77 Bible Verses About When You Feel Alone

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About When You Feel Alone
  1. 35 Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? 36 Kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini;

    an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”

    37 A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. 38 Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, 39 ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  2. 9 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni,

    kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi;

    kai ne ka kasance mai taimakona.

    Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni,

    Ya Allah Mai cetona.

    10 Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni,

    Ubangiji zai karɓe ni.

  3. 18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

    19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

    Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

    23 Sai mutumin ya ce,

    “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

    nama kuma na namana.

    Za a ce da ita ‘mace,’

    gama an ciro ta daga namiji.”

    24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  4. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

    6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

    “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

    Me mutum zai iya yi mini?”

  5. 5 Uba ga marayu, mai kāre gwauraye,

    shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.

    6 Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai,

    ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi;

    amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.

  6. 15 “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada, 17 Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku. 18 Ba zan bar ku marayu ba; zan zo wurinku.

  7. 18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”

  8. 1 Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. 2 Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.”

    3 Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can. 4 Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” 5 Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci.

    Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.” 6 Ya duba kewaye, sai ga wainar burodi kusa da kansa a bisa garwashin wuta mai zafi, da kuma tulun ruwa. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya sāke kwanta.

    7 Mala’ikan Ubangiji ya sāke dawowa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za tă yi maka yawa.” 8 Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah.

  9. 29 Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30 sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

    31 Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! 32 Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

    33 Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34 A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

  10. 15 Idanuna kullum suna a kan Ubangiji,

    gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.

    16 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai,

    gama na kaɗaice ina kuma wahala.

    17 Damuwoyin zuciyata sun ninka;

    ka ’yantar da ni daga wahalata.

    18 Ka dubi wahalata da kuma azabata

    ka ɗauke mini dukan zunubaina.

    19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru

    da kuma yadda suka ƙara ƙina!

    20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;

    kada ka bari in sha kunya,

    gama na nemi mafaka daga gare ka.

    21 Bari mutunci da adalci su tsare ni,

    domin begena yana a kanka.

  11. 6 Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”

  12. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”

  13. 10 Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

    kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

    Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

    zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

  14. 31 Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata! 32 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.

    33 “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda.

    1 Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?

    Me ya sa ka yi nisa da cetona,

    ka yi nesa daga kalmomin nishina?

    2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba,

    da dare kuma ban yi shiru ba.

  16. 45 Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. 46 Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

  17. 1 Akwai wani mutum daga Ramatayim, mutumin Zuf daga ƙasar tuddan Efraim, sunansa Elkana, ɗan Yeroham, shi jikan Elihu ɗan Tohu, tattaɓa kunnen Zuf, mutumin Efraim. 2 Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.

    3 Shekara-shekara wannan mutum yakan haura daga garinsa zuwa Shilo domin yin sujada da miƙa hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki. A can kuwa ’ya’yan Eli maza biyu, Hofni da Finehas su ne firistoci na Ubangiji. 4 Duk sa’ad da rana ta kewayo don Elkana yă miƙa hadaya, yakan ba da kashin nama ga matarsa Feninna da dukan ’ya’yanta maza da mata. 5 Amma Hannatu kuwa sai yă ba ta babban rabo gama yana ƙaunarta ko da yake Ubangiji ya kulle mahaifarta. 6 Saboda Ubangiji ya kulle mahaifarta, sai kishiyarta ta dinga tsokanarta don tă ba ta haushi. 7 Wannan ya ci gaba shekara da shekaru. Duk lokacin da Hannatu ta haura zuwa haikalin Ubangiji, sai kishiyarta tă tsokane ta har tă yi ta kuka tă kuma ƙi cin abinci. 8 Elkana mijinta kuwa yakan ce mata, “Hannatu don me kike kuka? Me ya sa ba za ki ci abinci ba? Don me kika karaya? Ashe, ban fi ’ya’ya goma a gare ki ba?”

  18. 1 To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi da ya halicce ka, ya Yaƙub,

    shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila,

    “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka;

    na kira ka da suna; kai nawa ne.

    2 Sa’ad da kuka bi ta ruwaye,

    zan kasance tare da ku;

    sa’ad da kuka bi ta koguna,

    ba za su kwashe ku ba.

    Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta,

    ba za tă ƙone ku ba;

    harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.

    3 Gama ni ne Ubangiji, Allahnku,

    Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku;

    na bayar da Masar don fansa,

    Kush da Seba a maimakonku.

    4 Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona,

    saboda kuma ina ƙaunarku,

    zan ba da mutane a maimakonku,

    al’umma kuma domin ranku.

    5 Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku;

    zan kawo yaranku daga gabas

    in kuma tattara ku daga yamma.

