64 Bible Verses About Panic Attacks

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Panic Attacks
  1. 25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

    28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

  2. 4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! 5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

    8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

    10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

    14 Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.

  3. 5 Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

    “Allah yana gāba da mai girman kai,

    amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”

    6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

    8 Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

    10 Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11 Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin.

  4. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

    11 “Duk wanda ya yi fushi da kai

    tabbatacce zai sha kunya da ƙasƙanci;

    waɗanda suka yi hamayya da kai

    za su zama kamar ba kome ba su kuma hallaka.

    12 Ko ka nemi abokan gābanka,

    ba za ka same su ba.

    Waɗanda suke yaƙi da kai

    za su zama kamar ba kome ba.

    13 Gama ni ne Ubangiji Allahnka,

    wanda ya riƙe ka da hannun damana

    ya kuma ce maka, Kada ka ji tsoro;

    zan taimake ka.

    14 Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub marar ƙarfi,

    ya ƙaramin Isra’ila,

    gama ni kaina zan taimake ka,” in ji Ubangiji,

    Mai Fansarka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  5. 22 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23 Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa! 25 Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa? 26 Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?

    27 “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba. 28 In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya! 29 Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.

  6. 25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum,

    amma maganar alheri kan faranta masa rai.

  7. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”

  8. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

    7 Kada ka zama mai hikima a ganinka;

    ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

    8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya

    yă kuma adana ƙasusuwanka.

  9. 22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji

    zai kuwa riƙe ku;

    ba zai taɓa barin

    mai adalci yă fāɗi ba.

    23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye

    zuwa cikin ramin lalacewa;

    masu kisa da mutane masu ruɗu

    ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba.

    Amma ni dai, na dogara gare ka.

  10. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

  11. 3 Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka.

    4 Ga Allah wanda maganarsa nake yabo

    ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum mai mutuwa zai yi mini?

  12. 31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? 32 Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?

  13. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  14. 18 Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”

    ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.

    19 Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,

    ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

    20 Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,

    wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?

  15. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

  16. 1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

    shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

    “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

    na kira ka da suna; kai nawa ne.

    2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

    zan kasance tare da ku;

    sa’ad da kuka bi ta koguna,

    ba za su kwashe ku ba.

    Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

    ba za tă ƙone ku ba;

    harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

    3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

    4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

    saboda kuma ina ƙaunarku,

    zan ba da mutane a maimakonku,

    al’umma kuma domin ranku.

  17. 4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;

    ya cece ni daga dukan tsoro.

    5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka;

    fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.

    6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi;

    ya cece shi daga dukan wahalarsa.

    7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa,

    ya kuwa cece su.

    8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau;

    mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  18. 26 Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. 27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

    28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.

  19. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

  20. 4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

  21. 8 Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  22. 5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

    ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

    6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya,

    gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

    7 Ka natsu a gaban Ubangiji

    ka kuma jira da haƙuri gare shi;

    kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu,

    sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

    8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala;

    kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.

    9 Gama za a datse mugayen mutane,

    amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.

  23. 5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

    wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

    wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

    6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

    ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

    Za su zauna a busassun wuraren hamada,

    a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

    7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

    wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

    8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

    wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

    Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

    ganyayensa kullum kore suke.

    Ba shi da damuwa a shekarar fări

    ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  24. 3 Za ka kiyaye shi da cikakken salama

    shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka,

    domin ya dogara a gare ka.

  25. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.

  26. 15 Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

  27. 3 Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi,

    ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji;

    4 ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata,

    “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro;

    Allahnku zai zo,

    zai zo domin ya ɗau fansa;

    da ramuwar Allah

    zai zo don yă cece ku.”

  28. 30 Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

    samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

    31 amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

    za su sabunta ƙarfinsu.

    Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

    za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

    za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

  29. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  30. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

    an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”

    37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  31. 16 Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.

  32. 17 Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18 Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.

