40 Bible Verses About Integrity
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
3 Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su,
amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
4 Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi,
amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
5 Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu,
amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.
6 Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su,
amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.
7 Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka;
dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.
8 Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala,
sai ta dawo wa mugu a maimako.
9 Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa,
amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.
10 Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki;
sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.
11 Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita,
amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.
-
Ta Dawuda.
1 Ka nuna rashin laifina, ya Ubangiji,
gama na yi rayuwa marar zargi;
Na dogara ga Ubangiji
ba tare da kaucewa ba.
2 Ka jarraba ni, ya Ubangiji, ka kuma gwada ni,
ka bincike zuciyata da tunanina;
3 gama ƙaunarka kullum tana a gabana,
kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.
4 Ba na zama tare da masu ruɗu,
ko in yi tarayya da masu riya;
5 na ƙi jinin taron masu aikata mugunta
na ƙi in zauna tare da mugaye.
6 Na wanke hannuwana cikin rashin laifi,
ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,
7 ina shelar yabonka da ƙarfi
ina faɗin dukan ayyukanka masu banmamaki.
8 Ina ƙaunar gidan da kake zama, ya Ubangiji,
wurin da ɗaukakarka ke zaune.
9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi
raina tare da masu son yin kisankai
10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,
waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
11 Amma na yi rayuwa marar zargi;
ka cece ni ka kuma yi mini jinƙai.
12 Ƙafafuna suna tsaye daram;
cikin taro mai girma zan yabi Ubangiji.
-
9 Mai mutunci yana tafiya lafiya,
amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
-
6 Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne,
amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
7 Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
-
1 Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar, 2 ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. 3 To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa. 4 A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. 5 A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”
-
19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru
da kuma yadda suka ƙara ƙina!
20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
21 Bari mutunci da adalci su tsare ni,
domin begena yana a kanka.
-
4 “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, 5 zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’
-
3 Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.”
-
11 Na sani kana jin daɗina,
gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
12 Cikin mutuncina ka riƙe ni
ka sa ni a gabanka har abada.
13 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,
har abada abadin.
Amin kuma Amin.
-
6 Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi
da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.
-
1 Gara matalauci wanda yake marar laifi
da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
-
9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”
10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”
A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
-
5 Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita ’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.”
6 Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba.
-
8 bari Ubangiji mai shari’ar mutane.
Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina,
bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.
-
Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Zan rera wa ƙauna da adalcinka;
gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.
2 Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi,
yaushe za ka zo gare ni?
Zan bi da sha’anin gidana
da zuciya marar abin zargi
-
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
-
22 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya cikin kome; kada ku yi aikin ganin ido kamar masu neman yabon mutane, sai dai ku yi aiki tsakaninku da Allah, kamar masu tsoron Ubangiji. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
-
1 Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki. 2 Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro. 3 Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
4 Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”
5 Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.”
Suka ce, “I, shi ne shaida.”
-
70 Ya zaɓi Dawuda bawansa
ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;
71 daga kiwon tumaki ya kawo shi
don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub,
na Isra’ila gādonsa.
72 Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya;
da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.
-
7 Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo 8 da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.
-
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
-
1 Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,
2 “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata,
Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3 Muddin ina da rai a cikina
kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4 bakina ba zai faɗi mugun abu ba,
harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
5 Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba;
har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
6 Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba;
lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.
-
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,
amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
-
5 Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. 6 Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. 7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.
-
4 Bai ga hanyoyina ba ne
bai ƙirga kowace takawata ba?
5 “In da na yi tafiya cikin rashin gaskiya
ko kuma ƙafata ta yi sauri zuwa yin ƙarya,
6 Bari Allah yă auna a kan ma’auni na gaskiya
zai kuma san cewa ni marar laifi ne.
7 In takawata ta kauce daga hanya,
in zuciyata ta bi abin da idanuna ke so,
ko kuma in hannuwana suna da laifi;
8 bari waɗansu su ci abin da na shuka,
kuma bari a tuge amfanin gonata.
-
31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
-
2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.
-
8 Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata. 9 Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?” 10 Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.
11 Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki. 12 Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
-
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya,
shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata
yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
-
3 Yin abin da yake daidai da kuma nagari
Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
-
25 Bari idanunka su dubi gaba sosai,
ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
26 Ka san inda ƙafafunka suke takawa
ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
27 Kada ka kauce dama ko hagu;
ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.
-
6 Adalci yakan lura da mutum mai mutunci,
amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
-
3 Idanun Ubangiji suna a ko’ina,
suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.
-
18 Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya,
amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.
-
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
-
22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23 Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!
-
10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.
-
16 Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.
-
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
-
2 Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba.
Shows Read in context, Share and Copy.