  19. 16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

  20. 10 Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu. 11 Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina? 12 Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu? 13 Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’ 14 Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa. 15 In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”

  21. 4 Ko da na yi tafiya

    ta kwari na inuwar mutuwa,

    ba zan ji tsoron mugu ba,

    gama kana tare da ni;

    bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,

    za su yi mini ta’aziyya.

    5 Ka shirya mini tebur

    a gaban abokan gābana.

    Ka shafe kaina da mai;

    kwaf nawa ya cika har yana zuba.

    6 Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi

    dukan kwanakin raina,

    zan kuwa zauna a gidan Ubangiji

    har abada.

  22. 6 Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7 Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

  23. 5 Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

    6 “Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. 7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.

  24. 7 Na kuma ga wani abu marar amfani a duniya.

    8 Akwai wani mutum shi kaɗai;

    bai shi da ɗa ko ɗan’uwa.

    Ba shi da hutu daga wahalarsa,

    duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba.

    Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala,

    kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?”

    Wannan ma ba shi da amfani,

    harkar baƙin cikin ne kawai!

    9 Biyu sun fi ɗaya,

    gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.

    10 In ɗaya ya fāɗi,

    abokinsa zai taimake shi yă tashi.

    Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi

    ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!

    11 In mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna.

    Amma yaya mutum ɗaya zai ji ɗumi yana shi kaɗai?

    12 Ana iya shan ƙarfin mutum ɗaya,

    mutum biyu za su iya kāre kansu.

    Igiya riɓi uku tana da wuya tsinkawa.

  25. 28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

  26. 8 Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”

  27. 4 Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa;

    na manta in ci abinci.

    5 Saboda nishina mai ƙarfi

    na rame na bar ƙasusuwa kawai.

    6 Ni kamar mujiyar jeji ne,

    kamar mujiya a kufai.

    7 Na kwanta a faɗake; na zama

    kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.

  28. 6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. 7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

    8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. 9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  29. 14 Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. 15 Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

  30. 17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su;

    yakan cece su daga dukan wahalarsu.

    18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

    ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

    19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa,

    amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  31. 2 Na kawo gunagunina a gabansa;

    a gabansa na faɗa wahalata.

    3 Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina,

    kai ne wanda ya san hanyata.

    A hanyar da nake tafiya

    mutane sun kafa mini tarko.

    4 Duba ta damata ka gani;

    babu wanda ya kula da ni.

    Ba ni da mafaka;

    babu wanda ya kula da raina.

    5 Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

    Na ce, “Kai ne mafakata,

    rabona a ƙasar masu rai.”

    6 Ka saurari kukata,

    gama ina cikin matsananciyar bukata;

    ka cece ni daga waɗanda suke fafarata,

    gama sun fi ni ƙarfi sosai.

    7 Ka ’yantar da ni daga kurkuku,

    don in yabi sunanka.

    Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni

    saboda alherinka gare ni.

  32. 15 “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

    ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

    Mai yiwuwa ta manta,

    amma ba zan taɓa manta da ke ba!

    16 Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;

    katangarki kullum suna a gabana.

  33. 3 Mutane suka rena shi suka ƙi shi,

    mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.

    Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi

    aka rena shi aka yi banza da shi.

    4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu

    ya kuma daure da baƙin cikinmu

    duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,

    ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.

    5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,

    aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;

    hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,

    kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

  34. 3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”

    Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

    5 Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.

  35. 3 Ya warkar da masu raunanar zuciya

    ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

    4 Ya lissafta yawan taurari

    ya kuma kira kowannensu da suna.

    5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;

    ganewarsa ba shi da iyaka.

  36. 23 Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,

  37. 27 Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

  38. 23 Duk da haka kullum ina tare da kai;

    ka riƙe ni a hannun damana.

    24 Ka bishe ni da shawararka,

    bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

    25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba?

    Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

    26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,

    amma Allah ne ƙarfin zuciyata

    da kuma rabona har abada.

  39. 5 Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.

  40. 10 Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”

  41. 4 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni;

    rigyawan hallaka sun sha kaina.

    5 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni;

    tarkon mutuwa ya yi mini arangama.

    6 Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;

    Na yi kuka ga Allahna don taimako.

    A Haikalinsa ya ji muryata,

    Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

  42. 7 Ina zan tafi daga Ruhunka?

    Ina zan gudu in tafi daga gabanka?

    8 In na haura zuwa sammai, kana a can;

    in na yi gado a zurfafa, kana a can.

    9 In na tashi a fikafikan safiya,

    in na sauka a gefe mai nisa na teku,

    10 can ma hannunka zai bishe ni,

    hannunka na dama zai riƙe ni gam.

  43. 35 Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a.

  44. 3 Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, 4 wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. 5 Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. 6 In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha.

  45. 15 Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace. 16 Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.

