare da ba mu biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki dare da rana, muna fama muna wahala kuma don kada mu nawaita wa waninku. 9 Mun yi wannan, ba don ba mu da ’yancin karɓar irin taimakon nan ba ne, sai dai domin mu zama gurbin da za ku bi. 10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

    11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.

  19. 15 Ragwanci kan jawo zurfin barci,

    mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.

  20. 18 In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa,

    in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.

  21. 60 Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba

    in yi biyayya da umarnanka.

  22. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  23. 1 A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. 2 Gama ya ce,

    “A lokacin samun alherina, na ji ka,

    a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.”

    Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

  24. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.

  25. 9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. 11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.

  26. 26 Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu,

    haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.

  27. 24 Rago kan sa hannunsa a kwano

    ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!

  28. 4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka. 5 Gara kada ka yi alkawari, da ka yi amma ba ka cika ba.

  29. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.

  30. 14 Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.

  31. 17 Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.

  32. 9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

  33. 21 In fa kuka yi alkawari ga Ubangiji Allahnku, to, kada ku yi jinkirin cikawa, gama tabbatacce Ubangiji Allahnku zai neme shi daga gare ku, za ku kuma zama masu laifin zunubi.

  34. 19 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace,

    amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.

  35. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

  36. 6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;

    ku yi kira gare shi tun yana kusa.

  37. 16 Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnku

    kafin ya kawo duhu,

    kafin ƙafafunku su yi tuntuɓe

    a kan tuddai masu duhu.

    Za ku sa zuciya ganin haske

    amma zai mai da shi duhu mai kauri

    ya kuma canja shi zuwa duhu baƙi ƙirin.

  38. 16 Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai.

  39. 11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,

    amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.

  40. 23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

    25 “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku.