33 Bible Verses About Retirement

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Retirement
  1. 23 Ubangiji ya ce wa Musa, 24 “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada, 25 amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki. 26 Za su iya taimakon ’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”

  2. 12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino,

    za su yi girma kama al’ul na Lebanon;

    13 da aka daddasa a gidan Ubangiji,

    za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.

    14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu,

    za su kasance ɗanye kuma kore shar,

    15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;

    shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

  3. 3 “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,

    dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,

    ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,

    na kuma riƙe ku tun haihuwarku.

    4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

    ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

    Na yi ku zan kuma riƙe ku;

    zan lura da ku

    in kuma kuɓutar da ku.

    5 “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni?

    Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?

  4. 31 Furfura rawani ne mai daraja;

    akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.

  5. 31 Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.

    32 “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin. 33 Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba. 34 Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.

  6. 1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

    3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu,

  7. 18 Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”

    19 Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi. 20 Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”

    21 Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali. 22 Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.

    23 Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida. 24 Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar. 25 Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”

  8. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  9. 16 Bari a nuna ayyukanka ga bayinka,

    darajarka ga ’ya’yansu.

    17 Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;

    ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,

    I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

  10. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

  11. 31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”

    32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.

  12. 16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

    18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

    20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

    21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

  13. 23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.

  14. 25 Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

    duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

    ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.

  15. 5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,

    ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

    6 Daga haihuwa na dogara gare ka;

    kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.

    Kullayaumi zan yabe ka.

    7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,

    amma kai ne katangata mai ƙarfi.

    8 Bakina ya cika da yabonka,

    ina furta darajarka dukan yini.

    9 Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa;

    kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.

  16. 6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

    ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

    7 Ba shi da jagora

    ba shugaba ko mai mulki,

    8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

    ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

  17. 22 Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa,

    amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.

  18. 20 A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau,

    amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.

  19. 19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20 Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21 Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.

  20. 3 Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku. 4 A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

  21. 10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

    11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci.

  22. 16 Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka;

    zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.

    17 Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini

    har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.

    18 Ko sa’ad da na tsufa da furfura,

    kada ka yashe ni, ya Allah,

    sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa,

    ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

    19 Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah,

    kai da ka yi manyan abubuwa.

    Wane ne kamar ka, ya Allah?

  23. 1 Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata

    ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,

  24. 15 Ku sha ruwa daga tankinku,

    ruwa mai gudu daga rijiyarku.

  25. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  26. 24 Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

  27. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

  28. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  29. 8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

  30. 11 Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure. 12 Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko. 13 Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba. 14 Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna. 15 Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.

  31. 17 Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. 18 Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.” 19 Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. 20 Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.

  32. 7 Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.

  33. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”