50 Bible Verses About Marriage and Love

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Marriage and Love
  1. 18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

    19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

    Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

    25 Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.

  2. 1 In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai. 2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. 3 In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

    4 Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. 5 Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. 6 Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. 7 Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

    8 Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

  3. 22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

    25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31 “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” 32 Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. 33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.

  4. 15 Ku sha ruwa daga tankinku,

    ruwa mai gudu daga rijiyarku.

    16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,

    rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

    17 Bari su zama naka kaɗai,

    don kada ka raba da baƙi.

    18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

    bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

    19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

    bari mamanta su ishe ka kullum,

    bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

  5. Ƙaunatacciya

    16 Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce;

    yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana.

  6. 2 Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla.

  7. 4 Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’ 5 ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’? 6 Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”

    7 Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”

    8 Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. 9 Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

    10 Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”

    11 Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. 12 Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”

  8. 1 To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure. 2 Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3 Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4 Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5 Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku. 6 Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba. 7 Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.

    8 To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. 9 Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.

    10 Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. 11 In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.

    12 Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta. 13 In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren. 14 Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.

    15 Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. 16 Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?

  9. Maganar ƙarshe. Mace Mai Halin Kirki

    10  Wa yake iya samun mace mai halin kirki?

    Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.

    11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita

    kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.

    12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,

    dukan kwanakin ranta.

  10. 26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

    27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

    28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”

  11. 8 Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

  12. 9 Biyu sun fi ɗaya,

    gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

    10 In ɗaya ya fāɗi,

    abokinsa zai taimake shi yă tashi.

    Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

    ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

    11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

    Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

    12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

    mutum biyu za su iya kāre kansu.

    Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

  13. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

    19 Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

    20 ’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.

    21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.

  14. 7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

  15. 5 Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6 Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ 7 ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8 su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9 Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”

    10 Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. 11 Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12 In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

  16. 4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

  17. 12 Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. 13 Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. 14 Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

    15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

  18. 6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka,

    kamar hatimi a hannunka;

    gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa,

    kishinta yana kamar muguntar kabari,

    yana ƙuna kamar wuta mai ci,

    kamar gagarumar wuta.

    7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba,

    koguna ba za su iya kwashe ta ba.

    In wani zai bayar da

    dukan dukiyar gidansa don ƙauna,

    za a yi masa dariya ne kawai.

  19. 13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

  20. 14 Ku yi kome da ƙauna.

  21. 1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5 Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6 kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

  22. 7 Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8 Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.

  23. 3 Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai;

    ka ɗaura su kewaye da wuyanka,

    ka rubuta su a allon zuciyarka.

    4 Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau

    a gaban Allah da kuma a gaban mutane.

    5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  24. 27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

    31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

  25. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  26. 22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

    ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

  27. 6 Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa,

    “Halleluya!

    Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.

    7 Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna

    mu kuma ɗaukaka shi!

    Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi,

    amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

    8 Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta

    ta sanya.”

    (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)

    9 Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

  28. 5 Gama Mahaliccinki shi ne mijinki,

    Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila ne Mai Fansarki;

    ana ce da shi Allahn dukan duniya.

  29. 14 Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

  30. 12 Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

  31. 8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

  32. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  33. 24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. 25 Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

    26 Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. 27 Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

  34. 10 Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.

  35. 3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  36. 14 Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne,

    amma mace mai basira daga Ubangiji ne.

  37. 14 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari.

    15 Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah. Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.

  38. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,

  39. 1 Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.

    2 Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku. 3 To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.

  40. 3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

  41. 12 Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

  42. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

    19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  43. 16 Rut Amma Rut ta amsa, “Kada ki roƙe ni in bar ki ko in koma daga gare ki. Inda za ki, zan tafi, kuma inda za ki zauna, zan zauna. Mutanenki, za su zama mutanena kuma Allahnki, zai zama Allahna. 17 Inda za ki mutu zan mutu, zan mutu a can kuma za a binne ni. Bari Ubangiji ya hukunta ni da tsanani sosai, in wani abu in ba mutuwa ce ta raba ke da ni ba.”

  44. 8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

    gama na sa zuciyata a gare ka.

    Ka nuna mini hanyar da zan bi,

    gama a gare ka na miƙa raina.

  45. 12 Ƙiyayya kan haddasa wahala,

    amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.

  46. 9 Kin saci zuciyata, ’yar’uwata, amaryata;

    kin saci zuciyata

    da hararar idanunki,

    da dutse mai daraja guda na abin wuyanki.

  47. 18 “Duk wanda ya saki matarsa ya auri wata mace, zina ne yake yi. Kuma mutumin da ya auri macen da aka sake, zina ne yake yi.

  48. 29 Ango ne mai amarya. Abokin da yake masa hidima yakan jira ya kuma saurara masa, yakan kuma cika da farin ciki sa’ad da ya ji muryar ango. Wannan farin cikin kuwa nawa ne, ya kuma cika a yanzu.

  49. 34 “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”

  50. 16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

    Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.