64 Bible Verses About Gifts

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Gifts
  1. 1 To, game da baye-baye na ruhaniya, ’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani. 2 Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana. 3 Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.

    4 Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. 5 Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. 6 Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.

    7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11 Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.

  2. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

    3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7 In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; 8 in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.

  3. 1 A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. 2 Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna. 3 Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna. 4 Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku. 5 Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya, 6 Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

    7 Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba. 8 Shi ya sa aka ce,

    “Sa’ad da ya hau sama,

    ya bi da kamammu kamar tawagarsa

    ya kuma ba da baye-baye ga mutane.”

    9 (Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba? 10 Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.) 11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. 12 Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. 13 Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.

    14 An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. 15 Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan 16 dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.

  4. 27 To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28 A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri. 29 Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? 30 Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? 31 Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma.

    Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.

  5. 10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam. 11 In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.

  6. 12 Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.

    13 Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka. 14 Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa.

    15 Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa! 16 Kyautar Allah kuwa ba kamar sakamakon da ya bi zunubin mutum gudan nan ba ne, Hukuncin ya bi zunubin mutum gudan nan, ya kuma kawo hallaka, amma kyautar ta bi laifofin masu yawa ta kuma sa Allah ya gan mu a matsayin marasa laifi. 17 Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.

    18 Saboda haka, kamar yadda sakamakon laifin mutum guda ya jawo hallaka ga dukan mutane, haka ma sakamakon aikin adalci guda ya sa Allah ya same mu marasa laifi, wannan kuwa kawo rai ga dukan mutane. 19 Gama kamar yadda ta wurin rashin biyayyar mutum guda, mutane masu yawa suka zama masu zunubi, haka kuma ta wurin biyayyar mutum guda, mutane da yawa za su zama masu adalci.

    20 An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai, 21 domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.

  7. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  8. 9 “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 10 Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.

    11 “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, 12 ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? 13 In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”

  9. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  10. 3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.

    6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  11. 7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

    9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!

  12. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. 18 Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. 19 Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. 20 Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. 21 Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

  13. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

    4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

    8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare. 9 Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne. 10 Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe. 11 Sa’ad da nake yaro, na yi magana kamar yaro, na yi tunani kamar yaro, na yanke shawara kamar yaro. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin yarantakata. 12 Yanzu kam muna ganin abubuwa kamar a madubi sai dai ba sosai ba, amma a ranan nan za mu gani fuska da fuska. Yanzu kam sanina ba cikakke ba ne, amma a ranan nan zan kasance da cikakken sani, kamar dai yadda Allah ya san ni a yanzu.

    13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  14. 23 Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  15. 6 Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7 Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. 8 Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ya ba gajiyayyu hannu sake,

    ayyukansa na alheri madawwama ne.”

    10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

    12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15 Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!

  16. 11 Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa. 12 Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. 13 Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. 14 Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.

    15 Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. 16 Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.

  17. 10 Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”

  18. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

  19. 38 Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.

  20. 10 Rana guda a filayen gidan sun fi

    dubu a wani wuri dabam;

    zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna

    da in zauna a tentunan mugaye.

    11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

    Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

    ba ya hana kowane abu mai kyau

    wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

    12 Ya Ubangiji Maɗaukaki,

    mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

  21. 23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.

  22. 7 Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

    8 To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. 9 Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

  23. 12 Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. 13 Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.

  24. 19 Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah. 20 Da ƙyar yake tunani a kan kwanakin rayuwarsa, domin Allah ya yarje masa, yă zauna da farin ciki.

  25. 1 Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin. 2 Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu. 3 Sai ya ce, “Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran. 4 Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”

  26. 29 gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.

  27. 18 Sa’ad da ka hau bisa,

    ka bi da kamammu cikin tawagarka;

    ka karɓi kyautai daga mutane,

    har ma daga ’yan tawaye,

    don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.

  28. 1 Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,

    2 Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.

