36 Bible Verses About Restoration

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Restoration
  1. 19 Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, 20 don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan. 21 Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.

  2. 18 Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa

    yă kuma ji tausayin mutanensa.

    19 Ubangiji zai amsa musu ya ce,

    “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,

    isashe da zai ƙosar da ku sosai;

    ba kuma zan ƙara maishe ku

    abin dariya ga al’ummai ba.

    20 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku,

    in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma,

    kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku

    da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.

    Warinsu kuma zai bazu;

    ɗoyinsu zai tashi.”

    Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.

    21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;

    ki yi murna ki kuma yi farin ciki.

    Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.

    22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,

    gama wuraren kiwo sun yi kore shar.

    Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;

    itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.

    23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,

    ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,

    gama ya ba ku

    ruwan bazara cikin adalci.

    Yakan aika muku yayyafi a yalwace,

    na bazara da na kaka, kamar dā.

    24 Masussukai za su cika da hatsi;

    randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.

    25 “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru

    waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,

    da kuma sauran fāra da tarin fāra

    babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.

    26 Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,

    za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,

    wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;

    mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

  3. 12 Ka mayar mini farin cikin cetonka

    ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

    13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka,

    masu zunubi kuma za su komo gare ka.

  4. 1 ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.

  5. 1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

    5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

  6. 17 Amma zan mayar muku da lafiya

    in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji,

    ‘domin ana ce da ku yasassu,

    Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’

  7. 10 Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.

  8. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

    3 yakan maido da raina.

    Yakan bi da ni a hanyoyin adalci

    saboda sunansa.

    4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

    5 Ka shirya mini tebur

    a gaban abokan gābana.

    Ka shafe kaina da mai;

    kwaf nawa ya cika har yana zuba.

    6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi

    dukan kwanakin raina,

    zan kuwa zauna a gidan Ubangiji

    har abada.

  9. 13 “Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji,

    “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi

    mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi.

    Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu

    yă kuma kwararo daga tuddai.

    14 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila.

    “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu.

    Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu;

    za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.

    15 Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu,

    ba kuwa za a ƙara tumɓuke su

    daga ƙasar da na ba su ba,”

    in ji Ubangiji Allahnku.

  10. 20 Ko da yake ka sa na ga wahaloli,

    masu yawa da kuma masu ɗaci,

    za ka sāke mayar mini da rai;

    daga zurfafan duniya

    za ka sāke tā da ni.

    21 Za ka ƙara girmana

    ka sāke ta’azantar da ni.

  11. 10 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”

  12. 12 Ku koma maɓuya, ya ku ’yan kurkuku masu sa zuciya;

    ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.

  13. 22 Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. 23 Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”

    24 Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”

    25 Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.

  14. 1 “Ku zo, mu koma ga Ubangiji.

    Ya yayyage mu kucu-kucu

    amma zai warkar da mu;

    ya ji mana ciwo

    amma zai daure mana miyakunmu.

  15. 14 Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, 15 don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”

    16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  16. 5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” 6 Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.

    7 Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”

    8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”

    9 Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.

  17. 10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

  18. 6 Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”

    7 Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.

  19. 17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!

  20. 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.

  21. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  22. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, 3 ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4 sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. 5 Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  23. 7 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!

    Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa,

    bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

  24. 17 “Matalauta da mabukata suna neman ruwa,

    amma babu kome;

    harsunansu sun bushe saboda ƙishi.

    Amma Ni Ubangiji zan amsa musu;

    Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.

    18 Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai,

    maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka.

    Zan mai da hamada tafkunan ruwa,

    busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.

    19 Zan sa a hamada ta tsiro da

    al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun.

    Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa,

    tare da fir da kuma saifires,

    20 don mutane su gani su kuma sani,

    su lura su kuma fahimci,

    cewa hannun Ubangiji ne ya aikata haka,

    cewa Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya sa abin ya faru.

  25. 18 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub

    in kuma ji tausayin wuraren zamansa;

    za a sāke gina birnin a kufansa,

    fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.

    19 Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya

    da kuma sowa ta farin ciki.

    Zan riɓaɓɓanya su,

    ba za su kuwa ragu ba;

    zan kawo musu ɗaukaka,

    ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.

    20 ’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā

    jama’arsu kuma za su kahu a gabana;

    zan hukunta duk wanda ya zalunce su.

    21 Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu;

    mai mulkinsu zai taso daga cikinsu.

    Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni,

    gama wane ne zai miƙa kansa

    don yă yi kusa da ni?’

    In ji Ubangiji.

    22 ‘Saboda haka za ku zama mutanena,

    ni kuwa in zama Allahnku.’ ”

  26. 27 “Ni ne Ubangiji Allah na dukan ’yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?

  27. 32 A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.

    33 Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34 Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”). 35 Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

  28. 43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.

  29. 2 A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3 Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4 Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.

  30. 25 Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika. 26 Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Mai ceto zai zo daga Sihiyona;

    zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.

    27 Wannan kuwa shi ne alkawarina da su

    sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”

  31. 16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

  32. 10 Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa! 11 Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

    12 Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.”

    Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.

  33. 31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  34. 14 Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;

    ka cece ni zan kuwa cetu,

    gama kai ne nake yabo.

  35. 9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

    “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

    a tsarkake sunanka,

    10 mulkinka yă zo

    a aikata nufinka a duniya

    kamar yadda ake yi a sama.

    11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

    12 Ka gafarta mana laifofinmu,

    kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

    13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

    amma ka cece mu daga mugun nan. ’

  36. 11 Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. 12 Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. 13 Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, “Kada ki yi kuka.”

    14 Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, “Saurayi, na ce maka, tashi!” 15 Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.