35 Bible Verses About Loneliness
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.
Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
23 Sai mutumin ya ce,
“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana
nama kuma na namana.
Za a ce da ita ‘mace,’
gama an ciro ta daga namiji.”
24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
-
5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,
shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
6 Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai,
ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi;
amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
-
5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
“Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba.”
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?”
-
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
15 Idanuna kullum suna a kan Ubangiji,
gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
16 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,
gama na kaɗaice ina kuma wahala.
17 Damuwoyin zuciyata sun ninka;
ka ’yantar da ni daga wahalata.
18 Ka dubi wahalata da kuma azabata
ka ɗauke mini dukan zunubaina.
19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru
da kuma yadda suka ƙara ƙina!
20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
21 Bari mutunci da adalci su tsare ni,
domin begena yana a kanka.
-
15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. 18 Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.
-
9 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni,
kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi;
kai ne ka kasance mai taimakona.
Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni,
Ya Allah Mai cetona.
10 Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni,
Ubangiji zai karɓe ni.
-
18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”
-
33 Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34 A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).
-
16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
-
7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.
8 Akwai wani mutum shi kaɗai;
bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.
Ba shi da hutu daga wahalarsa,
duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.
Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala,
kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?”
Wannan ma ba shi da amfani,
harkar baƙin cikin ne kawai!
9 Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
10 In ɗaya ya fāɗi,
abokinsa zai taimake shi yă tashi.
Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi
ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.
Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?
12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,
mutum biyu za su iya kāre kansu.
Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.
-
28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”
-
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
5 Ka shirya mini tebur
a gaban abokan gābana.
Ka shafe kaina da mai;
kwaf nawa ya cika har yana zuba.
6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi
dukan kwanakin raina,
zan kuwa zauna a gidan Ubangiji
har abada.
-
31 Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! 32 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.
33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
-
6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
-
3 Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
aka rena shi aka yi banza da shi.
4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
6 Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
kowannenmu ya kama hanyarsa;
Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
hukuncin da ya wajaba a kanmu.
-
35 Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a.
-
9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
-
24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
-
15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
-
8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
-
4 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni;
rigyawan hallaka sun sha kaina.
5 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni;
tarkon mutuwa ya yi mini arangama.
6 Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
Na yi kuka ga Allahna don taimako.
A Haikalinsa ya ji muryata,
Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
-
23 Duk da haka kullum ina tare da kai;
ka riƙe ni a hannun damana.
24 Ka bishe ni da shawararka,
bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.
25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba?
Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.
26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,
amma Allah ne ƙarfin zuciyata
da kuma rabona har abada.
-
1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.
-
14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.
1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?
Me ya sa ka yi nisa da cetona,
ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,
da dare kuma ban yi shiru ba.
-
7 Ina zan tafi daga Ruhunka?
Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8 In na haura zuwa sammai, kana a can;
in na yi gado a zurfafa, kana a can.
9 In na tashi a fikafikan safiya,
in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10 can ma hannunka zai bishe ni,
hannunka na dama zai riƙe ni gam.
-
4 Duba ta damata ka gani;
babu wanda ya kula da ni.
Ba ni da mafaka;
babu wanda ya kula da raina.
-
16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;
suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,
gama ana kirana da sunanka,
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.
17 Ban taɓa zauna a cikin ’yan tawaye ba,
ban taɓa yi murna da su ba;
na zauna ni kaɗai domin hannunka yana a kaina
ka kuma sa na cika da haushi.
-
3 Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi. 4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah. 5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako. 6 Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.
-
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;
yakan cece su daga dukan wahalarsu.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai
ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
-
11 Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna;
maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
-
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
-
20 Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”
Shows Read in context, Share and Copy.