45 Bible Verses About Insecurity

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Insecurity
  1. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  2. 25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

    28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  3. Ta Dawuda.

    1 Kada ka tsorata saboda mugayen mutane

    ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

    2 gama kamar ciyawa za su bushe,

    kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

    3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

    yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

    4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

    zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

  4. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

  5. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

    19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  6. 5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

    wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

    wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

    6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

    ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

    Za su zauna a busassun wuraren hamada,

    a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

    7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

    wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

    8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  7. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

    18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

  8. 17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  9. 1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  10. 13 Gama ka halicci ciki-cikina;

    ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

    14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

    ayyukanka suna da banmamaki,

    na san da haka sosai.

    15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

    sa’ad da aka yi ni asirce.

    Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

  11. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  12. 3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama

    shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

    domin ya dogara a gare ka.

  13. 1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

  14. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  15. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  16. 25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,

    amma maganar alheri kan faranta masa rai.

  17. 1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.

  18. 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

  19. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  20. 15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.

  21. 8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”

  22. 7 Amma Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Kada ka dubi kyan tsarinsa ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai daga waje, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”

  23. 10 Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,

    gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  24. 5 Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na;

    ka kiyaye rabona,

    6 Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi;

    tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

    7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;

    ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

    8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

    9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;

    jikina kuma zai zauna lafiya,

  25. 18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”

    ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

    19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,

    ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

  26. 26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

    kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

  27. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

  28. 14 Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya.

  29. 27 “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28 In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.

  30. 10 Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

    11 Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne? 12 Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”

  31. 24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

  32. 31 Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

  33. 16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

    18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

    20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

    21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”

  34. 32 Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”

  35. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.

  36. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

  37. 7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

  38. 16 Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. 17 In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.

  39. 34 Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?

  40. 37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  41. 4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. 5 Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. 6 A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.

  42. 9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

  43. 3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.

  44. 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

  45. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.