30 Bible Verses About Depression

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Depression
  1. 15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

    16 fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta,

    don yă sa a manta da su a duniya.

    17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;

    yakan cece su daga dukan wahalarsu.

    18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

    19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,

    amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

    1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;

    ya juya wurina ya kuma ji kukata.

    2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,

    daga laka da taɓo;

    ya sa ƙafafuna a kan dutse

    ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.

    3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,

    waƙar yabo ga Allahna.

    Da yawa za su gani su tsorata

    su kuma dogara ga Ubangiji.

  3. 8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

  4. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

    8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

  5. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  6. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  7. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  8. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  9. 3 Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.

  10. 1 Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. 2 Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.”

    3 Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can. 4 Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” 5 Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci.

    Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.”

  11. 25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,

    amma maganar alheri kan faranta masa rai.

  12. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  13. 8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”

  14. 3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

    ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

  15. 11 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da kuma Allahna.

  16. 30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  17. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  18. 10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  19. 5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  20. 11 Ka mai da kukata ta zama rawa;

    ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

  21. 3 Hawayena ne sun zama abincina

    dare da rana,

    yayinda mutane suke ce da ni dukan yini,

    “Ina Allahnka ɗin?”

    4 Waɗannan abubuwa ne nakan tuna

    sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina,

    yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a,

    ina bishe su a jere zuwa gidan Allah,

    da sowa ta farin ciki da kuma godiya

    a cikin taron biki.

    5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da kuma Allahna.

    6 Raina yana baƙin ciki a cikina;

    saboda haka zan tuna da kai

    daga ƙasar Urdun,

    a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  22. 23 Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,

    gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.

  23. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

  24. 7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. 8 Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. 9 Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. 10 Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.

  25. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  26. 9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,

    mafaka a lokutan wahala.

    10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,

    gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  27. 4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

  28. 7 Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji;

    ƙarfina ya ƙare.

    Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni

    in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.

    8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

    gama na sa zuciyata a gare ka.

    Ka nuna mini hanyar da zan bi,

    gama a gare ka na miƙa raina.

    9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji,

    gama na ɓoye kaina a gare ka.

  29. 3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.

  30. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.