56 Bible Verses About Pain

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Pain
  1. 16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

  2. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

  3. 16 Sa’an nan ya ce wa macen,

    “Zan tsananta naƙudarki ainun,

    da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.

    Za ki riƙa yin marmarin mijinki

    zai kuwa yi mulki a kanki.”

    17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’

    “Za a la’anta ƙasa saboda kai.

    Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.

    18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya

    za ka kuwa ci ganyayen gona.

    19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,

    da yake daga cikinta aka yi ka.

    Gama kai turɓaya ne,

    kuma ga turɓaya za ka koma.”

  4. 1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

  5. 1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,

    Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.

    2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

    3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. 7 Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.

    8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.

  6. 7 A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. 8 Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala 9 kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. 10 Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.

  7. 1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”

    3 Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”

  8. 22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.

  9. 2 Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, 3 domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. 4 Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.

  10. Ta Dawuda. Maskil ne.

    1 Mai farin ciki ne shi

    wanda aka gafarta masa laifofinsa,

    wanda aka shafe zunubansa.

    2 Mai farin ciki ne mutumin

    da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa

    wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.

    3 Sa’ad da na yi shiru,

    ƙasusuwana sun yi ta mutuwa

    cikin nishina dukan yini.

    4 Gama dare da rana

    hannunka yana da nauyi a kaina;

    an shanye ƙarfina ƙaf

    sai ka ce a zafin bazara. Sela

    5 Sa’an nan na furta zunubina a gare ka

    ban kuwa ɓoye laifina ba.

    Na ce, “Zan furta

    laifofina ga Ubangiji.”

    Ka kuwa gafarta

    laifin zunubina. Sela

  11. 18 Me ya sa wahalata ba ta ƙarewa

    mikina kuma ba ya warkuwa?

    Za ka zama mini kamar rafi mai yaudara ne,

    kamar maɓulɓulan da ta kafe ne?

    19 Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “In ka tuba, zan maido da kai

    don ka bauta mini;

    in ka ambaci maganganu masu kyau, ba marasa kyau ba,

    za ka zama kakakina.

    Bari wannan mutane su juyo gare ka,

    amma kada ka juye gare su.

  12. 5 Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,

    “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,

    kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

    6 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

    7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? 8 In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. 9 Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! 10 Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. 11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.

  13. 6 Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.”

    7 Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. 8 Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.

    9 Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!”

    10 Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?”

    A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.

    11 Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. 12 Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, 13 sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.

  14. 22 Zafin jikinsa kaɗai yake ji

    yana kuka wa kansa ne kaɗai.”

  15. 17 Dare ya huda ƙasusuwana;

    ina ta shan azaba ba hutawa.

    18 A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina;

    ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.

  16. 7 Bayana yana fama da zazzaɓi;

    babu lafiya a jikina.

  17. 2 Ku saki zuciya da mu. Ba mu yi wa kowa laifi ba, ba mu ɓata kowa ba, ba mu cuci kowa ba. 3 Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. 4 Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.

    5 Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. 6 Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus, 7 ba ma don zuwansa kaɗai ba, har ma a game da ƙarfafa zuciyan nan da ya samu a wurinku. Ya gaya mana yadda kuke so ku gan ni sosai, da kuma yadda kuka yi baƙin ciki game da abin da ya faru, da niyyar da kuka yi na goyon bayana. Wannan ne ya sa na ji daɗi ƙwarai.

    8 Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. 9 Duk da haka, yanzu ina farin ciki, ba don na sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin baƙin cikinku ya kai ku ga tuba. Gama kun yi baƙin ciki kamar yadda Allah ya so, saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba. 10 Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. 11 Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.

  18. 15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji;

    za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.

    16 Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina

    ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”

    17 Gama ina gab da fāɗuwa,

    kuma cikin azaba nake kullum.

    18 Na furta laifina;

    na damu da zunubina.

  19. Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannot maskil na Heman dangin Ezra.

    1 Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni,

    dare da rana ina kuka a gabanka.

    2 Bari addu’ata ta zo a gabanka;

    ka kasa kunne ga kukata.

    3 Gama raina yana cike da wahala

    rayuwata tana gab da kabari.

  20. 47 In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, 48 inda

    “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,

    wutar kuma ba a iya kashewa.’

  21. 33 Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. 34 Sai ya yi tambaya ya ce, “Ina kuka sa shi?”

    Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.”

    35 Yesu ya yi kuka.

  22. 1 Saboda haka na yanke shawara ba zan sāke kawo muku ziyara ta ɓacin rai ba. 2 Gama in na sa ku baƙin ciki, wa ya rage yă faranta mini zuciya, in ba ku waɗanda na sa baƙin cikin ba? 3 Na rubuta yadda na yi ne saboda sa’ad da na iso kada waɗanda ya kamata su faranta mini rai, su sa ni baƙin ciki. Na amince da ku duka a kan farin cikina naku ne ku duka. 4 Gama na rubuta muku ne cikin baƙin ciki mai yawa da ɓacin zuciya har ma da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba ne, a’a, sai dai domin in nuna muku zurfin ƙaunar da nake yi muku.

    5 In wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma a wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba na faɗa haka don in matsa muku lamba ba ne.

  23. 23 In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. 24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. 25 Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. 26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. 27 Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.

  24. 22 Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ 23 Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.”

  25. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.

    1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?

    Me ya sa ka yi nisa da cetona,

    ka yi nesa daga kalmomin nishina?

  26. 18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

  27. 5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da kuma Allahna.

    6 Raina yana baƙin ciki a cikina;

    saboda haka zan tuna da kai

    daga ƙasar Urdun,

    a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.

  28. 9 Na ce wa Allah Dutsena,

    “Me ya sa ka manta da ni?

    Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,

    a danne a hannun abokin gāba?”

    10 Ƙasusuwana suna jin jiki da wahala

    yayinda maƙiyana suna mini ba’a,

    suna ce mini dukan yini,

    “Ina Allahnka ɗin?”

    11 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da kuma Allahna.

  29. 11 Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. 12 Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

  30. 54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”

    55 “Ya ke mutuwa, ina nasararki?

    Ya ke mutuwa, ina dafinki?”

    56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

    58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

  31. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  32. 32 Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, 33 waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, 34 suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. 35 Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. 36 Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. 37 Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci 38 duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

    39 Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. 40 Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.

  33. 20 Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. 21 Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

    22 “Bai taɓa yin laifi ba sam,

    ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”

    23 Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. 24 Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.

  34. 19 Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

  35. 15 Zan kuma sa ƙiyayya

    tsakaninka da macen,

    tsakanin zuriyarka da zuriyarta.

    Zai ragargaje kanka,

    kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

  36. 8 To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.

  37. 11 Bokaye suka kāsa tsayawa a gaban Musa saboda maruran da suke bisansu da a kan dukan Masarawa.

  38. 10 Da sai in ji daɗi

    duk zafin da nake sha

    ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

  39. 6 “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi;

    in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.

  40. 19 “Ko kuma mutum yă sha horo

    ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa,

    20 yadda zai ji ƙyamar abinci,

    har yă ƙi son abinci mafi daɗi.

    21 Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki

    kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito.

    22 Ransa yana matsawa kusa da rami,

    ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.

  41. 3 Saboda hasalarka babu lafiya a jikina;

    ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.

    4 Laifofina sun mamaye ni

    kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.

    5 Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari

    saboda wawancina na zunubi.

  42. 3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

    ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

    4 Ya lissafta yawan taurari

    ya kuma kira kowannensu da suna.

    5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

    ganewarsa ba shi da iyaka.

  43. 7 Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;

    kada ku juye daga abin da nake faɗa.

    8 Ku yi nesa da hanyarta,

    kana ku je kusa da ƙofar gidanta,

    9 don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu

    da kuma shekarunku ga wani marar imani,

    10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku

    wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.

    11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,

    sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.

    12 Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo!

    Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!

    13 Ban yi biyayya da malamaina ba

    ko in saurari masu koyar da ni.

    14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya

    a tsakiyar dukan taron.”

  44. 28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.

  45. 38 Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

  46. 16 Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”

  47. 28 “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.

  48. 33 Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

  49. 33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  50. 17 Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya. 18 Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya. 19 Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa. 20 Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. 21 Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.

    22 “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. 23 Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. 24 Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

  51. 15 Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.

  52. 27 Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.

  53. 13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege.

  54. 12 Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. 13 Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. 14 In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.

  55. 8 (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci)

  56. 12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. 14 Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.

    15 Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. 16 Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! 17 Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”