89 Bible Verses About God's Sovereignty
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15 Gama ya ce wa Musa,
“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,
zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”
16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.” 18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.
19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” 21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?
22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai? 25 Kamar yadda ya faɗa a Hosiya.
“Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba;
zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”
26 kuma,
“Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu,
‘Ku ba mutanena ba,’
za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”
-
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?
-
7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.
11 A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12 Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah.
-
8 “Ku tuna da wannan, ku sa shi a zuciya,
ku riƙe shi a zuciya, ku ’yan tawaye.
9 Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā;
ni ne Allah, kuma babu wani;
ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.
10 Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko,
daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba.
Na ce nufina zai tabbata,
kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
11 Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta;
daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina.
Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru;
abin da na shirya, shi zan aikata.
-
11 Girma da iko
da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,
gama kome a sama da ƙasa naka ne.
Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;
an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
12 Wadata da girma daga gare ka suke;
kai ne mai mulkin dukan abubuwa.
A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke
don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
-
32 Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.”
33 Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.
34 A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada.
Mulkinsa dawwammamen mulki ne;
sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani.
35 Dukan mutanen duniya
ba a bakin kome suke ba.
Yakan yi abin da ya gamshe shi
da ikokin sama
da kuma na mutanen duniya.
Babu mai hana shi
ko yă ce masa; “Me ka yi?”
-
3 Allahnmu yana a sama;
yana yin duk abin da ya ga dama.
-
15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.
-
1 A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne
wanda yake bi da shi duk inda ya so.
-
1 Sa’an nan Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
2 “Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;
ba wanda zai iya ɓata shirinka.
3 Ka yi tambaya, ‘Wane ne wannan da ya ƙi karɓar shawarata shi marar ilimi?’
Ba shakka na yi magana game da abubuwan da ban gane ba,
abubuwan ban al’ajabi da sun fi ƙarfin ganewata.
4 “Ka ce, ‘Saurara yanzu, zan kuma yi magana
zan tambaye ka,
kuma za ka amsa mini.’
5 Kunnuwana sun ji game da kai
amma yanzu na gan ka.
6 Saboda haka na rena kaina
na kuma tuba cikin ƙura da toka.”
-
6 Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,
a sammai da kuma a duniya,
cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
7 Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya;
yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama
ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
-
23 Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu,
Ga Allahn da ba a sani ba.
To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku.
24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
29 “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. 30 A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”
-
33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!
Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,
hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?
Ko kuwa yă ba shi shawara?”
35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,
da Allah zai sāka masa?”
36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
-
6 saboda daga fitowar rana
har zuwa fāɗuwarta
mutane za su san cewa babu wani in ban da ni.
Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
7 Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu,
ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i;
ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
8 “Ku sammai, ku sauko da adalci kamar ruwan sama;
bari gizagizai su zubar da yayyafi kamar adalci.
Bari ƙasa ta buɗe,
bari ceto ya tsiro,
bari adalci ya yi girma tare da shi;
ni, Ubangijine, na sa ya faru.
9 “Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,
da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.
Yumɓu ya iya ce wa magini,
‘Me kake yi?’
Aikinka na iya cewa,
‘Ba shi da hannuwa’?
10 Kaiton wanda yake cewa mahaifinsa,
‘Me ka manta?’
Ko kuwa ga mahaifiyarsa,
‘Me kin haifa?’
11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.
Game da abubuwan da ke zuwa,
kun tambaye ni game da ’ya’yana,
ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya
na kuma halicci mutum a kanta.
Hannuwana ne sun miƙe sammai;
na umarci rundunar sararin sama.
13 Zan tā da Sairus cikin adalcina.
Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe.
Zai sāke gina birnina
ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala,
amma ba don wata haya ko lada ba,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
-
26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. 33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
-
13 Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14 Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. 15 A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.” 16 Ga shi, kuna fariya da taƙama. Duk irin wannan taƙama mugun abu ne.
-
20 Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa.
-
5 Sa’an nan Yehoshafat ya miƙe tsaye a taron Yahuda da Urushalima a haikalin Ubangiji a sabon filin 6 ya ce,
“Ya Ubangiji Allah na kakanninmu, ba kai ne Allah wanda yake sama ba? Kana mulki a bisa dukan mulkokin ƙasashe. Iko da girma suna a hannunka, kuma ba wanda zai iya tsayayya da kai.
-
33 Akan jefa ƙuri’a a kan cinya,
amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
-
16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.
-
14 Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne. 15 Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau. 16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. 17 Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.
-
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,
ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,
domin ka halicci dukan abubuwa,
kuma ta wurin nufinka aka halicce su
suka kuma kasance.”
-
1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske.
-
9 ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu,
amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
-
21 Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,
amma manufar Ubangiji ce takan cika.
-
13 Ku lura da abin da Allah ya yi.
Wa zai iya miƙe
abin da ya tanƙware?
14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,
amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,
Allah ne ya yi wancan
shi ne kuma ya yi wannan.
Saboda haka, mutum ba zai san
wani abu game da nan gabansa ba.
-
24 Ubangiji Maɗaukaki ya rantse,
“Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance,
kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
25 Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata;
a kan duwatsuna zan tattake shi.
Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena,
a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
26 Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya;
wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
27 Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi?
Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
-
26 Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”
-
13 I, kuma tun fil azal ni ne shi.
Babu wani da zai amshi daga hannuna.
Sa’ad da na aikata, wa zai iya sauyawa?”
