78 Bible Verses About Being Happy

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Being Happy
  1. 4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

    8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

    10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  2. 7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;

    ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

    8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

    9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;

    jikina kuma zai zauna lafiya,

    10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,

    ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

    11 Ka sanar da ni hanyar rai;

    za ka cika ni da farin ciki a gabanka,

    da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  3. 13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

  4. 20 Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,

    kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.

  5. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.

  6. 1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.

  7. 3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

  8. 16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

    18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

    20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

  9. 10 In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11 Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

  10. 13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima,

    mutumin da ya sami fahimi,

    14 gama ta fi azurfa riba

    tana kuma da amfani fiye da zinariya.

    15 Ta fi lu’ulu’u daraja;

    ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.

    16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama;

    a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.

    17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi,

    dukan hanyoyinta kuma salama ne.

    18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta;

    waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.

  11. 20 Gaskiya nake gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, yayinda duniya take murna. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki. 21 Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya. 22 Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.

  12. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

  13. 22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

  14. 17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;

    zai ba ka farin cikin da kake so.

  15. Waƙar haurawa.

    1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,

    waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

    2 Za ka ci amfanin aikinka;

    albarku da wadata za su zama naka.

  16. 10 Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”

  17. 22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,

    kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

    23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;

    ka nemi hikima, horo da fahimi.

    24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

    duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

    25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna;

    bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!

  18. 12 Na san ba abin da ya fi wa mutane kyau fiye da su ji daɗi su kuma yi alheri yayinda suke da rai. 13 Cewa kowa yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗi cikin dukan aikinsa, wannan kyautar Allah ce.

  19. 7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8 Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum, 9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

  20. 1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

    6 Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. 7 Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. 8 Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

    9 Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! 10 Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! 11 Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.

  21. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.

  22. 15 Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka;

    masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.

  23. 13 Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo,

    kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.

  24. 13 Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske,

    amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.

  25. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa,

  26. 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”

  27. 22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,

    amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.

  28. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  29. 5 In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa yă je yaƙi, ko yă yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, yă faranta wa matar da ya aura rai.

  30. 17 “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure;

    saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

  31. 17 Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,

  32. 11 Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.

  33. LITTAFI NA ƊAYA

    1 Mai farin ciki ne mutumin

    da ba ya aiki da shawarar mugaye

    ko yă yi abin da masu zunubi suke yi

    ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

    2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,

    kuma yana ta nazarinta dare da rana.

    3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,

    wanda yake ba da amfani a daidai lokaci

    wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.

    Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

    4 Ba haka yake da mugaye ba!

    Su kamar yayi ne

    da iska take kwashewa.

  34. 15 Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi,

    amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.

  35. 2 Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;

    zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.

    Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;

    ya zama mai cetona.”

    3 Da farin ciki zan ɗebo ruwa

    daga rijiyoyin ceto.

    4 A wannan rana za ku ce,

    “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;

    a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,

    a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

    5 Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;

    bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

    6 Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,

    gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

  36. 13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.

  37. 6 Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.”

  38. 5 Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce;

    ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.

    6 Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka

    ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.

    7 Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji

    ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka

    ba zai jijjigu ba.

  39. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  40. 15 Ka gane, ya Ubangiji;

    ka tuna da ni ka kuma lura da ni.

    Ka yi mini ramuwa a kan masu tsananta mini.

    Cikin jimirinka, kada ka ɗauke ni;

    ka tuna yadda na sha zagi saboda kai.

    16 Sa’ad da maganganunka suka zo, na cinye su;

    suka zama abin farin ciki zuciyata kuma ta yi murna,

    gama ana kirana da sunanka,

    Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki.

  41. 9 Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku? 10 Dare da rana muna addu’a da himma domin mu sāke ganinku, mu kuma ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

  42. 2 Bakunanmu sun cika da dariya,

    harsunanmu da waƙoƙin farin ciki.

    Sai ana faɗi a cikin al’ummai,

    “Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominsu.”

    3 Ubangiji ya aikata manyan abubuwa dominmu,

    mun kuwa cika da farin ciki.

  43. 1 Na ce wa kaina, “Zo, zan gwada ka da jin daɗi don in ga abin da yake da kyau.” Amma wannan ma ya zama ba amfani. 2 Sai na ce, “Dariya hauka ce. Kuma me jin daɗi yake kawowa?”

  44. 26 Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.

  45. 9 Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,

    bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.

    Ka bi shawarar zuciyarka

    da kuma duk abin da idanunka suka gani,

    amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan

    Allah zai shari’anta ka.

  46. 21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

  47. 14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta. 15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka. 16 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.

  48. 6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

  49. 9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta

    ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki.

    Yabi Ubangiji.

  50. 20 Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya

    amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.

  51. 10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;

    raina yana farin ciki a cikin Allahna.

    Gama ya suturce ni da rigunan ceto

    ya yi mini ado da rigar adalci,

    yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist

    kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.

  52. 5 Sai Yunana ya fita daga birnin ya yi wajen gabas, ya zauna. A nan ya yi wa kansa rumfa, ya zauna cikin inuwarta yana jira yă ga abin da zai sami birnin. 6 Sai Ubangiji Allah ya sa wata ’yar kuringa ta tsiro, ta yi girma a inda Yunana yake, don ta inuwantar da shi, yă ji daɗi. Yunana kuwa ya yi murna matuƙa da wannan kuringa. 7 Amma kashegari da safe sai Allah ya sa tsutsa ta cinye ’yar kuringar har ta mutu. 8 Sa’ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro, zafin ranar kuma ya buga kan Yunana, har ya ji sai ka ce zai suma. Ya so a ce ya mutu ma, sai ya ce, “Gara in mutu da a ce ina zaune da rai.”

    9 Amma Allah ya ce wa Yunana, “Daidai ne ka yi fushi saboda wannan kuringa?”

    Sai Yunana ya ce, “I, daidai ne, ina fushi matuƙa, har ina so da na mutu ma.”

    10 Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita. 11 Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”

  53. 11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  54. 10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.

  55. 20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce,

    “Masu albarka ne ku da kuke matalauta,

    gama mulkin Allah naku ne.

    21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,

    gama za ku ƙoshi.

    Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,

    gama za ku yi dariya.

    22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,

    suka ware ku, suka zage ku,

    suna ce da ku mugaye,

    saboda Ɗan Mutum.

    23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.

  56. 21 Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila. 22 Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana.

    Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist. 23 Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya. 24 Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.

    25 Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.

  57. 6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,

    gama ya ji kukata na neman jinƙai.

    7 Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata;

    zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako.

    Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki

    zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

    8 Ubangiji shi ne ƙarfin mutanensa,

    kagarar ceto domin shafaffensa.

  58. 4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,

    ga Allah, farin cikina da murnata.

    Zan yabe ka da garaya,

    Ya Allah, Allahna.

  59. 5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye

    za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

    6 Shi da ya fita yana kuka,

    riƙe da iri don shuki,

    zai dawo da waƙoƙin farin ciki,

    ɗauke da dammuna.

  60. 30 Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya,

    kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa.

  61. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  62. 25 Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna. 26 Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya. 27 Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki. 28 Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa. 29 Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa, 30 domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

  63. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  64. 5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne

    amma alherinsa har matuƙa ne;

    mai yiwuwa a yi kuka da dare

    amma farin ciki kan zo da safe.

  65. 8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;

    dokar tana cikin zuciyata.”

  66. 11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;

    bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;

    12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.

    Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;

    13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,

    yana zuwa don yă hukunta duniya.

    Zai hukunta duniya cikin adalci

    mutane kuma cikin amincinsa.

  67. 28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki,

    amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.

  68. 15 Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya.

  69. 15 Farin ciki ya rabu da zuciyarmu;

    rayuwarmu ta zama makoki.

  70. 44 “Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.

    45 “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. 46 Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

  71. 25 “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.

  72. 52 Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

  73. 3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa. 7 In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar; 8 in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.

  74. 13 Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa.

    Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.

  75. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  76. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”

  77. 12 Za ku fita da farin ciki

    a kuma bi da ku da salama;

    duwatsu da tuddai

    za su ɓarke da waƙa a gabanku,

    dukan itatuwan jeji kuma

    za su tafa hannuwansu.

  78. 9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.