114 Bible Verses About Fools

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Fools
  1. 7 Ka guji wawa,

    gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.

    8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,

    amma wautar wawaye ruɗu ne.

    9 Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi,

    amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.

    10 Kowace zuciya ta san ɓacin ranta,

    kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda.

    1 Wawaye sukan ce a ransu,

    “Ba Allah.”

    Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne;

    babu wani da yake yi abu mai kyau.

    2 Ubangiji ya duba daga sama

    a kan ’yan adam

    don yă ga ko akwai wani da ya gane,

    wani wanda yake neman Allah.

    3 Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu;

    babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau,

    ba ko ɗaya.

    4 Masu aikata mugunta za su taɓa koyo.

    Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa

    kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?

    5 Ga su, tsoro ya sha kansu,

    gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.

    6 Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza,

    amma Ubangiji ne mafakansu.

  3. Gabatarwa, manufa da kuma kan magana

    1 Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

    2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

    don ganewa kalmomi masu zurfi;

    3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

    kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

    4 don sa marar azanci yă yi hankali,

    yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

    5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

    bari masu tunani kuma su sami jagora,

    6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,

    kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

    7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

    amma wawaye sun rena hikima da horo.

    Gargaɗi don a rungumi hikima

    8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

    9 Za su zama kayan ado don su inganta ka

    da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

  4. 11 In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi,

    ina amfanin maganin?

    12 Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne,

    amma maganganun wawa za su hallaka shi.

    13 Farkon maganarsa wauta ce,

    ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,

    14 wawa kuma yakan yi ta surutu.

    Ba wanda ya san abin da zai zo

    wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

    15 Aikin wawa yakan gajiyar da shi,

    har bai san hanyar zuwa gari ba.

  5. 6 Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa,

    bakinsa kuma kan gayyaci dūka.

    7 Bakin wawa lalatar da kansa yake yi

    leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.

  6. 10 Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni

    haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.

    11 Kamar yadda kare kan koma ga amansa,

    haka wawa kan maimaita wautarsa.

    12 Gwamma riƙaƙƙen wawa

    da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

  7. 19 Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai,

    amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.

    20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,

    amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.

  8. 5 Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,

    in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.

    6 Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi

    haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.

    7 Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas

    haka karin magana yake a bakin wawa.

  9. 15 Hanyar wawa daidai take a gare shi,

    amma mai hikima kan saurari shawara.

  10. 1 Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.

    2 Kada ka yi subul da bakinka,

    kada zuciyarka tă yi garajen

    furta wani abu a gaban Allah.

    Allah yana sama

    kai kuma kana duniya,

    saboda haka, kada kalmominka su zama da yawa.

    3 Kamar yadda son cika buri yakan zo sa’ad da kana da yawan damuwa,

    haka jawabin wawa yake sa’ad da yake yawan magana.

    4 Sa’ad da ka yi alkawari ga Allah, kada ka ɓata lokaci wajen cika shi. Ba ya jin daɗin wawaye; ka cika alkawarinka.

  11. 2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta

    amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

    3 Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo,

    haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.

  12. 23 Wawa yakan ji daɗi halin mugunta,

    amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.

    24 Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi;

    abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.

    25 Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye,

    amma adalai za su tsaya daram har abada.

  13. 11 Wawa yakan nuna fushinsa a fili,

    amma mai hikima kan kanne fushinsa.

  14. 18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.

    21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. 22 Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye, 23 suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

    24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

    26 Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. 27 Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

    28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

  15. 26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne,

    amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.

  16. 20 Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,

    tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;

    21 tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,

    tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.

    22 “Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?

    Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku

    wawaye kuma ku ƙi ilimi?

  17. 1 Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, 2 kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane.

    3 A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. 4 Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5 sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6 wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, 7 wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. 8 Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum.

    9 Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. 10 Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. 11 Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.

  18. 18 Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa,

    duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.

    19 Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki,

    amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.

  19. 9 Kada ranka yă yi saurin tashi,

    gama fushi yana zama a cinyar wawaye.

  20. 18 Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake cewa,

    “Zan rushe hikimar mai hikima,

    basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

    20 Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21 Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22 Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23 amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24 amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

    26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28 Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29 domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”

  21. 28 “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba;

    za su neme ni amma ba za su same ni ba.

    29 Da yake sun ƙi sani

    ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

    30 da yake ba su karɓi shawarata ba

    suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

    31 za su sami sakayyar abubuwan da suka yi

    su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

    32 Gama rashin hankalin marasa azanci zai kashe su,

    rashin kulawar wawaye kuma zai hallaka su;

    33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya

    yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”

  22. 1 Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare,

    haka ’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.

    2 Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai,

    amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.

    3 Ko yayinda yake tafiya a kan hanya

    wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali,

    yakan nuna wa kowa wawancinsa.

