74 Bible Verses About Safety
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
17 Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.
18 “ ‘Ku bi farillaina, ku kuma yi hankali ga kiyaye dokokina, za ku kuwa zauna lafiya a ƙasar. 19 Sa’an nan ƙasar za tă ba da amfaninta, za ku kuwa ci ku ƙoshi, ku kuma zauna lafiya.
-
1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8 Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai
don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
12 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
13 Za ka taka zaki da gamsheƙa;
za ka tattake babban zaki da maciji.
14 Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi;
zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
15 Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala,
zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
16 Da tsawon rai zan ƙosar da shi
in kuma nuna masa cetona.”
-
10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
11 Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
12 Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
-
6 Yawanci suna cewa, “Wa zai yi mana alheri?”
Bari hasken fuskarka yă haskaka a kanmu, ya Ubangiji.
7 Ka cika zuciyata da farin ciki
sa’ad da hatsinsu da sabon ruwan inabinsu ya yi yawa.
8 Zan kwanta in kuma yi barci lafiya,
gama kai kaɗai, ya Ubangiji,
kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
-
25 Jin tsoron mutum tarko ne,
amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
-
3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;
ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,
ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela
5 Na kwanta na yi barci;
na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma
suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
-
5 Ubangiji yana tsaronka,
Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba
balle wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa,
zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka
yanzu da har abada kuma.
-
2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
-
21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira,
kada ka bar su su rabu da kai;
22 za su zama rai a gare ka,
abin adon da zai gyara wuyanka.
23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya,
ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba;
sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya
ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka
zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
-
27 Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29 Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30 Da ni da Uba ɗaya ne.”
-
17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
-
8 Kada ku yi kamar yadda muke yi a nan yau, yadda kowa yake yin abin da ya ga dama. 9 Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna. 10 Amma sa’ad da kuka haye Urdun, kuka zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, zai kuwa ba ku hutu daga dukan abokan gābanku da suke kewaye da ku, kuka sami zaman lafiya, 11 sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa. 12 A can kuma za ku yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku, ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, waɗanda ba a ba su rabo ba, ba su kuma da gādo na kansu. 13 Ku kula fa kada ku miƙa hadayun ƙonawa a wani wurin da kuka ga dama. 14 Ku miƙa su kawai a wurin da Ubangiji zai zaɓa a cikin ɗaya daga kabilanku, a can za ku yi kowane abin da na umarce ku.
-
33 amma duk wanda ya saurare ni, zai zauna lafiya
yă kuma kasance da rai kwance, ba tare da tsoron lahani ba.”
-
35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;
an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
-
12 Game da Benyamin ya ce,
“Bari ƙaunataccen Ubangiji yă zauna lafiya kusa da shi,
gama yana tsare shi dukan yini,
wanda kuma Ubangiji yake ƙauna yana zama a tsakanin kafaɗunsa.”
-
8 “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah;
zan gaya masa damuwata.
9 Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa,
mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa.
10 Yana zuba ruwan sama a ƙasa;
yana zuba ruwa a gonaki.
11 Yana ɗaukaka masu sauƙinkai,
yana kāre waɗanda suke makoki.
12 Yana dagula shirye-shiryen masu wayo
don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi.
13 Yana kama masu wayo cikin wayonsu,
yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba.
14 Da rana sukan yi karo da duhu;
da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke.
15 Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi;
yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
16 Saboda haka matalauta suna da bege,
rashin gaskiya kuma ta yi shiru.
-
14 Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi,
amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
-
20 “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa. 21 A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin. 22 Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta. 23 Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.
-
10 Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.
11 Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.
-
3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;
yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
-
15 “ ‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci
zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda;
zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar.
16 A kwanakin nan zan ceci Yahuda
Urushalima kuma za tă zauna lafiya.
Sunan da za a kira ta shi ne,
Ubangiji Adalcinmu.’
-
11 “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. 12 Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. 13 Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.
14 “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, 15 kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.
-
3 Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan. 4 Muna da tabbaci cikin Ubangiji cewa kuna bin umarnai da muka yi muku, za ku kuma ci gaba da yin abubuwan da muka umarta. 5 Bari Ubangiji yă bi da zukatanku ga ƙaunan nan ta Allah da kuma jimirin nan na Kiristi.
-
18 Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.
-
1 “ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
2 “ ‘Ku kiyaye Asabbataina, ku kuma ba wa wuri mai tsarkina girma. Ni ne Ubangiji.
3 “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5 Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.
6 “ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba.
-
4 Ko da na yi tafiya
ta kwari na inuwar mutuwa,
ba zan ji tsoron mugu ba,
gama kana tare da ni;
bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,
za su yi mini ta’aziyya.
-
7 Kai ne wurin ɓuyata;
za ka tsare ni daga wahala
ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela
-
53 Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro;
amma teku ya cinye abokan gābansu.
-
7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala,
kana kiyaye raina;
ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana,
da hannunka na dama ka cece ni.
8 Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;
ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,
kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye;
ka tsare ni daga mutane masu rikici,
2 masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu
suna kuma kawo yaƙi kullum.
3 Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji;
dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela
4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;
ka tsare ni daga mutane masu rikici
waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
-
7 Ubangiji nagari ne,
mafaka kuma a lokacin wahala.
Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
-
9 Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. 10 Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
su kiyaye ka da kyau;
11 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
12 Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
13 Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.
-
31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?
-
2 Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, 3 “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.”
-
25 A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.
-
7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya
ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
-
Miktam ne na Dawuda.
1 Ka kiyaye ni, ya Allah,
gama a cikinka nake samun mafaka.
-
13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,
amma ka cece mu daga mugun nan. ’
-
15 “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane), 16 to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. 17 Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida. 18 Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa. 19 Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21 Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
22 “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. 23 A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25 Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
26 “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27 Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. 28 Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
-
12 Yayinda nake tare da su, na kāre su na kuma kiyaye su ta wurin sunan nan da ka ba ni. Ba ko ɗayan da ya ɓace, sai dai wannan da aka ƙaddara zuwa ga hallaka don Nassi yă cika.
-
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
-
1 A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.
-
15 Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”
16 Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai. 17 Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!”
-
8 Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido;
ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka
9 daga mugaye waɗanda suke kai mini hari,
daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
10 Sun rufe zukatansu marar tausayi,
da bakunansu suna magana da fariya.
-
4 Abu guda na roƙi Ubangiji,
wannan shi ne na nema,
cewa in zauna a gidan Ubangiji
dukan kwanakin raina,
in dubi kyan Ubangiji
in kuma neme shi a cikin haikalinsa.
5 Gama a lokacin wahala,
zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa;
zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa
ya kuma sa ni can a bisa dutse.
-
19 Alherinka da girma yake,
wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,
wanda ka mayar a gaban mutane
a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su
daga makircin mutane;
a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya
daga harsuna masu zagi.
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji,
gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni
sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.
-
8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini,
daga tarkon da mugaye suka sa.
10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu,
amma bari ni in zo in wuce lafiya.
-
28 Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya;
ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
-
18 Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya,
amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.
-
26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne,
amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.
-
1 A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda.
Muna da birni mai ƙarfi;
Allah yake ceton
katanga da kuma kagarunta.
2 A buɗe ƙofofi
saboda al’umma mai adalci ta shiga,
al’ummar da mai aminci.
3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama
shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,
domin ya dogara a gare ka.
4 Ku dogara ga Ubangiji,
gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
5 Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa
ya kawar da birni mai alfarma ƙasa;
ya rusa ta har ƙasa
ya jefar da ita cikin ƙura.
6 Ƙafafu sukan tattake ta,
ƙafafu waɗanda aka zalunta,
wato, sawun matalauta.
-
10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;
kada ka karai, gama ni ne Allahnka.
Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;
zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
11 “Duk wanda ya yi fushi da kai
tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;
waɗanda suka yi hamayya da kai
za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.
12 Ko ka nemi abokan gābanka,
ba za ka same su ba.
Waɗanda suke yaƙi da kai
za su zama kamar ba kome ba.
-
2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,
zan kasance tare da ku;
sa’ad da kuka bi ta koguna,
ba za su kwashe ku ba.
Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,
ba za tă ƙone ku ba;
harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
-
5 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci,
Sarki wanda zai yi mulki da hikima
ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
6 A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda
Isra’ila kuma zai zauna lafiya.
Sunan da za a kira shi ke nan,
Ubangiji Adalcinmu.
-
37 tabbatacce zan tattara su daga dukan ƙasashen da na kore su zuwa cikin fushina da hasalata mai girma; zan komo da su wurin nan in sa su zauna lafiya. 38 Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu.
-
13 Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
14 Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, 15 inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”
-
27 Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.
28 “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine. 29 Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.
30 “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana. 31 A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu. 32 Ku tuna fa da matar Lot! 33 Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi. 34 Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan. 35 Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.”
37 Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?”
Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”
-
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
-
7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.
-
11 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.
-
13 Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. 14 Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. 15 Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. 16 Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. 17 Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
-
18 Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
-
8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.
Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
-
8 Yadda muka ji,
haka muka gani
a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki,
a cikin birnin Allahnmu.
Allah ya sa ta zauna lafiya
har abada. Sela
-
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji
zai kuwa riƙe ku;
ba zai taɓa barin
mai adalci yă fāɗi ba.
-
2 Shi kaɗai ne dutsena da cetona;
shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
-
8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
-
Waƙar haurawa.
1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,
wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.
2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,
haka Ubangiji ya kewaye mutanensa
yanzu da har abada kuma.
-
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka,
kuma ga ’ya’yansa zai zama mafaka.
-
10 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,
ku yi yabonsa daga iyakar duniya,
ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,
ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.
11 Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;
bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.
Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;
bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.
12 Bari su ɗaukaka Ubangiji
su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.
13 Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi,
kamar jarumi zai yi himma;
da ihu zai tā da kirarin yaƙi
zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.
-
18 A waccan rana zan yi alkawari dominsu
da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama
da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa.
Baka da takobi da yaƙi
zan sa su ƙare a ƙasar,
domin duk su zauna lafiya.
-
11 Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya.
-
16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’
18 “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’
20 “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’
21 “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”
-
15 Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
Shows Read in context, Share and Copy.