    3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

    4 Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5 Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku 6 gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. 7 Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  29. 1 Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. 2 Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, 3 yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi. 4 Allah shi ma ya shaida ta wurin alamu, abubuwan banmamaki da mu’ujizai iri-iri, da kuma baye-bayen Ruhu Mai Tsarki da aka rarraba bisa ga nufinsa.

  30. 44 Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon. 45 Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai. 46 Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah.

    Sai Bitrus ya ce, 47 “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.” 48 Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki.

  31. 11 Ina marmarin ganinku don in ba ku wata baiwar ruhaniya, don ku yi ƙarfi 12 wato, don ni da ku mu ƙarfafa juna ta wurin bangaskiyarmu.

  32. 3 Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa. 4 Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.

    5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.

    10 Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

  33. 13 Saboda haka aka kawo Daniyel a gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Kai ne Daniyel ɗin nan, ɗaya daga cikin kamammu waɗanda mahaifina sarki ya kawo daga Yahuda? 14 Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima. 15 An kawo masu hikima da masu dabo a gabana domin su karanta wannan rubutu su kuma faɗa mini abin da yake nufi, amma ba su iya ba. 16 Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”

    17 Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.

  34. 9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

  35. 20 Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!

  36. 1 Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba. 2 Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. 3 Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.

    4 Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, 5 waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, 6 ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a. 7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah. 8 Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.

  37. 11 Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba. 12 To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna, 13 sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, 14 to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. 15 Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. 16 Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya. 17 Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.” 18 Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.

    19 In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku. 20 Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba.

  38. 6 Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki,

    kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.

  39. 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?

  40. 23 Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. 24 Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai.

  41. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  42. 16 Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa

    yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.

  43. 3 Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku? 4 Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’ 5 Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’ 6 ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.

  44. 29 Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya. 30 Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

  45. 1 To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. 2 A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba. 3 In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.

  46. 19 Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.

  47. 18 Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna. 19 Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.

    20 Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su. 21 Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta. 22 Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.”

  48. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

  49. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  50. 6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

    “Allah yana gāba da masu girman kai

    amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”

  51. 1 “ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

    2 “ ‘Ku kiyaye Asabbataina, ku kuma ba wa wuri mai tsarkina girma. Ni ne Ubangiji.

    3 “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5 Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.

    6 “ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba. 7 Za ku kori abokan gābanku, za su kuwa fāɗi a kaifin takobi a gabanku. 8 Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku.

    9 “ ‘Zan dube ku da idon rahama, in kuma sa ku riɓaɓɓanya ku kuma ƙaru, zan kiyaye alkawarina da ku. 10 Za ku ci gaba da cin girbin bara, har ku fitar da shi don ku sami wurin saboda sabo. 11 Zan kafa wurin zamana a cikinku, ba zan kuma yi ƙyamarku ba. 12 Zan yi tafiya a cikinki in kuma zama Allahnku, za ku kuwa zama mutanena. 13 Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar don kada ku ƙara zama bayi ga Masarawa; na karya sandunan wahalarku, na kuma bar ku ku yi tafiya a sake.

  52. 1 Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.

  53. 26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  54. 19 Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. 20 Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

  55. 11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

  56. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  57. 32 Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. 33 Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”

  58. 7 Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

  59. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  60. 17 Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

  61. 7 A wannan dare Allah ya bayyana ga Solomon, ya ce masa, “Roƙi duk abin da kake so in ba ka.”

    8 Solomon ya amsa wa Allah, “Ka nuna alheri mai girma ga Dawuda mahaifina ka kuma naɗa ni sarki a matsayinsa. 9 To, yanzu, ya Ubangiji Allah, ka cika alkawarin da ka yi ga mahaifina Dawuda yă tabbata, gama ka naɗa ni sarki a bisa mutanen da suka wuce ƙirge kamar ƙurar ƙasa. 10 Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”

    11 Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, 12 saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”

    13 Sa’an nan Solomon ya tafi Urushalima daga masujadar kan tudu a Gibeyon, da kuma daga gaban Tentin Sujada. Ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila.

  62. 11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa;

    Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

  63. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5 domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

  64. 25 Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai.