63 Bible Verses About Faith
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. 2 Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan.
3 Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.
4 Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, sa’ad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu.
5 Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah. 6 In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
7 Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
8 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba. 9 Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi. 10 Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne. 11 Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne. 12 Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.
13 Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya. 14 Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu.
-
8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela. 9 Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. 11 Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” 12 Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, 13 gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
-
1 To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu? 2 In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba. 3 Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
4 To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa. 5 Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne.
-
8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
-
21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.
27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin da zamu yi taƙama a kai. A kan wace ƙa’ida ce za mu yi taƙama? Ta hanyar bin doka ne? A’a, sai dai ta wurin bangaskiya. 28 Gama mun tsaya a kan cewa ta wurin bangaskiya ne ake kuɓutar da mutum, ba ta wurin kiyaye doka ba. 29 Allah ɗin, Allahn Yahudawa ne kaɗai? Shi ba Allahn Al’ummai ba ne? I, shi Allahn Al’ummai ne ma, 30 da yake Allah ɗaya ne kaɗai, shi kuma zai kuɓutar da masu kaciya bisa ga bangaskiya da kuma marasa kaciya ta wurin wannan bangaskiya ɗin. 31 To, za mu soke dokar saboda wannan bangaskiyar ne? Ko kaɗan! A maimako, sai ma tabbatar da ita muke yi.
-
20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22 Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
-
5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.
-
18 Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.
19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. 24 Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. 25 Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu.
-
16 Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai. 17 Gama a cikin bishara an bayyana adalci daga Allah wanda yake ta wurin bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
18 Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, 19 gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. 20 Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
21 Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.
-
16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
23 Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
24 Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
-
18 Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
19 Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”
20 Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
-
14 Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? 15 A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, 16 sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? 17 Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
18 Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.”
Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi. 19 Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
20 Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?
-
5 Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.
6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba.
-
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;
ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
-
1 Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2 Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3 Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5 Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
-
24 Toma kuwa (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran sa’ad da Yesu ya zo. 25 Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”
Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba, ba zan gaskata ba.”
26 Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!” 27 Sa’an nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”
28 Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
29 Sai Yesu ya ce masa, “Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”
-
38 Duk wanda ya gaskata da ni, kamar yadda Nassi ya ce, kogunan ruwa masu rai za su gudana daga cikinsa.” 39 Da wannan yana nufin Ruhu ke nan, wanda waɗanda suka gaskata da shi za su karɓa daga baya. Har yă zuwa wannan lokaci ba a ba da Ruhu ba tukuna, da yake ba a riga an ɗaukaka Yesu ba.
-
20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
-
16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita.
-
5 Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”
-
15 “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba, 16 mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.
-
7 Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. 8 A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. 9 An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. 10 Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. 11 Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. 12 Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
13 A rubuce yake cewa, “Na gaskata; saboda haka na yi magana.” Da wannan ruhun bangaskiya ne mu ma muka gaskata, saboda haka muke magana. 14 Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.
-
10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali. 12 Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.
-
22 bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
-
32 Amma Yesu ya ci gaba da dubawa don yă ga wa ya taɓa shi. 33 Matar, da yake ta san abin da ya faru da ita, sai ta zo ta durƙusa a gabansa, da tsoro da rawan jiki, ta kuma gaya masa dukan abin da ya faru. 34 Sai ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, kin kuma rabu da dukan wahalarki.”
35 Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.”
36 Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”
-
7 Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. 8 Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
-
43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
45 Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?”
Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
46 Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
47 Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48 Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
-
25 Yesu ya ce mata, “Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu; 26 kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”
27 Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
-
3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.
-
8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda.
-
13 Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.
-
1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
-
16 Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.
-
36 Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
-
26 Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 27 Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.
-
5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.
10 Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.
-
21 Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon. 22 Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”
23 Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”
24 Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”
25 Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”
26 Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”
27 Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”
28 Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.
-
2 In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.
-
21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23 Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
-
20 Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.
-
52 Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
-
43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
-
29 Ya ce, “Zo.”
Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu. 30 Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”
31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
32 Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta. 33 Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”
-
48 Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”
49 Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
50 Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”
-
40 Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
-
8 Filibus ya ce, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan kuwa zai biya bukatarmu.”
9 Yesu ya amsa ya ce, “Ba san ni ba, Filibus, duk da daɗewan nan da na yi tare da ku? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’? 10 Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa. 11 Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu. 12 Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba. 13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. 14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
-
5 Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. 6 Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; 7 hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. 8 Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
9 Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne. 10 Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci. 11 In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.
12 Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba. 13 Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.
14 Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah. 15 Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “Abba, Uba.” 16 Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. 17 In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
-
11 A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.” 12 Doka ba tă dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.” 13 Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.” 14 Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yă zo ga Al’ummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.
-
13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
-
8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
-
35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37 Gama,
“A cikin ɗan lokaci kaɗan,
mai zuwan nan zai zo
ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38 Amma,
“Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.
In kuwa ya ja da baya,
ba zan ji daɗinsa ba.”
39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.
-
28 Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
29 Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
-
1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. 2 Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai.
-
5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,
wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi
wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;
ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.
Za su zauna a busassun wuraren hamada,
a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.
Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;
ganyayensa kullum kore suke.
Ba shi da damuwa a shekarar fări
ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
-
6 Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
-
47 Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
-
24 Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”
-
23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.
-
13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
-
15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
-
2 Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba.
Shows Read in context, Share and Copy.