  46. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Ka umarci Isra’ilawa su kori duk wanda yake da ciwon fatan jiki, ko mai ɗiga na kowane iri, ko wanda ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, daga cikin sansani. 3 Ka kori maza da mata ma; ka kai su bayan sansani domin kada su ƙazantar da sansani inda nake zama a cikinsu.”

  47. 5 Da Shawulu ya ga sojojin Filistiyawa sai ya ji tsoro, ya firgita ƙwarai. 6 Ya nemi nufin Ubangiji amma bai sami amsa daga wurin Ubangiji ko ta wurin mafarki, ko ta wurin Urim, ko ta wurin annabawa ba. 7 Shawulu ya ce wa fadawansa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”

    Suka ce, “Akwai guda a En Dor.”

  48. 7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara;

    ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

    8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana.

    Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

    9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;

    jikina kuma zai zauna lafiya,

    10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,

    ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

    11 Ka sanar da ni hanyar rai;

    za ka cika ni da farin ciki a gabanka,

    da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

  49. 6 Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba,

    wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.

    7 Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a;

    suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,

    8 “Ya dogara ga Ubangiji;

    bari Ubangiji yă cece shi.

    Bari yă cece shi,

    da yake yana jin daɗinsa.”

    9 Duk da haka ka fitar da ni daga ciki;

    ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.

    10 Daga haihuwa an jefa ni a kanka;

    daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.

    11 Kada ka yi nesa da ni,

    gama wahala na kusa

    kuma babu wani da zai taimaka.

  50. 5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da kuma Allahna.

  51. 11 “Amma mutanena ba su saurare ni ba;

    Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

    12 Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare

    don su bi dabararsu.

  52. 10 Kaitona, mahaifiyata, da kika haife ni,

    mutumin da dukan ƙasa take faɗa take kuma gardama da shi!

    Ban ba da bashi ko in ci bashi ba,

    duk da haka kowa yana zagina.

  53. 1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.

  54. 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

  55. 8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. 9 Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. 10 Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,

  56. 22 Saboda suna mai girma da Ubangiji yake da shi, ba zai taɓa ƙin mutanensa ba. Gama Ubangiji ya ji daɗi da ya yi ku mutanensa.

  57. 17 Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne. 18 Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba.

  58. 16 Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada.

    Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani.

  59. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

    1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

    kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

  60. 11 Yesu ya ci gaba da cewa, “Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. 12 Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.

    13 “Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. 14 Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. 15 Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu. 16 Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.

    17 “Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 19 Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’ 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

    “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

    21 “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

    22 “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa. 23 Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali. 24 Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.

    25 “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa. 26 Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa. 27 Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’

    28 “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi. 29 Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba. 30 Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’

    31 “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne. 32 Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”

  61. 5 Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. 6 Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”

    7 Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”

    8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” 9 Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.

    A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,

  62. 1 “Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2 A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri. 3 In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake. 4 Ai, kun san hanyar zuwa inda za ni.”

  63. 1 ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. 2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. 3 In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. 4 Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, 5 gama kowa zai ɗauki kayansa.

  64. 19 Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. 20 Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. 21 Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. 22 Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.

  65. 8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

  66. 10 Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. 11 Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12 In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”

  67. 21 Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.

  68. Zabura ta Dawuda.

    1 Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

    2 Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,

    yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,

  69. 9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa;

    idanuna sun gaji da baƙin ciki,

    raina da jikina sun tafke tilis.

    10 Baƙin ciki ya rufe raina

    shekaruna sun cika da nishi;

    ƙarfina ya karai saboda azaba,

    ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis.

    11 Saboda dukan abokan gābana,

    Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana;

    na zama abin tsoro ga abokaina,

    waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni.

    12 An manta da ni sai ka ce na mutu;

    na zama kamar fasasshen kasko.

  70. 5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

    Me ya sa ka damu a cikina?

    Ka dogara ga Allah,

    gama zai sāke yabe shi,

    Mai Cetona da Allahna.

  71. 18 Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni;

    duhu ne abokina na kurkusa.

  72. 10 Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba;

    ban hana zuciyata wani jin daɗi ba.

    Zuciyata ta yi murna da dukan aikina,

    wannan kuwa shi ne ladan dukan famata.

    11 Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana,

    da abin da na yi fama don in samu,

    sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai;

    babu wata riba a duniya.

  73. 18 “Halinki da ayyukanki

    sun kawo wannan a kanki.

    Hukuncinki ke nan.

    Yana da ɗaci!

    Ya soke ki har zuciyarki!”

    19 Azabana, azabana!

    Ina birgima cikin zafi.

    Azabana, azabar zuciyata!

    Zuciyata yana bugu a cikina,

    Ba zan yi shiru ba.

    Gama na ji karan ƙaho;

    na ji kirarin yaƙi.

  74. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.

  75. 75 Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.

  76. 13 Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14 Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15 Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.

  77. 24 Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25 Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.