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat. Wani maskil na Dawuda.

    1 Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa,

    “Ba Allah.”

    Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau;

    babu wani mai aikata abu mai kyau.

  24. 3 Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa,

    amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.

  25. 8 Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni

    amma surutun wawa kan kai ga lalaci.

  26. 16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

    18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

    20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

    21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

  27. 13 Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi,

    amma bulala domin bayan marasa azanci ne.

    14 Mai hikima kan yi ajiyar sani,

    amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.

  28. 24 Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,

    amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.

    25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa

    da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.

  29. 16 “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’ 17 Wawaye makafi! Wanne ya fi girma, zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18 Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’ 19 Makafi kawai! Wanne ya fi girma, bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar? 20 Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa. 21 Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22 Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.

    23 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba. 24 Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.

    25 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai. 26 Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta.

    27 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta. 28 Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.

  30. 35 Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna,

    amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.

  31. 24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

  32. 5 Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,

    amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.

  33. 14 Mai hikima ya san inda ya nufa,

    wawa kuwa yana tafiya a cikin duhu;

    amma sai na gane

    cewa ƙaddara ɗaya ce take samunsu.

    15 Sai na yi tunani a zuciyata,

    “Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma.

    Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?”

    Na ce a zuciyata,

    “Wannan ma ba shi da amfani.”

    16 Gama ba za a ƙara tunawa da mai hikima ko wawa ba;

    nan gaba za a manta da su.

    Yadda wawa zai mutu, haka ma mai hikima!

  34. 17 Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa

    suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.

  35. 2 Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani,

    amma bakin wawa kan fitar da wauta.

  36. 5 Wawa yakan kame hannuwansa

    yă kuma lalatar da kansa.

  37. 8 Masu ba’a kan kuta faɗa a birni,

    amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

    9 In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa,

    wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.

  38. 16 Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta,

    amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.

  39. 7 Leɓunan masu hikima sukan baza sani;

    ba haka zukatan wawaye suke ba.

  40. 29 An shirya tara saboda masu ba’a ne,

    dūka kuma saboda bayan wawaye.

  41. 9 Kada ka yi magana da wawa,

    gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.

  42. 11 Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.

    12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

    14 Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa 15 don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” 16 Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.

  43. 18 Ka tuna da yadda abokin gāba ya yi maka ba’a, ya Ubangiji,

    yadda wawaye suka ɓata sunanka.

    19 Kada ka ba da ran kurciyarka ga namun jeji;

    kada ka manta har abada da rayukan mutanenka masu shan azaba.

    20 Ka kula da alkawarinka,

    domin akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar.

    21 Kada ka bar waɗanda ake danniya su sha kunya;

    bari matalauta da mabukata su yabe sunanka.

    22 Ka tashi, ya Allah, ka kāre muradinka;

    ka tuna yadda wawaye suka yi maka ba’a dukan yini.

  44. 1 Gara matalauci wanda yake marar laifi

    da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.

  45. 22 Ko da ka daka wawa a turmi,

    kana daka shi kamar hatsi da taɓarya,

    ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.

  46. 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.

  47. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.

  48. 10 Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki

    surutun wawa kuma kan zo da lalaci.

  49. 16 Wawa kan nuna fushinsa nan take,

    amma mai la’akari kan ƙyale zargi.

  50. 22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,

    amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

    23 Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa,

    amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.

  51. 20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,

    amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.

    21 Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki,

    amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.

  52. 28 Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne,

    da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

  53. 1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,

    haka girmamawa bai dace da wawa ba.

  54. 6 Gama wawa maganar wauta yakan yi,

    zuciyarsa ta cika da mugunta,

    yana aikata abubuwan rashin sanin Allah

    yana baza kurakurai game da Ubangiji;

    yana barin mayunwata da yunwa

    ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.

  55. 6 Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu;

    yi tafiya a hanyar fahimi.

    7 “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi

    duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.

    8 Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka;

    ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.

  56. 13 Wawancin mace a bayyane yake;

    ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.

    14 Takan zauna a ƙofar gidanta,

    a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,

    15 tana kira ga masu wucewa,

    waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.

    16 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!”

    Tana ce wa marasa hankali.

    17 “Ruwan da aka sata ya fi daɗi;

    abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”

    18 Amma ba su san cewa matattu suna a can ba,

    cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.

  57. 6 Mutum marar azanci ba zai sani ba,

    wawa ba zai gane ba,

    7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa

    kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka,

    za a hallaka su har abada.

    8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.

    9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji,

    tabbatacce abokan gābanka za su hallaka;

    za a watsar da dukan masu aikata mugunta.

  58. 5 Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali;

    ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.

  59. 6 Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome,

    amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.

  60. 12 Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya

    fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.

  61. 13 Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne,

    mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.

