71 Bible Verses About Alcohol
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne;
duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
-
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
-
4 “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,
ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,
ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,
5 don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,
su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.
6 A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,
ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;
7 bari su sha su manta da talaucinsu
kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.
8 “Yi magana domin bebaye,
domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;
a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
-
29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki?
Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni?
Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?
30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi,
waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.
31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja,
sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya,
sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!
32 A ƙarshe yana sara kamar maciji
da kuma dafi kamar gamsheƙa.
33 Idanunka za su riƙa gane-gane,
zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.
34 Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna,
kwance a sama itacen jirgin ruwa.
35 Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba!
Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa!
Yaushe zan farka
don in ƙara shan wani?”
-
17 Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. 18 Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.
19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
-
29 ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? 30 In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
-
19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,
ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.
20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa
ko masu haɗama kansu da abinci,
21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,
gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
-
23 Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
-
14 Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu,
tsire-tsire domin mutum ya nome,
suna fid da abinci daga ƙasa,
15 ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna,
mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske,
abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.
-
20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe. 21 Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.
-
1 Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. 2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5 Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu.
-
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare, 3 dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan ’ya’yan inabi, ko yă ci ’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba. 4 Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga ’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
-
22 Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi
da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
23 waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,
amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
-
9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
-
8 Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.
-
1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.
3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.
-
8 Sa’an nan Ubangiji ya yi magana da Haruna ya ce, 9 “Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa. 10 Dole ku bambanta tsakanin mai tsarki da marar tsarki, tsakanin marar tsabta da mai tsabta, 11 za ku kuma koyar da Isra’ilawa dukan farillan da Ubangiji ya ba su ta wurin Musa.”
-
7 Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi
suke jiri don sun sha barasa
Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa
sun kuma yi tatur da ruwan inabi;
suna jiri saboda sun sha barasa,
suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,
suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.
8 Duk amai ya rufe teburori
kuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.
-
19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
-
11 Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe
don su nufi wurin shaye-shaye,
waɗanda suke raba dare
har sai sun bugu da ruwan inabi.
12 Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,
ganguna da busa da ruwan inabi,
amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,
ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
-
13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.
-
2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.
-
7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.
-
15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
-
33 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 34 Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ 35 Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta.”
-
20 Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi. 21 Sa’ad da ya sha ruwan inabin ya kuwa bugu, sai ya kwanta tsirara cikin tentinsa. 22 Ham, mahaifin Kan’ana ya ga tsiraici mahaifinsa, ya kuma faɗa wa ’yan’uwansa biyu a waje. 23 Amma Shem da Yafet suka ɗauki mayafi, suka shimfiɗa a kafaɗarsu, sa’an nan suka shiga suna tafiya da baya har zuwa inda mahaifinsu yake kwance, suka rufe tsiraicinsa. Suka kau da fuskokinsu domin kada su ga tsiraicin mahaifinsu.
-
17 Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”
-
6 Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.
7 Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.
8 Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”
Suka yi haka. 9 Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya 10 ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
11 Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.
-
8 Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.
9 Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11 Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. 12 Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13 Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.
-
17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci;
duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
-
13 “Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji,
“sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi
mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi.
Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu
yă kuma kwararo daga tuddai.
14 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila.
“Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu.
Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu;
za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu.
15 Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu,
ba kuwa za a ƙara tumɓuke su
daga ƙasar da na ba su ba,”
in ji Ubangiji Allahnku.
-
18 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19 Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”
-
34 “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.
-
26 Yi amfani da kuɗin ku saya duk abin da kuke so, ko shanu, ko tumaki, ko ruwan inabi, ko dai wani abin shan da ya yi tsami, ko kuwa duk abin da kuke so. Sai ku da gidanku, ku ci a can, a gaban Ubangiji Allahnku, ku kuma yi farin ciki.
-
11 ga karuwanci,
ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi,
waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace
suka kuwa sami amsa daga sanda.
Halin karuwanci yakan ɓad da su;
sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu
suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai,
a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri,
inda inuwa take da daɗi.
Saboda haka ’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci
surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
-
48 Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49 Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50 Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51 Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.
-
12 “Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.
-
4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
-
9 Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,
ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
10 ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,
randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
-
13 Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
-
1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.
-
11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.
-
7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8 A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse.
-
5 Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku. 6 Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.
-
6 A kan wannan dutse Ubangiji Maɗaukaki zai shirya bikin abinci mai kyau don dukan mutane,
liyafar ajiyayyen ruwan inabi da nama mafi kyau da ruwan inabi mafi kyau.
7 A wannan dutse zai kawar da
baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,
ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
8 zai haɗiye mutuwa har abada.
Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye
daga dukan fuskoki;
zai kawar da kunyar mutanensa
daga dukan duniya.
Ubangiji ne ya faɗa.
9 A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
-
1 “Ku zo, dukanku masu jin ƙishi,
ku zo wurin ruwaye;
ku kuma da ba ku da kuɗi,
ku zo, ku saya ku kuma ci!
Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara
ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
-
14 ‘Yehonadab ɗan Rekab ya umarci ’ya’yansa maza kada su sha ruwan inabi sun kuma kiyaye wannan umarni. Har yă zuwa yau ba sa shan ruwan inabi, domin sun yi biyayya da umarnin kakansu. Amma na yi muku magana sau da sau, duk da haka ba ku yi biyayya ba.
-
21 Kada firist ya sha ruwan inabi sa’ad da zai shiga fili na can ciki. 22 Kada su auri gwauruwa ko macen da aka sāke; za su auri budurwai ne kaɗai na Isra’ilawa ko gwaurayen firistoci. 23 Za su koyar da mutanena bambanci tsakanin tsarki da rashin tsarki su kuma nuna musu yadda za su bambanta marar tsarki da mai tsarki.
-
15 “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha,
yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu,
don dai yă ga tsiraicinsu.
16 Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka.
Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka!
Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai,
abin kunya kuma zai rufe darajarka.
17 Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka,
kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka.
Gama ka zub da jinin mutum;
ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
-
27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. 29 Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
-
8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.
-
9 Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, 10 shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. 11 Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”
-
28 Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa,
yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.
-
18 In mutum yana da gagararren ɗa mai tawaye, wanda ba ya biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ba ya kuma jin su sa’ad da suke horonsa, 19 mahaifinsa da mahaifiyarsa za su kama shi su kawo shi ga dattawa a ƙofar garinsu. 20 Za su ce wa dattawan, “Wannan ɗanmu gagararre ne, mai tawaye. Ba ya mana biyayya. Mai zari ne, kuma mashayi.” 21 Sa’an nan dukan mazan garinsa za su jajjefe shi har yă mutu. Dole ku fid da mugu daga cikinku. Dukan Isra’ila kuwa za su ji wannan su kuma ji tsoro.
-
8 A shekara ta ashirin da shida ta Asa sarkin Yahuda, Ela ɗan Ba’asha ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Tirza shekaru biyu.
9 Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. 10 Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.
-
9 Babu sauran shan ruwan inabi suna rera waƙa;
barasa ya zama da ɗaci ga masu shanta.
-
1 Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su. 2 Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. 3 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. 4 Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.
-
3 Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.
-
19 Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 20 Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. 21 Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. 22 Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
-
20 Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.
-
13 “Amma kuringar ta ce, ‘In bar ruwan inabina, wanda yake faranta zuciyar alloli da mutane, in zo in yi fama da itatuwa?’
-
1 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda haka ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba’in.
2 Akwai wani mutumin Zora, mai suna Manowa, daga kabilar Dan, matarsa kuwa bakararriya ce, ba ta haihuwa. 3 Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa. 4 To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, 5 gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”
6 Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, “Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. 7 Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ ”
-
14 Sai ya ce mata, “Har yaushe za ki ci gaba da maye? Ki daina shan ruwan inabi.”
15 Hannatu ta ce, “Ba haka ba ne, ranka yă daɗe, ni mace ce da take cikin matsala ƙwarai da gaske. Ban sha ruwan inabi ba, ko wani abu mai sa maye, ina dai faɗa wa Ubangiji abin da yake damuna ne.
-
13 Dawuda ya gayyace shi, ya kuwa ci ya sha tare da shi, Dawuda ya sa ya bugu tilis. Amma da yamma Uriya ya koma ya kwanta a tabarmarsa cikin bayin maigidan sarki; bai je gida ba.
-
18 Ubangiji ya ce,
“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,
Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,
za su zama fari kamar ƙanƙara;
ko da sun yi ja kamar mulufi,
za su zama kamar ulu.
-
10 An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya;
babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi;
babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi,
gama na kawo ƙarshen yin sowa.
-
12 Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki
ya kira ku a wannan rana
don ku yi kuka ku yi ihu,
don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.
13 Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna,
kuna yankan shanu kuna kashe tumaki,
kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi!
Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha,
gama gobe za mu mutu!”
-
1 Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,
ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,
da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,
ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!
-
8 Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama
ta hannunsa kuma mai iko cewa,
“Ba zan ƙara ba da hatsinki
ya zama abinci ga abokan gābanki ba,
baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin
wanda kika sha wahala samu ba;
9 amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi
su kuma yabi Ubangiji,
waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi
a filayen wurina mai tsarki.”
-
10 Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.
-
1 Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2 Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. 3 Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. 4 Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. 5 Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.
Shows Read in context, Share and Copy.