42 Bible Verses About Confidence

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Confidence
  1. 24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;

    sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.

    25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya

    ko lalacin da yakan auka wa mugaye,

    26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka

    zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.

  2. 3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba, 4 ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka.

    In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi, 5 an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne; 6 wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne.

    7 Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. 8 Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi 9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.

  3. 13 Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. 14 Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15 In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.

  4. 31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?

  5. 32 Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33 Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. 35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.

    36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari.

  6. 5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu, 6 da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.

  7. 8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga mutum.

    9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga sarakuna.

  8. 5 Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

    6 “Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. 7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. 8 Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  9. 8 “Amma kai, ya Isra’ila, bawana,

    Yaƙub, wanda na zaɓa,

    zuriyar Ibrahim abokina,

    9 na ɗauke ka daga iyakar duniya,

    daga kusurwoyi masu nesa na kira ka.

    Na ce, ‘Kai bawana ne’;

    na zaɓe ka ban kuwa ƙi ka ba.

    10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  10. 12 A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi.

  11. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  12. 14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  13. 5 Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

    6 Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. 7 Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. 8 Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. 9 Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.

  14. 26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,

    kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.

  15. 7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

    wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

    8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  16. 1 Yabon kanmu ne kuma muka fara yi? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi? 2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta. 3 Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.

    4 Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah. 5 Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne. 6 Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

  17. 17 Aikin adalci zai zama salama;

    tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

  18. 16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

    Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

  19. 7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,

    amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

    8 Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi,

    amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

  20. Ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne haskena da cetona,

    wa zan ji tsoro?

    Ubangiji ne mafakar raina,

    wane ne zan ji tsoro?

    2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini

    don su cinye ni,

    sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,

    sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

    3 Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,

    zuciyata ba za tă ji tsoro ba;

    ko da yake ya ɓarke a kaina,

    duk da haka zan ƙarfafa.

    4 Abu guda na roƙi Ubangiji,

    wannan shi ne na nema,

    cewa in zauna a gidan Ubangiji

    dukan kwanakin raina,

    in dubi kyan Ubangiji

    in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  21. 24 “In na dogara ga zinariya

    ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’

  22. 4 Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye,

    da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.

    5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,

    ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

    6 Daga haihuwa na dogara gare ka;

    kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.

    Kullayaumi zan yabe ka.

    7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,

    amma kai ne katangata mai ƙarfi.

  23. 3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

  24. 9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,

  25. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  26. 21 Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan.

  27. 32 Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”

    33 Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”

    34 Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita. 35 Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe. 36 Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai. 37 Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.”

    Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  28. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

    1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

    kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

    2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

    duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

    3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

    duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

  29. 3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

    4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

    ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

  30. 13 Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.

  31. 5 Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. 6 Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.

  32. 14 Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe.

  33. 17 Sai ya ƙara da cewa,

    “Zunubansu da kurakuransu

    ba zan ƙara tunawa da su ba.”

    18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.

    19 Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, 20 ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, 21 da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, 22 bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.

  34. 28 Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.

  35. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  36. 1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.

  37. 28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

  38. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  39. 1 Ba ni da ’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba? 2 Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.

    3 Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina.

  40. 16 Ina farin ciki ne don na amince da ku ƙwarai da gaske.

  41. 13 Waɗanda suke hidima da kyau suna samar wa kansu kyakkyawan suna da kuma cikakken tabbatarwa a cikin bangaskiyarsu cikin Kiristi Yesu.

  42. 1 Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba.