25 Bible Verses About Grandmothers

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Grandmothers
  1. 3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.

  2. 6 Jikoki rawanin tsofaffi ne,

    kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.

  3. 12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

  4. 13 da aka daddasa a gidan Ubangiji,

    za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.

    14 Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu,

    za su kasance ɗanye kuma kore shar,

    15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;

    shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

  5. 1 Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. 2 Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

    3 Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. 4 Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, 5 su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  6. 9 Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.

  7. 9 A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda, 10 ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom.

    11 Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. 12 Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi. 13 Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. 14 Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

  8. 31 Furfura rawani ne mai daraja;

    akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.

  9. 28 Ba ku sani ba?

    Ba ku ji ba?

    Ubangiji madawwamin Allah ne,

    Mahaliccin iyakokin duniya.

    Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,

    kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.

    29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji

    yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.

    30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  10. 22 Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa,

    amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.

  11. 13 Sai Bowaz ya ɗauki Rut ta kuwa zama matarsa. Sa’an nan ya kwana da ita, Ubangiji kuma ya sa ta yi ciki, ta haifi ɗa. 14 Mata suka ce wa Na’omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila! 15 Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ’ya’ya maza bakwai, ta haife shi.”

    16 Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi. 17 Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.

  12. 17 Amma daga madawwami zuwa madawwami

    ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

    adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  13. 32 “ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  14. 25 Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,

    duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba

    ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.

    26 Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba,

    za a yi wa ’ya’yansu albarka.

  15. 4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

    ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

    Na yi ku zan kuma riƙe ku;

    zan lura da ku

    in kuma kuɓutar da ku.

    5 “Da wa za ku kwatanta ni ko ku ɗauka daidai da ni?

    Da wa nake kama da har da za ku kwatanta ni?

  16. 4 Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;

    za mu faɗa wa tsara mai zuwa

    ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,

    ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.

    5 Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub

    ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila,

    wadda ya umarce kakanni-kakanninmu

    su koya wa ’ya’yansu,

    6 don tsara na biye su san su,

    har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba,

    su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.

    7 Ta haka za su dogara ga Allah

    ba kuwa za su manta da ayyukansa ba

    amma za su kiyaye umarnansa.

    8 Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba,

    masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa,

    waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba,

    waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.

  17. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

    5 Sai Toma ya ce masa, “Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, to, ta yaya za mu san hanyar?”

    6 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.

  18. 9 Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.”

    Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”

  19. 4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;

    za su yi magana game da manyan ayyukanka.

  20. 12 Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  21. 1 Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka, 2 saboda ku, ’ya’yanku, da kuma ’ya’yansu bayansu za su ji tsoron Ubangiji Allahnku muddin kuna rayuwa ta wurin kiyaye dukan ƙa’idodinsa da umarnan da na ba ku, da kuma don ku yi tsawon rai.

  22. 17 Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini

    har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.

    18 Ko sa’ad da na tsufa da furfura,

    kada ka yashe ni, ya Allah,

    sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa,

    ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

  23. 1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

  24. 10 aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

  25. 5 Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

    “Allah yana gāba da mai girman kai,

    amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”