    19 Muna ƙauna, domin ya ƙaunace mu da farko.

  33. 6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”

  34. 5 Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji,

    ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.

    6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai yi mini?

    7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona.

    Zan yi nasara a kan abokan gābana.

    8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

    da in dogara ga mutum.

  35. Waƙar haurawa.

    1 Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,

    ta ina ne taimakona zai zo?

    2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,

    wanda ya kafa sama da ƙasa.

  36. 22 Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.

  37. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  38. Ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne haskena da cetona,

    wa zan ji tsoro?

    Ubangiji ne mafakar raina,

    wane ne zan ji tsoro?

    2 Sa’ad da mugaye suka tasar mini

    don su cinye ni,

    sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari,

    sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

    3 Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni,

    zuciyata ba za tă ji tsoro ba;

    ko da yake ya ɓarke a kaina,

    duk da haka zan ƙarfafa.

  39. 10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

    za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

    za a ɗaukaka ni cikin duniya.”

  40. 38 Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da ’yar’uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa. 40 Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ’yar’uwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”

    41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa. 42 Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”

  41. 19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

  42. 17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;

    yakan cece su daga dukan wahalarsu.

    18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

    19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,

    amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  43. 16 A wannan rana za su cewa Urushalima,

    “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;

    kada ki bar hannuwanki su raunana.

    17 Ubangiji Allahnki yana tare da ke,

    mai iko ne don ceto.

    Zai yi matuƙar farin ciki da ke,

    zai rufe ki da ƙaunarsa,

    zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”

  44. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

    1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

    kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

    2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

    duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

    3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

    duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

  45. 26 “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

    32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. 33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.

  46. 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

  47. 28 Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.

  48. 13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”

  49. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

  50. 14 Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”

  51. 7 Sai Musa ya kira Yoshuwa, ya ce masa a gaban dukan Isra’ila, “Ka ƙarfafa, ka kuma yi ƙarfin hali, gama dole ka tafi tare da mutanen nan zuwa cikin ƙasar da Ubangiji ya rantse cewa za ba wa kakanninku, dole kuma ka raba ta gare su ta zama gādonsu. 8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”

  52. 8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

  53. 8 Ubangiji zai cika manufarsa a kaina;

    ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada,

    kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

  54. 25 Jin tsoron mutum tarko ne,

    amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.

  55. 22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;

    gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

    23 Sababbi ne kowace safiya;

    amincinka kuwa mai girma ne.

    24 Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;

    saboda haka zan jira shi.”

  56. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.

  57. 22 Kada ku ji tsoronsu, gama Ubangiji Allahnku zai yi yaƙi dominku.”

  58. 64 Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba. 65 A cikin waɗancan al’ummai ba za ku sami hutu ba, ba wurin hutu wa tafin ƙafanku. A can Ubangiji zai sa fargaba a zuciyarku, yă sa idanunku su lalace, ranku zai yi suwu. 66 Za ku yi zama cikin damuwa kullum, cike da tsoro, dare da rana, ba tabbacin abin da zai faru da ranku. 67 Da safe za ku ce, “Da ma yamma ne!” Da yamma kuma ku ce, “Da ma safiya ce!” Saboda tsoron da ya cika zukatanku da kuma abubuwan da idanunku za su gani.

  59. Ta Dawuda.

    1 Kada ka tsorata saboda mugayen mutane

    ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;

    2 gama kamar ciyawa za su bushe,

    kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.

  60. 16 Amma na kira ga Allah,

    Ubangiji kuwa ya cece ni.

    17 Safe, rana da yamma

    ina kuka da nishi,

    yakan kuwa ji muryata.

    18 Yakan fisshe ni lafiya

    daga yaƙin da ake yi da ni,

    ko da yake da yawa suna gāba da ni.

  61. 23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

    26 Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

    27 Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

  62. 32 Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33 Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa 34 hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta. 35 Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

  63. 6 In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.

  64. 1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah.