42 Bible Verses About Friendship
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. 17 Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
-
5 Gara tsawatawar da ake yi a fili
da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
6 Za a iya amince da rauni daga aboki,
amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
7 Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma
amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.
8 Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa
haka yake da mutumin da ya bar gidansa.
9 Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,
gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,
kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,
gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
-
17 Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,
ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
18 Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani
ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
-
24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
-
9 Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
10 In ɗaya ya fāɗi,
abokinsa zai taimake shi yă tashi.
Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi
ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.
Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?
12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,
mutum biyu za su iya kāre kansu.
Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
-
17 Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe
haka mutum kan koyi daga mutum.
-
12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.
15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. 16 Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.
-
1 Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa. 2 Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba. 3 Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa. 4 Yonatan ya tuɓe doguwar taguwarsa da ya sa, ya ba wa Dawuda, tare da sulkensa, har ma da māshi da kibiyarsa, da kuma bel nasa.
5 Duk abin da Shawulu ya aiki Dawuda yă yi yakan yi shi cikin aminci, har Shawulu ya ba shi babban makami a rundunarsa. Wannan ya faranta wa dukan mutane zuciya har ma da ma’aikatan Shawulu.
-
20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
-
24 Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai,
kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
25 in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa
ka kuma sa kanka a tarko.
26 Kada ka zama mai ɗaukar lamuni
ko ka ba da jingina saboda bashi;
27 gama in ka kāsa biya
za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
-
23 Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.
-
4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
-
9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne,
amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
-
33 Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.”
-
16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17 Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.” 18 Sa’ad da Na’omi ta gane cewa Rut ta ƙudura tă tafi tare da ita, sai ta daina nema tă koma.
-
20 Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne
yayinda nake kuka ga Allah;
21 a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah
kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.
-
9 Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari. 10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa. 11 Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.
-
14 “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki
ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
15 Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,
kamar rafin da yakan bushe da rani,
-
28 Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali,
mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
-
8 “Amma kai, ya Isra’ila, bawana,
Yaƙub, wanda na zaɓa,
zuriyar Ibrahim abokina,
-
2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
-
9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. 10 Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi. 11 Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
-
11 Ubangiji yakan yi magana da Musa fuska da fuska, kamar yadda mutum yake magana da abokinsa. Sa’an nan Musa yă koma sansani, amma saurayin nan Yoshuwa ɗan Nun mai taimakonsa ba ya barin tentin.
-
7 Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka?
-
26 Adali yakan yi hankali a abokantaka,
amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
27 Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta,
amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
-
27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri. 28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka. 31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
-
8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa. 9 Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba. 10 Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.
-
12 Da a ce abokin gāba ne ke zagina,
da na jure da shi;
da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina,
da na ɓoye daga gare shi.
13 Amma kai ne, mutum kamar ni,
abokina, abokina na kurkusa,
14 wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai
yayinda muke tafiya tare
a taron jama’a a gidan Allah.
-
Waƙar haurawa. Ta Dawuda.
1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma
sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
-
15 “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.
-
5 Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, 6 domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ 7 Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ 8 Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.
-
24 Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25 Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
-
11 Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. 12 Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, 13 sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
-
4 Wadata kan kawo abokai da yawa,
amma abokin matalauci kan bar shi.
5 Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba,
kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
6 Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki,
kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.
7 ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi,
balle abokansa, su ma za su guje shi.
Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo,
ba zai sam su ba.
-
11 Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12 Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’
13 “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14 Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15 Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’
16 “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”
-
50 Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.”
Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.
-
26 Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana;
ƙaunatacce kake a gare ni.
Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce,
abar al’ajabi fiye da ta mace.
-
9 Har abokina na kurkusa,
wanda na amince da shi,
wanda muke cin abinci tare,
ya juya yana gāba da ni.
-
1 Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,
in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
2 in maganarka ta taɓa kama ka,
ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
3 to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;
da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka,
ka tafi ka ƙasƙantar da kanka;
ka roƙi maƙwabcinka!
4 Ka hana kanka barci,
ko gyangyaɗi a idanunka ma.
5 Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,
kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
-
19 Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”
-
11 “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren. 12 Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.
13 “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
14 “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
-
1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3 Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. 4 Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
Shows Read in context, Share and Copy.