39 Bible Verses About Waiting
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
Ta Dawuda.
1 Kada ka tsorata saboda mugayen mutane
ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
2 gama kamar ciyawa za su bushe,
kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji
zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;
ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,
gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
7 Ka natsu a gaban Ubangiji
ka kuma jira da haƙuri gare shi;
kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,
sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;
kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
9 Gama za a datse mugayen mutane,
amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
-
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? 25 Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
-
13 Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa
zan ga alherin Ubangiji;
a ƙasar masu rai.
14 Ka dogara ga Ubangiji,
ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya
ka kuma dogara ga Ubangiji.
-
5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
6 Raina na jiran Ubangiji
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,
fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila
daga dukan zunubansu.
-
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
26 yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.
1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;
ya juya wurina ya kuma ji kukata.
-
5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
dogarata kan zo daga gare shi ne.
6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,
shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.
8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;
ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,
gama Allah ne mafakarmu. Sela
-
35 “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36 kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37 Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. 38 Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39 Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40 Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”
-
27 Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce
kana kuma gunaguni cewa,
“Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji;
Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
-
18 “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
-
6 Masu adalci za su ga su ji tsoro;
za su yi masa dariya, suna cewa,
7 “Yanzu, ga mutumin
da bai mai da Allah mafakarsa ba
amma ya dogara a yawan arzikinsa
ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
8 Amma ni kamar itace zaitun ne
ina haɓaka a gidan Allah;
na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah
har abada abadin.
9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;
a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.
Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.
-
22 Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!”
Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
-
5 ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,
gama kai ne Allah Mai cetona,
kuma begena yana a kanka dukan yini.
-
4 A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5 Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
-
1 Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.
2 Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan. 3 Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka. 4 Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri. 5 Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. 6 Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.
-
20 Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
-
7 A wannan dutse zai kawar da
baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,
ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;
8 zai haɗiye mutuwa har abada.
Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye
daga dukan fuskoki;
zai kawar da kunyar mutanensa
daga dukan duniya.
Ubangiji ne ya faɗa.
9 A wannan rana za su ce,
“Tabbatacce wannan shi ne Allah;
mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.
Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;
bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”
-
18 Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;
ya tashi don yă nuna muku jinƙai.
Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.
Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!
-
6 Amma dole ku koma ga Allahnku;
ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,
ku kuma saurari Allahnku kullum.
-
18 Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19 ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi 20 waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,
-
2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;
muna marmarinka.
Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,
cetonmu a lokacin damuwa.
-
16 Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.
17 Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.” 18 Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan.
Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.”
19 Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?”
20 Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus. 21 Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”
-
3 Ba wanda yake sa bege a gare ka
da zai taɓa shan kunya,
amma za su sha kunya
su da suke tayarwa babu dalili.
-
7 “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?
Begena yana a gare ka.
8 Ka cece ni daga dukan laifofina;
kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.
-
14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
15 Idanun kowa yana dogara gare ka,
kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
16 Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
-
7 Hanyar masu adalci sumul take;
Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.
8 I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka,
muna sa zuciya gare ka;
sunanka da tunani a kanka
su ne marmarin zukatanmu.
9 Raina yana marmarinka da dare;
da safe kuma raina yana son ganinka.
Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,
mutanen duniya kan koyi adalci.
-
4 Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji,
babu kunnen da ya gane,
babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai,
wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.
-
33 Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna. 34 In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci.
Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.
-
34 Ku sa zuciya ga Ubangiji
ku kuma kiyaye hanyarsa.
Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar,
sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
-
13 Amma nan da nan suka manta abin da ya yi
ba su kuwa jira shawararsa ba.
14 A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su
a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
15 Sai ya ba su abin da suka roƙa,
amma ya aika musu da muguwar cuta.
-
23 Sarakuna za su zama kamar iyayen reno,
sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye.
Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa;
za su lashe ƙura a ƙafafunki.
Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji;
waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
-
3 Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci;
tana zancen ƙarshe
kuma ba za tă zama ƙarya ba.
Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta;
lalle za tă zo, ba za tă makara ba.
-
8 Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji;
“a ranar da zan tsaya in ba da shaida,
Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai,
in tattara mulkoki
in kuma zuba fushina a kansu,
da dukan zafin haushina.
Za a mamaye dukan duniya
da zafin fushina.
-
16 Yayinda Bulus yake jiransu a Atens, ya damu ƙwarai da ya ga birnin cike da gumaka. 17 Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.
-
7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
-
3 Na gaji da kira ina neman taimako;
maƙogwarona ya bushe
idanuna sun dushe,
suna neman Allahna.
-
7 Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,
ina sauraron Allah Mai Cetona;
Allahna kuwa zai ji ni.
-
20 Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, 21 shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.
-
27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, 28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
Shows Read in context, Share and Copy.