75 Bible Verses About Vanity
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Kalmomin Malami, ɗan Dawuda, Sarki a Urushalima.
2 “Ba amfani! Ba amfani!”
In ji Malami.
“Gaba ɗaya ba amfani!
Kome ba shi da amfani!”
3 Wace riba ce mutum yake samu daga wahalar
da yake fama a duniya?
4 Zamanai sukan zo zamanai su wuce,
amma duniya tana nan har abada.
5 Rana takan fito rana ta kuma fāɗi,
ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
6 Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa;
tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
7 Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku,
duk da haka teku ba ya cika.
Daga inda rafuffukan suke fitowa,
a can suke komawa kuma.
8 Dukan abubuwa suna kawo gajiya,
gaban magana.
Ido ba ya gaji da gani,
haka ma kunne yă ƙoshi da ji.
9 Abin da ya taɓa kasancewa, zai sāke kasance,
abin da aka yi za a sāke yi kuma;
babu wani abu sabo a duniya.
10 Akwai wani abin da za a ce,
“Duba! Ga wani abu sabo”?
Abin yana nan, tun dā can,
ya kasance kafin lokacinmu.
11 Ba a tunawa da mutanen dā,
haka su ma da ba a haifa ba tukuna
waɗanda za su biyo bayansu
ba za a tuna da su ba.
-
12 Ni, Malami, sarki ne bisa Isra’ila a Urushalima. 13 Na dauri aniyata in gwada don in bincika ta wurin hikima dukan abin da ake yi a duniya. Kaya mai nauyi ne Allah ya ɗora a kan mutane! 14 Na ga dukan abubuwan da ake yi a duniya, dukansu ba su da amfani, naushin iska ne kawai.
15 Abin da yake tanƙwararre ba zai miƙu ba;
ba za a kuma iya ƙidaya abin da ba shi ba.
16 Na yi tunani a raina na ce, “Duba, na yi girma, na kuma ƙaru da hikima fiye da duk wanda ya taɓa mulki a bisa Urushalima kafin ni; na ɗanɗana hikima mai yawa da kuma ilimi.” 17 Sa’an nan na ɗaura aniyata ga fahimtar hikima, in kuma san bambanci tsakanin hauka da wauta, amma na koyi cewa wannan ma, naushin iska ne kawai.
18 Gama yawan hikima yakan kawo yawan baƙin ciki;
yawan sani, yawan ɓacin rai.
-
1 Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani. 2 Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?” 3 Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.
4 Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. 5 Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. 6 Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa. 7 Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni. 8 Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so. 9 Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba.
10 Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba;
ban hana zuciyata wani jin daɗi ba.
Zuciyata ta yi murna da dukan aikina,
wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.
11 Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana,
da abin da na yi fama don in samu,
sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai;
babu wata riba a duniya.
-
12 Sai na juya ga tunanina don in lura da hikima,
da kuma hauka da wauta.
Me ya rage wa magājin sarki yă yi
fiye da abin da aka riga aka yi?
13 Na ga cewa hikima ta fi wauta,
kamar yadda haske ya fi duhu.
14 Mai hikima ya san inda ya nufa,
wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu;
amma sai na gane
cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu.
15 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma.
Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?”
Na ce a zuciyata,
“Wannan ma ba shi da amfani.”
16 Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba;
nan gaba za a manta da su.
Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima!
17 Don haka na ƙi jinin rayuwa, gama aikin da ake yi a duniya yana ɓata mini rai. Dukan abin da yake cikinta kuwa ba shi da amfani, naushin iska ne kawai. 18 Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana. 19 Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani. 20 Saboda haka zuciyata ta fara karaya a kan dukan faman aikina a duniya. 21 Gama mutum zai yi aikinsa da dukan hikimarsa, da saninsa, da gwanintarsa, sa’an nan dole yă bar dukan abin da ya mallaka ga wani wanda bai yi wahalar kome a ciki ba. Wannan ma ba shi da amfani, hasara ce mai yawa. 22 Me mutum zai samu daga aikin da ya yi duka, da irin ɗawainiyar da ya sha a kan yin aikin a duniya? 23 Dukan kwanakinsa aikinsa damuwa ce da ɓacin zuciya; ko da dare ma hankalinsa ba a kwance yake ba. Wannan ma ba shi da amfani.
24 Ba abin da mutum zai yi da ya fi yă ci, yă sha, yă ji wa ransa daɗi daga aikinsa. Na lura cewa wannan ma, ya fito daga hannun Allah ne, 25 gama in ba tare da shi ba, wa zai iya ci yă sha yă kuma ji daɗi? 26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
-
1 Na sāke dubawa sai na ga zaluncin da ake yi a duniya.
Na ga hawayen waɗanda ake zalunta
kuma ba su da mai taimako;
masu iko suna goyon bayan masu zalunci,
ga shi ba su da mai taimako.
2 Sai na furta cewa matattu,
waɗanda suka riga suka mutu,
sun fi waɗanda suke a raye farin ciki,
waɗanda har yanzu suke da rai.
3 Amma wanda ya fi su duka
shi ne wanda bai riga ya kasance ba,
wanda bai ga muguntar
da ake yi a duniya ba.
4 Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
5 Wawa yakan kame hannuwansa
yă kuma lalatar da kansa.
6 Gara tafin hannu guda cike da kwanciyar rai
da tafin hannu biyu cike da tashin hankali
da harbin iska kawai.
7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.
8 Akwai wani mutum shi kaɗai;
bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.
Ba shi da hutu daga wahalarsa,
duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.
Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala,
kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?”
Wannan ma ba shi da amfani,
harkar baƙin cikin ne kawai!
-
7 Haske da yana da kyau,
abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.
8 Kome tsawon rayuwar mutum,
bari yă more su duka.
Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu,
gama su ma za su yi yawa.
Duk abin da zai faru ba shi da amfani.
9 Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,
bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.
Ka bi shawarar zuciyarka
da kuma duk abin da idanunka suka gani,
amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan
Allah zai shari’anta ka.
10 Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka
ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,
gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.
-
4 “Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata
da kuma yawan kwanakina;
bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
5 Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai;
yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka.
Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum,
har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. Sela
6 “Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa.
Yana ta yawo, amma a banza ne kawai;
yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.
-
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
-
1 Ka tuna da Mahaliccinka
a kwanakin ƙuruciyarka,
kafin lokacin wahala ta zo
shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,
“Ba na jin daɗinsu,”
2 kafin rana da haske
wata da taurari su daina haske,
gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;
3 sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,
majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,
sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,
idanun da suke duba ta taga suka duhunta;
4 sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna
ƙarar niƙa kuma ya tsagaita;
sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane,
ba a kuwa jin waƙoƙinsu,
5 sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu
da kuma hatsarori a tituna;
sa’ad da itacen almon ya toho,
fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar,
sha’awace-sha’awace sun kafe.
Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa
ya bar masu makoki suna ta yi.
6 Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse,
ko tasar zinariya ta fashe;
kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula,
ko guga ta tsinke a rijiya,
7 turɓaya ta koma ƙasar da ta fito,
rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.
8 “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami,
“Gaba ɗaya ba amfani!”
9 Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa. 10 Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.
11 Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda. 12 Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan.
Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki.
13 Yanzu an ji kome;
ga ƙarshen magana.
Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,
gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,
har da waɗanda aka yi a ɓoye,
ko nagari ne, ko mugu.
-
1 Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai. 2 Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.
3 Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa. 4 Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi. 5 Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba, 6 ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?
7 Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa,
duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.
8 Da me mai hikima ya fi wawa?
Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?
9 Gara abin da ido ya gani
da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba.
Wannan ma ba shi da amfani,
naushin iska ne kawai.
10 Duk abin da ya kasance, to, yana da suna,
kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani.
Ba mutumin da zai iya ƙarawa
da wanda ya fi shi ƙarfi.
11 Yadda yawan magana take
haka ƙarancin amfaninta,
yaya wannan zai amfane wani?
12 Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?
-
10 Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;
duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu.
Wannan ma ba shi da amfani.
-
11 Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu;
kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi,
kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela
-
30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;
amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.
-
17 To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.
-
3 Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi,
ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?
4 Mutum yana kama da numfashi;
kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.
-
15 Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.
-
37 Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani;
ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
-
11 Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
-
5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi,
da suka tsaya nesa da ni?
Sun bi gumakan banza
su kansu suka kuma zama banza da kansu.
-
17 Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu. 18 Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure. 19 Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi. 20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. 21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. 22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”
-
2 Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya?
Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela
-
8 Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;
ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
9 Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne?
Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
10 Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne?
Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
11 Ubangiji ya san tunanin mutum;
ya san cewa tunaninsu banza ne.
-
8 Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni;
kada ka ba ni talauci ko arziki,
amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.
-
19 Ya Ubangiji, ƙarfina da katangana,
mafakata a lokacin damuwa,
gare ka al’ummai za su zo
daga iyakokin duniya su ce,
“Kakanninmu ba su mallaki kome ba sai allolin ƙarya,
gumakan banza da ba su yi musu amfani ba.
-
16 Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada.
Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.
-
7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;
wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
-
6 Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza;
na dogara ga Ubangiji.
-
16 Babu ƙarshe ga dukan mutanen da suka riga su. Amma waɗanda suka zo daga baya, ba su gamsu da magājin ba. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.
-
9 Duk masu yin gumaka ba kome ba ne,
da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne.
Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne;
jahilai ne, marasa kunya.
10 Waɗanda suke siffanta allah su kuma yi zubin gunki,
waɗanda ba za su yi musu ribar kome ba?
11 Shi da irinsa za su sha kunya;
masu sassaƙa ba kome ba mutane ne kurum.
