45 Bible Verses About Fathers

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Fathers
  1. 4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

  2. 13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

    haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

  3. 19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

  4. 11 Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji

    kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

    12 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

  5. 22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,

    kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

    23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;

    ka nemi hikima, horo da fahimi.

    24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

    duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

  6. 6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,

    kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

  7. 7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9 Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10 Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

  8. 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  9. 15 Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa.”

  10. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  11. 9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

  12. 17 “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

    “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

    21 “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

    22 “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. 23 Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. 24 Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.

  13. 8 Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.

    9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

    “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

    a tsarkake sunanka,

    10 mulkinka yă zo

    a aikata nufinka a duniya

    kamar yadda ake yi a sama.

    11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

    12 Ka gafarta mana laifofinmu,

    kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

    13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

    amma ka cece mu daga mugun nan. ’

    14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

  14. 26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

    kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

  15. 13 Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. 14 Ku yi kome da ƙauna.

  16. 7 Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;

    masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.

  17. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  18. 17 “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  19. 14 Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata. 15 Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

  20. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

    25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.

  21. 15 “Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  22. 5 Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.

  23. Karin maganar Solomon

    1 Karin maganar Solomon.

    Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,

    amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

  24. 8 Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu.

    Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane;

    dukanmu aikin hannunka ne.

  25. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.

  26. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba. 4 Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace. 5 (In mutum bai san yadda zai tafiyar da iyalinsa ba, yaya zai iya kula da ikkilisiyar Allah?)

  27. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  28. 1 Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.

  29. 4 Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.

  30. 3 “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  31. 10 Sa’an nan Mika ya ce masa, “Ka zauna tare da ni ka zama mini mahaifi da firist, zan kuwa ba ka azurfa goma na shekel a shekara, tufafinka da kuma abincinka.” Sai Balawen ya tafi.

  32. Gargaɗi don a rungumi hikima

    8 Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  33. 1 Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

    ku mai da hankali, ku sami fahimi.

    2 Ina ba ku sahihiyar koyarwa,

    saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

    3 Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,

    yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

    4 ya koya mini ya ce,

    “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;

    ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

  34. 24 Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,

    amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.

  35. 2 Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su.

  36. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

  37. 5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

    shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

    6 Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai,

    ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi;

    amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.

  38. 20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

    kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

  39. 5 Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,

    amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.

  40. 16 Amma kai Ubanmu ne,

    ko Ibrahim bai san mu ba

    Isra’ila kuma bai yarda da mu ba;

    kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu,

    Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.

  41. 4 Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ 5 Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6 ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.

  42. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

  43. 14 Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu. 15 Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara. 16 Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni. 17 Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

  44. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

    4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

  45. 4 Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5 domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya. 6 Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”