39 Bible Verses About God's Wisdom

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Wisdom
  1. 13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,

    mutumin da ya sami fahimi,

    14 gama ta fi azurfa riba

    tana kuma da amfani fiye da zinariya.

    15 Ta fi lu’ulu’u daraja;

    ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.

    16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;

    a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.

    17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,

    dukan hanyoyinta kuma salama ne.

    18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;

    waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.

    19 Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya,

    ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;

    20 ta wurin sani aka rarraba zurfafa,

    gizagizai kuma suka zubo raɓa.

    21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,

    kada ka bar su su rabu da kai;

    22 za su zama rai a gare ka,

    abin adon da zai gyara wuyanka.

    23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,

    ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;

    24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

    sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

    25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya

    ko lalacin da yakan auka wa mugaye,

    26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka

    zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.

  2. 18 Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake cewa,

    “Zan rushe hikimar mai hikima,

    basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

    20 Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21 Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22 Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23 amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24 amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

    26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28 Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29 domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”

  3. 13 Wane ne mai hikima da fahimta a cikinku? Bari yă nuna ta ta wurin rayuwarsa mai kyau, ta wurin ayyukan da aka yi cikin tawali’un da suke fitowa daga hikima. 14 Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. 15 Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma. 16 Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.

    17 Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. 18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

  4. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa. 7 Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji; 8 shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.

  5. 19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama. 20 Ya ce,

    “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin;

    hikima da iko nasa ne.

    21 Yana sāke lokuta,

    yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu.

    Yana ba da hikima ga masu hikima

    kuma ilimi ga masu basira.

    22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa;

    ya san abin da yake cikin dare,

    haske kuwa yana zaune tare da shi.

    23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina.

    Kai ka san hikima da iko,

    ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

  6. 30 Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, 31 haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. 32 Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.

    33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

    Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

    hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

    34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

    Ko kuwa yă ba shi shawara?”

    35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,

    da Allah zai sāka masa?”

    36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

    Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

  7. 1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina

    ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,

    2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,

    kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,

    3 in kuma ka kira ga tsinkaya

    ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,

    4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa

    ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,

    5 to, za ka gane tsoron Ubangiji

    ka kuma sami sanin Allah.

    6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,

    daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.

    7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,

    shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,

    8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata

    yana kuma tsare hanyar amintattunsa.

    9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci

    da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.

    10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka,

    sani kuma zai faranta maka rai.

    11 Tsinkaya za tă tsare ka,

    ganewa kuma za tă yi maka jagora.

    12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane,

    daga kalmomin mutane masu ɓatanci,

    13 waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi

    don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,

    14 waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau

    suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,

    15 waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne

    waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.

  8. 8 Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka;

    ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.

    9 Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima;

    ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.

    10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,

    sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

    11 Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa,

    za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.

    12 In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada;

    in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”

  9. Gabatarwa, manufa da kuma kan magana

    1 Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

    2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

    don ganewa kalmomi masu zurfi;

    3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

    kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

    4 don sa marar azanci yă yi hankali,

    yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

    5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

    bari masu tunani kuma su sami jagora,

    6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,

    kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

    7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

    amma wawaye sun rena hikima da horo.

  10. 24 Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne?

    Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?

    25 Sa’ad da ya shirya wuri da kyau,

    ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba?

    Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsa

    sha’ir a kunyoyinsa,

    tamba kuma a filinsa ba?

    26 Allahnsa ya umarce shi

    ya kuma koya masa hanyar da take daidai.

    27 Ba a bugan kanumfari da ƙaton sanda

    ko a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya;

    akan buga kanumfari da siririn sanda

    ɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.

    28 Dole a niƙa hatsi don a yi burodi;

    saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba.

    Ya san yadda zai sussuke alkamarsa,

    ba tare da ya ɓata tsabarta ba.

    29 Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,

    shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.

  11. 1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba. 2 Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, 3 a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.

  12. 18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21 Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22 ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, 23 ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

  13. 16 Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,

    ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!

  14. 1 Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. 2 Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. 3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

    6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. 8 Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ba idon da ya taɓa gani,

    ba kunnen da ya taɓa ji,

    ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin

    abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

    10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

    Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. 15 Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.

    16 “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji,

    har da zai koya masa?”

    Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.

  15. 1 Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce,

    2 “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata

    da surutan wofi?

    3 Ka sha ɗamara kamar namiji;

    zan yi maka tambaya,

    za ka kuwa amsa mini.

    4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?

    Gaya mini, in ka sani.

    5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!

    Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?

    6 A kan me aka kafa tushenta,

    ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,

    7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare

    dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.

    8 “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi,

    lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.

    9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga

    na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,

    10 sa’ad da na yi masa iyaka na

    sa masa ƙofofi da wurin kullewa.

    11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai,

    ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?

    12 “Ko ka taɓa ba safiya umarni

    ko kuma ka sa asuba ta fito,

    13 don ta kama gefen duniya

    ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?

    14 Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi;

    ta fito a fili kamar riga.

    15 An hana mugaye haskensu,

    hannun da suka ɗaga an karya shi.

    16 “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku,

    ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?

    17 Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa?

    Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?

    18 Ko ka gane fāɗin duniya?

    Gaya mini, in ka san wannan duka.

    19 “Ina ne hanyar zuwa gidan haske?

    Kuma a ina duhu yake zama?

    20 Ko za ka iya kai su wurarensu?

    Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?

    21 Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin!

    Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.

    22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara

    ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara

    23 waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala,

    domin kwanakin yaƙi da faɗa?

    24 Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya,

    ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?

    25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,

    da kuma hanyar walƙiyar tsawa

    26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin

    jeji inda ba mai zama ciki

    27 don a ƙosar da wurin da ya bushe

    a sa ciyawa ta tsiro a can?

    28 Ruwan sama yana da mahaifi?

    Wa ya zama mahaifin raɓa?

    29 Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara?

    Wane ne ya haifi jaura daga sammai

    30 lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse,

    lokacin da saman ruwa ya daskare?

    31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta?

    Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

    32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu

    ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

    33 Ka san dokokin sammai?

    Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?

    34 “Za ka iya tsawata wa gizagizai

    ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?

    35 Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa?

    Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’

    36 Wane ne yake cika zuciya da hikima

    ko kuma yake ba zuciya ganewa?

    37 Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai?

    Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai

    38 sa’ad da ƙura ta yi yawa

    ta daskare a wuri ɗaya?

    39 “Za ka iya farauto wa zakanya nama,

    ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.

    40 Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu,

    ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?

    41 Wane ne yake ba hankaka abinci

    lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah,

    kuma suna yawo don rashin abinci?

  16. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

  17. 15 Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22 Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23 Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

  18. 24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!

    Cikin hikima ka yi su duka;

    duniya ta cika da halittunka.

    25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,

    cike da halittun da suka wuce ƙirga,

    abubuwa masu rai babba da ƙarami.

    26 A can jiragen ruwa suna kai komo,

    kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

  19. 12 Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa,

    ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa?

    Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando,

    ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji,

    tuddai kuma a ma’auni?

    13 Wane ne ya fahimci zuciyar Ubangiji,

    ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?

    14 Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi,

    wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace?

    Wane ne ya koya masa sani

    ko ya nuna masa hanyar fahimta?

  20. 9 “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.

  21. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

    1 Ya Ubangiji, ka bincike ni

    ka kuwa san ni.

    2 Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi;

    ka san tunanina daga nesa.

    3 Ka san fitata da kuma kwanciyata;

    ka saba da dukan hanyoyina.

    4 Kafin in yi magana da harshena

    ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

    5 Ka kewaye ni, gaba da baya;

    ka sa hannunka a kaina.

    6 Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana,

    ya fi ƙarfi in gane.

  22. 28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

  23. 12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;

    ya kafa duniya ta wurin hikimarsa

    ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.

  24. 7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.”

    8 Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa. 9 To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa. 10 Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”

    11 Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, 12 saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”

  25. 8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

    yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”

    in ji Ubangiji.

    9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

    haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

    tunanina kuma dabam da naku.

  26. 8 Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali. 9 An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. 10 Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya. 11 Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  27. 5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

    ganewarsa ba shi da iyaka.

  28. 24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

    28 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29 domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.

  29. 7 “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. 8 Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. 9 Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

    10 Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. 11 Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12 zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. 13 Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. 14 In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”

  30. 28 Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

  31. 22 “Wani zai iya koya wa Allah ilimi

    tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?

  32. 7 Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji.

    Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana

    mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā,

    mene ne kuma bai riga ya faru ba,

    I, bari yă faɗa abin da zai zo.

  33. 7 Wane ne ba zai girmama ka ba,

    Ya Sarkin al’ummai?

    Tsoronka wajibi ne.

    A cikin dukan masu hikima na al’ummai

    kuma cikin dukan mulkokinsu,

    babu kamar ka.

  34. 12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?

    Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?

    13 “Allah ne mai iko da kuma hikima,

    shawara da ganewa nasa ne.

  35. 14 Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku. 15 Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.

  36. 29 Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku. 30 Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma. 31 Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye. 32 Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar. 33 Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi. 34 Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.

  37. 24 To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25 Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

  38. 30 Babu hikima, babu tunani, babu shirin

    da zai yi nasara a kan Ubangiji.

  39. 12 Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa. 13 Gama ya ce,

    “ ‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan,

    da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi.

    Na kau da iyakokin ƙasashe,

    na washe dukiyarsu;

    a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.

    14 Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu

    haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai;

    kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai,

    haka na tattara dukan ƙasashe;

    ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki,

    ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’ ”