-
37 Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika
in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38 Ba daga bakin Maɗaukaki ne
bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
39 Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni
sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
40 Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta,
sai mu kuma koma ga Ubangiji.
-
8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
-
19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama,
masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.
20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,
ku jarumawa masu yi masa aiki,
waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.
21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,
ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.
22 Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa
ko’ina a mulkinsa.
Yabi Ubangiji, ya raina.
-
51 Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;
ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.
52 Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu
amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53 Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa
amma ya sallami mawadata hannu wofi.
-
44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
-
65 Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
-
10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa;
Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.
-
1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;
duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.
5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
6 Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7 Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
-
27 Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. 28 Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.
-
38 Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe. 39 Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”
-
26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28 Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29 domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”
-
1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, 2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.
-
11 Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. 12 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. 13 Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. 14 Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.
-
39 Ku sani, ku kuma riƙe a zuciya a wannan rana, cewa Ubangiji shi ne Allah a sama da kuma a ƙasa. Babu wani kuma.
-
10 waɗanda suke gāba da Ubangiji za su hallaka.
Zai yi musu tsawa daga sama,
Ubangiji zai hukunta dukan duniya.
“Zai ba wa sarkinsa ƙarfi,
yă kuma ɗaukaka shafaffensa.”
-
31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
-
28 gama mulki na Ubangiji ne
kuma yana mulki a bisa al’ummai.
-
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance;
ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai;
yakan wofintar da manufofin mutane.
11 Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,
manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
-
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
-
4 Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa,
har ma da mugaye domin ranar masifa.
-
21 Ba ku sani ba?
Ba ku taɓa ji ba?
Ba a faɗa muku daga farko ba?
Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya?
22 Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya,
kuma mutanenta suna kama da fāra.
Ya miƙa sammai kamar rumfa,
ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.
23 Yakan mai da sarakuna ba kome ba
yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi.
24 Ba da jimawa ba bayan an shuka su,
ba da jimawa ba bayan an dasa su,
ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa,
sai yă hura musu iska su yanƙwane,
guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.
25 “Ga wa za ku kwatanta ni?
Ko kuwa wa yake daidai da ni?” In ji Mai Tsarkin nan.
26 Ku ɗaga idanunku ku duba sammai.
Wane ne ya halicce dukan waɗannan?
Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya,
yana kiransu, kowanne da sunansa.
Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma,
babu ko ɗayansu da ya ɓace.
-
15 Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan,
Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”
-
37 Gama ba abin da zai gagari Allah.”
-
17 Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.
-
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. 12 Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. 13 Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. 14 Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. 15 Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. 16 A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce,
Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
17 Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, 18 don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”
19 Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. 20 Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. 21 Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.
-
11 Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne?
-
39 “Ku duba yanzu cewa ni ne Shi!
Ba wani allah in ban da ni.
Nakan kashe in kuma rayar,
nakan sa rauni in kuma warkar,
ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
-
11 Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.
-
1 A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa,
2 “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela,
“ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda. 3 Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima. 4 Duk inda akwai mutumin Yahuda da ya rage, sai mutanen da suke zama kusa da shi, su taimake shi da azurfa, da zinariya, da kaya, da kuma dabbobi, tare da kyautai na yardar rai saboda Gidan Allah wanda yake a Urushalima.’ ”
-
6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
2 gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
-
6 Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin;
sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
-
2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne,
Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
-
1 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;
Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.
An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
-
2 An kafa kursiyin tun da daɗewa;
kana nan tun fil azal.
-
Waƙar haurawa.
1 Na tā da idanuna gare ka,
gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
-
3 Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa,
ya albarkace ku daga Sihiyona.
-
16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
-
8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,
yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”
in ji Ubangiji.
9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,
haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa
tunanina kuma dabam da naku.
-
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Sama kursiyina ce,
duniya kuma matashin sawuna.
Ina gidan da za ku gina mini?
Ina wurin hutuna zai kasance?
-
7 Wane ne ba zai girmama ka ba,
Ya Sarkin al’ummai?
Tsoronka wajibi ne.
A cikin dukan masu hikima na al’ummai
kuma cikin dukan mulkokinsu,
babu kamar ka.
-
7 A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, 8 in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. 9 In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, 10 in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.
-
17 “A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.
-
27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?
-
19 Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada;
kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
-
26 A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya, kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum. 27 Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi. 28 Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi.
Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.
-
19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. 20 Ya ce,
“Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;
hikima da iko nasa ne.
21 Yana sāke lokuta,
yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.
Yana ba da hikima ga masu hikima
kuma ilimi ga masu basira.
22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;
ya san abin da yake cikin dare,
haske kuwa yana zaune tare da shi.
23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.
Kai ka san hikima da iko,
ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
-
9 “Ina cikin dubawa,
“sai aka ajiye kursiyoyi,
sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.
Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;
gashin kansa sun yi fari kamar ulu.
Kursiyinsa kuma harshen wuta,
dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.
10 Kogin wuta yana gudu,
yana fitowa daga gabansa.
Dubun dubbai sun yi masa hidima;
dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa.
Aka zauna don shari’a,
aka kuma buɗe littattafai.
-
9 Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.
-
6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7 Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.
-
3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi. 4 A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.
-
12 Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah 13 ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.
-
1 “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. 2 Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. 3 Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. 4 Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
5 “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6 Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.
-
10 Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11 Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
-
5 Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), 6 duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.
-
8 Amma game da Ɗan ya ce,
“Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin,
adalci kuma zai zama sandan mulkinka.
-
17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
-
6 Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.
Shows Read in context, Share and Copy.