    14 Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,

    amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

  62. 20 Ka ga mutum mai yin magana da garaje?

    To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.

  63. 17 Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa

    ta fi ihun mai mulkin wawaye.

  64. 22 “Mutanena wawaye ne;

    ba su san ni ba.

    Su ’ya’ya ne marasa azanci;

    ba su da fahimi.

    Suna da dabarar aikata mugunta;

    ba su san yadda za su aikata alheri ba.”

  65. 8 Dukansu marasa azanci ne wawaye;

    gumakan itacen banza ne suke koya musu.

  66. 18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21 Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22 ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, 23 ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

  67. 10 Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu!

  68. 2 Fushi yana kashe wawa,

    ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.

    3 Ni ma na ga wawa yana cin gaba,

    amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne.

  69. 5 Masu fariya ba za su iya tsaya

    a gabanka ba.

    Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

  70. 5 Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji;

    suna danne gādonka.

    6 Suna kashe gwauraye da kuma baƙi;

    suna kisan marayu.

    7 Suna ce, “Ubangiji ba ya gani;

    Allah na Yaƙub bai kula ba.”

    8 Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;

    ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?

  71. 16 Kowane mai azanci yakan nuna sani,

    amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.

  72. 3 Bulala don doki, linzami don jaki,

    sanda kuma don bayan wawaye!

  73. 17 Kada ka cika yin mugunta,

    kada kuma ka cika yin wauta,

    don me za ka mutu kafin lokacinka?

  74. 39 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta. 40 Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba?

  75. 16 Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa,

    da yake ba shi da sha’awar samun hikima?

  76. 20 A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau,

    amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.

  77. 11 Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai;

    mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani.

    Yaya za ka ce wa Fir’auna,

    “Ni ɗaya ne cikin masu hikima,

    almajirin sarakuna na dā can”?

    12 Ina masu hikima suke yanzu?

    Bari su nuna maka su kuma sanar

    da abin da Ubangiji Maɗaukaki

    ya shirya a kan Masar.

    13 Shugabannin Zowan sun zama wawaye,

    an ruɗe shugabannin Memfis

    dutsen kan kusurwa na mutanenta

    su sa Masar ta kauce.

  78. 21 Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci,

    waɗanda suke da idanu amma ba sa gani,

    waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji.

    22 Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji.

    “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba?

    Na sa yashi ya zama iyakar teku,

    madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba.

    Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba;

    za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.

    23 Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne;

    sun kauce suka kuma rabu da ni.

    24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,

    wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,

    wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’

    25 Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa;

    zunubanku sun hana ku samun alheri.

  79. 7 Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.

  80. 21 Leɓunan adalai kan amfane yawanci,

    amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.

  81. 3 Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa,

    amma leɓunan masu hikima kan tsare su.

  82. 24 Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu,

    amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.

  83. 7 Leɓunan basira ba su dace da wawa ba,

    ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!

  84. 5 Gara ka saurari tsawatawar mai hikima

    da ka saurari waƙar wawaye.

  85. 10 Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa;

    wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka

    su bar wa waɗansu arzikinsu.

  86. 1 Mace mai hikima kan gina gidanta,

    amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.

  87. 9 Makircin wawa zunubi ne,

    mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.

  88. 8 Kamar ɗaura dutse a majajjawa

    haka yake da girmama wawa.

  89. 3 Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce,

    amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.

  90. 8 Da me mai hikima ya fi wawa?

    Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?

  91. 6 Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya,

    haka dariyar wawaye take.

    Wannan ma ba shi da amfani.

  92. 11 Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba

    haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba.

    A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi,

    a ƙarshe kuma zai zama wawa.

  93. 32 “Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33 Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34 Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.

    35 “Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36 In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci.

  94. 17 Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima

    yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.

  95. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  96. 29 Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai,

    kuma wawa zai zama bawan masu hikima.

  97. 12 Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum,

    amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.

  98. 15 Marar azanci kan gaskata kome,

    amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.

  99. 33 Hikima tana a zuciyar mai azanci,

    kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.

  100. 14 Zuciya mai la’akari kan nemi sani,

    amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.

  101. 22 Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi,

    amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.

  102. 21 Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki

    babu farin ciki ga mahaifin wawa.

  103. 13 Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,

    wannan wauta ce da kuma abin kunya.

  104. 10 Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba,

    haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!

  105. 7 Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai

    a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.

  106. 22 bawan da ya zama sarki,

    wawan da ya ƙoshi da abinci,

  107. 19 Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani.

  108. 4 Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki,

    amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.

  109. 5 Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba

    ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.

  110. 19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20 Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21 Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.

  111. 39 Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?

  112. 46 “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa? 47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata. 48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi. 49 Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”

  113. 24 Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. 25 Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. 26 To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. 27 A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

  114. 12 Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. 13 Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. 14 Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.