54 Bible Verses About Waiting on the Lord

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Waiting on the Lord
  1. 2 A gare ka na dogara, ya Allahna.

    Kada ka bari in sha kunya,

    ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.

    3 Ba wanda yake sa bege a gare ka

    da zai taɓa shan kunya,

    amma za su sha kunya

    su da suke tayarwa babu dalili.

    4 Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,

    ka koya mini hanyoyinka;

    5 ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

    gama kai ne Allah Mai cetona,

    kuma begena yana a kanka dukan yini.

    6 Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

    gama suna nan tun dā.

    7 Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

    da kuma hanyoyin tawayena;

    bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

    gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

    8 Ubangiji nagari da mai adalci ne;

    saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.

    9 Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai

    ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

  2. Ta Dawuda.

    1 Kada ka tsorata saboda mugayen mutane

    ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

    2 gama kamar ciyawa za su bushe,

    kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

    3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

    5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

    ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

    6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,

    gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

    7 Ka natsu a gaban Ubangiji

    ka kuma jira da haƙuri gare shi;

    kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

    sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

    8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;

    kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.

    9 Gama za a datse mugayen mutane,

    amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.

    10 A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe;

    ko ka neme su, ba za a same su ba.

    11 Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar

    su kuma zauna da cikakkiyar salama.

  3. 27 Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce

    kana kuma gunaguni cewa,

    “Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji;

    Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?

    28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

    29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

    yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

    30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  4. 11 Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji;

    ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya

    saboda masu danne ni.

    12 Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina,

    gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina,

    suna numfasa tashin hankali.

    13 Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa

    zan ga alherin Ubangiji;

    a ƙasar masu rai.

    14 Ka dogara ga Ubangiji,

    ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya

    ka kuma dogara ga Ubangiji.

  5. 21 Duk da haka na tuna da wannan

    na kuma sa bege ga nan gaba.

    22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

    25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,

    ga kuma wanda yake neman shi;

    26 yana da kyau ka jira shiru

    domin samun ceton Ubangiji.

  6. 5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,

    kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

    6 Raina na jiran Ubangiji

    fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,

    fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

    7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,

    gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa

    kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

    8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila

    daga dukan zunubansu.

  7. 18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.

    22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? 25 Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.

  8. 5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;

    dogarata kan zo daga gare shi ne.

    6 Shi ne kaɗai dutsena da cetona;

    shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

    7 Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne,

    shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.

    8 Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane;

    ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi,

    gama Allah ne mafakarmu. Sela

  9. 7 Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,

    ina sauraron Allah Mai Cetona;

    Allahna kuwa zai ji ni.

  10. 17 Zan saurari Ubangiji,

    wanda ya ɓoye fuskarsa daga gidan Yaƙub.

    Zan dogara gare shi.

  11. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce.

    1 Na jira da haƙuri ga Ubangiji;

    ya juya wurina ya kuma ji kukata.

    2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi,

    daga laka da taɓo;

    ya sa ƙafafuna a kan dutse

    ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.

    3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina,

    waƙar yabo ga Allahna.

    Da yawa za su gani su tsorata

    su kuma dogara ga Ubangiji.

    4 Mai albarka ne mutumin

    da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,

    wanda ba ya kula da masu girman kai,

    waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

  12. 6 Amma dole ku koma ga Allahnku;

    ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,

    ku kuma saurari Allahnku kullum.

  13. 7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa. 9 ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!

    10 ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.

  14. 18 Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

    ya tashi don yă nuna muku jinƙai.

    Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.

    Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

  15. 18 “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

  16. 9 Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. 10 Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” 11 Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.

  17. 20 Muna jiran Ubangiji da bege;

    shi ne taimakonmu da garkuwarmu.

    21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,

    gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.

    22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,

    ko ma da muke sa begenmu a gare ka.

  18. 7 “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?

    Begena yana a gare ka.

    8 Ka cece ni daga dukan laifofina;

    kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.

  19. 6 Masu adalci za su ga su ji tsoro;

    za su yi masa dariya, suna cewa,

    7 “Yanzu, ga mutumin

    da bai mai da Allah mafakarsa ba

    amma ya dogara a yawan arzikinsa

    ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

    8 Amma ni kamar itace zaitun ne

    ina haɓaka a gidan Allah;

    na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah

    har abada abadin.

    9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;

    a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.

    Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

  20. Waƙar haurawa.

    1 Na tā da idanuna gare ka,

    gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

    2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,

    kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,

    haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,

    sai ya nuna mana jinƙansa.

  21. 14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi

    yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.

    15 Idanun kowa yana dogara gare ka,

    kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.

    16 Ka buɗe hannunka

    ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.

  22. 35 “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci, 36 kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan. 37 Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci. 38 Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne. 39 Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba. 40 Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”

  23. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda.

    1 Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai;

    cetona na zuwa daga gare shi.

    2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;

    shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.

  24. 22 Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!”

    Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.

  25. 5 Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.

  26. 4 A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. 5 Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

  27. 5 Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

  28. 11 Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13 yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14 wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.

  29. 9 Ya ƙarfina, na dogara gare ka;

    kai, ya Allah, kai ne kagarata, 10 Allah mai ƙaunata.

    Allah zai sha gabana

    zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.

  30. 4 Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji,

    babu kunnen da ya gane,

    babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai,

    wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.

  31. 34 Ku sa zuciya ga Ubangiji

    ku kuma kiyaye hanyarsa.

    Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar,

    sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.

  32. 7 A wannan dutse zai kawar da

    baƙin cikin da ya lulluɓe dukan mutane,

    ƙyallen da ya rufe dukan al’ummai;

    8 zai haɗiye mutuwa har abada.

    Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye

    daga dukan fuskoki;

    zai kawar da kunyar mutanensa

    daga dukan duniya.

    Ubangiji ne ya faɗa.

    9 A wannan rana za su ce,

    “Tabbatacce wannan shi ne Allah;

    mun dogara a gare shi, ya kuma cece mu.

    Wannan shi ne Ubangiji, mun dogara a gare shi;

    bari mu yi murna mu kuma yi farin ciki a cikin cetonsa.”

  33. 1 Zan tsaya wurin tsarona

    in kuma zauna a kan katanga;

    zan jira in ga abin da zai ce mini,

    da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka.

    2 Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce,

    “Ka rubuta wannan ru’uya

    ka bayyana ta a fili a kan alluna

    don mai shela yă ruga da ita, yă kai.

    3 Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci;

    tana zancen ƙarshe

    kuma ba za tă zama ƙarya ba.

    Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta;

    lalle za tă zo, ba za tă makara ba.

  34. 3 Na gaji da kira ina neman taimako;

    maƙogwarona ya bushe

    idanuna sun dushe,

    suna neman Allahna.

  35. 21 Bari mutunci da adalci su tsare ni,

    domin begena yana a kanka.

  36. 23 Sarakuna za su zama kamar iyayen reno,

    sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye.

    Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa;

    za su lashe ƙura a ƙafafunki.

    Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji;

    waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”

  37. 27 Waɗannan duka suna dogara gare ka

    don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.

    28 Sa’ad da ba su da shi,

    sai su tattara shi;

    sa’ad da ka buɗe hannunka,

    sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.

  38. 2 Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai;

    muna marmarinka.

    Ka zama ƙarfinmu kowace safiya,

    cetonmu a lokacin damuwa.

  39. 5 Adalcina na zuwa da sauri,

    cetona yana a kan hanya,

    hannuna kuma zai kawo adalci ga al’ummai.

    Tsibirai za su dube ni

    su kuma jira da sa zuciya don hannuna.

  40. 8 Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji;

    “a ranar da zan tsaya in ba da shaida,

    Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai,

    in tattara mulkoki

    in kuma zuba fushina a kansu,

    da dukan zafin haushina.

    Za a mamaye dukan duniya

    da zafin fushina.

  41. 28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

  42. 8 Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

  43. 3 Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

    da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

    in kuma jira da sa zuciya.

  44. 13 Amma nan da nan suka manta abin da ya yi

    ba su kuwa jira shawararsa ba.

    14 A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su

    a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.

    15 Sai ya ba su abin da suka roƙa,

    amma ya aika musu da muguwar cuta.

  45. 7 Hanyar masu adalci sumul take;

    Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.

    8 I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka,

    muna sa zuciya gare ka;

    sunanka da tunani a kanka

    su ne marmarin zukatanmu.

    9 Raina yana marmarinka da dare;

    da safe kuma raina yana son ganinka.

    Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,

    mutanen duniya kan koyi adalci.

  46. 4 ba zai kāsa ko ya karai ba

    sai ya kafa adalci a duniya.

    Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”

  47. 20 Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, 21 shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

  48. 12 Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335.

  49. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

  50. 12 Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.

  51. 24 Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,

    dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.

  52. 13 Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji,

    a lokacin da ka ga dama;

    a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah,

    ka amsa mini da tabbacin ceto.

  53. 10 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

  54. 7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

    9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!