Bari su tattaru su ɗauki matsayinsu;
za su firgita su kuma sha mummunan kunya.
-
6 Duk sa’ad da wani ya zo ganina,
yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi;
sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
-
9 Talakawa dai kamar shaƙar iska suke,
Attajirai dai kamar shirim suke;
in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne;
dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
-
33 Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza
shekarunsu kuma cikin masifa.
-
6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya
tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
-
13 Sa’ad da kuka nemi taimako,
bari tarin gumakanku su cece ku!
Iska za tă kwashe dukansu tă tafi,
ɗan numfashi kawai zai hura su.
Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa
zai gāji ƙasar
ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”
-
6 Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. 7 So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.
-
31 Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani
domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.
-
1 Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki
mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
-
7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8 Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum, 9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
-
29 Duba, dukansu masu ƙarya ne!
Ayyukansu ba su da riba;
siffofinsu iska ne kawai da ruɗami.
-
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.
-
8 Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.
-
2 Banza ne ka farka da wuri
ka koma da latti,
kana fama don abincin da za ka ci,
gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
-
19 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace,
amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.
-
13 Ku lura da abin da Allah ya yi.
Wa zai iya miƙe
abin da ya tanƙware?
14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,
amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,
Allah ne ya yi wancan
shi ne kuma ya yi wannan.
Saboda haka, mutum ba zai san
wani abu game da nan gabansa ba.
15 A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu,
mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa,
mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.
-
10 Sa’an nan kuma, na ga an binne masu mugunta, waɗanda suke shiga da fita daga tsattsarkan wuri suke kuma samun yabo a birnin da suka yi wannan. Wannan ma ba shi da amfani.
11 In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba. 12 Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah. 13 Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.
14 Akwai kuma wani abu marar amfani da yake faruwa a duniya, masu adalci sukan sha hukuncin da ya dace da masu mugunta, masu mugunta kuma sukan karɓi sakayyar da ya cancanci masu adalci su samu. Na ce, wannan ma, ba shi da amfani. 15 Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya.
16 Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana, 17 sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.
-
13 Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa;
za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba.
Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe
saboda zafin fushin Ubangiji.”
-
20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”
-
3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.
-
20 Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, 21 wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya.
Alheri yă kasance tare da ku.
-
14 Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. 15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. 16 Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. 17 Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, 18 waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. 19 Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”
20 A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. 21 In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.
22 Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. 24 Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. 25 Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, 26 su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.
-
9 Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. 10 Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. 11 Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.
-
13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
22 Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23 Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24 Gama,
“Dukan mutane kamar ciyawa suke,
darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;
ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,
25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”
Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.
-
15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.
-
11 Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba,
gama taimakon mutum banza ne.
-
11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace,
amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
-
16 Sai na ga wani abu kuma a duniya,
a wurin shari’a, akwai mugunta a can,
a wurin adalci, akwai mugunta a can.
17 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Allah zai shari’anta
masu adalci da masu mugunta,
gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki,
lokaci domin kowane abu.”
18 Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba. 19 Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani. 20 Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma. 21 Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”
22 Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?
-
6 Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya,
haka dariyar wawaye take.
Wannan ma ba shi da amfani.
-
13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani!
Turarenku abin ƙyama ne gare ni.
Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini,
ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
-
32 Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
-
13 “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji Ubangiji.
“Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’
14 “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban Ubangiji Maɗaukaki? 15 A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ”
16 Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.
17 “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata, za su zama nawa,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. 18 Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi.
-
7 Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu.
-
23 Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu. 24 Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu. 25 Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa,
“ ‘Don me ƙasashe suke fushi,
mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?
26 Sarakunan duniya sun ja dāgā,
masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya,
suna gāba da Ubangiji
da kuma Shafaffensa.’
27 Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. 28 Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru. 29 Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali. 30 Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”
31 Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.
-
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
-
9 Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu.
-
14 Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?
-
2 Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka,
amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
-
12 Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku,
ba kuwa za su amfane ku ba.
-
8 Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.
-
14 Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!
Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya
turɓaya kuma za ka ci
dukan kwanakin rayuwarka.
15 Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
16 Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
-
47 Ka tuna yadda raina mai wucewa ne.
Gama ka halicce dukan mutane ba amfani!
-
3 Gama al’adun mutane banza ne;
sukan yanke itace daga kurmi,
sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.
4 Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya;
sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi,
don kada yă fāɗi.
5 Kamar dodon gona cikin gonar kabewa,
haka gumakansu ba sa iya magana;
dole a yi ta ɗaukansu
domin ba za su iya tafiya ba.
Kada ku ji tsoronsu;
ba za su iya yi wa wani lahani ba
ba sa iya yin wani abin kirki.”
-
15 “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu. 16 A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama.
-
10 Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne.
-
17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
-
15 Kaciya ko rashin kaciya ba wani abu ba ne; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta.
Shows Read in context, Share and Copy.