25 Bible Verses About Abortion

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Abortion
  1. 13 Gama ka halicci ciki-cikina;

    ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

    14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

    ayyukanka suna da banmamaki,

    na san da haka sosai.

    15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba

    sa’ad da aka yi ni asirce.

    Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

    16 Idanunka sun ga jikina marar fasali;

    dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

    kafin ɗayansu yă kasance.

  2. 22 “Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. 23 Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai, 24 ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa, 25 ƙuna don ƙuna, rauni don rauni, ƙujewa don ƙujewa.

  3. 4 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

    5 “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,

    kafin a haife ka, na keɓe ka;

    na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”

  4. 21 Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki. 22 Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji.

    23 Ubangiji ya ce mata,

    “Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki

    mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna,

    ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi,

    babban kuma zai bauta wa ƙaramin.”

    24 Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga ’yan biyu maza a mahaifarta. 25 Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa. 26 Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.

  5. 39 A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya, 40 inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet. 41 Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. 42 Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! 43 Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? 44 Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna. 45 Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

  6. 13 Ba za ka yi kisankai ba.

  7. 27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

    Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

    Miji da mace ya halicce su.

  8. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

    yara lada ne daga gare shi.

    4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

    haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

    5 Mai albarka ne mutumin

    da korinsa sun cika da su.

    Ba za a kunyata su ba

    sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

  9. 7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

  10. 3 Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.

    4 “Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna. 5 Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.

    6 “Duk wanda ya zub da jinin mutum,

    ta hannun mutum za a zub da jininsa;

    gama a cikin siffar Allah ne,

    Allah ya yi mutum.

  11. 15 Sai Sarkin Masar ya gaya wa ungozomomin matan Ibraniyawa, wato, su Shofra da Fuwa ya ce, 16 “Sa’ad da kuke taimakon matan Ibraniyawa lokacin haihuwa, in jaririn namiji ne ku kashe shi, amma in ta mace ce, ku bar ta da rai.” 17 Amma ungozomomin nan masu tsoron Allah ne, ba su kuwa aikata abin da sarkin Masar ya gaya musu ba; suka bar jarirai maza su rayu. 18 Sai sarkin Masar ya kira ungozomomin, ya tambaye su ya ce, “Don me kuka yi haka? Don me kuka bar jarirai maza su rayu?”

    19 Ungozoman suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Ai, matan Ibraniyawa ba kamar matan Masarawa ba ne, gwarzaye ne, sukan haihu kafin ungozomomin su kai wurinsu.”

    20 Saboda haka Allah ya nuna alheri wa ungozomomin, Isra’ilawa kuwa suka yi yawa fiye da dā. 21 Saboda ungozomomin suna tsoron Allah, sai Allah ya ba su iyalan kansu.

  12. 31 Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. 32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, 33 zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”

  13. 13 “In da na danne wa bayina maza da mata hakkinsu,

    sa’ad da suke da damuwa da ni,

    14 me zan yi lokacin da Allah ya tuhume ni?

    Me zan ce lokacin da ya tambaye ni?

    15 Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba?

    Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?

  14. 3 “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub,

    dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila,

    ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku,

    na kuma riƙe ku tun haihuwarku.

    4 Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura

    ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku.

    Na yi ku zan kuma riƙe ku;

    zan lura da ku

    in kuma kuɓutar da ku.

  15. 1 Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai;

    ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa.

    Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni;

    tun daga haihuwata ya ambaci sunana.

    2 Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi,

    cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni;

    ya sa na zama kamar kibiya mai tsini

    ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.

    3 Ya ce mini, “Kai bawana ne,

    Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”

  16. 13 Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna. 14 Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa, 15 gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  17. 10 Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. 11 Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka.

  18. 3 Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa. 4 To, sai ki lura kada ki sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye, kada kuma ki ci wani abu marar tsarki, 5 gama za ki yi ciki, ki haifi ɗa. Aska ba za tă taɓa kansa ba, domin yaron zai zama Banazare, keɓaɓɓe ga Allah tun daga haihuwa, shi ne kuwa zai soma ceton Isra’ilawa daga hannuwan Filistiyawa.”

  19. 37 Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya

    ’yan matansu kuma ga aljanu.

    38 Suka zub da jini marar laifi,

    jinin ’ya’yansu maza da mata,

    waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana,

    ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.

    39 Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi;

    ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.

  20. 5 Yanzu fa Ubangiji ya ce

    ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa

    don in dawo da Yaƙub gare shi

    in kuma tattara Isra’ila gare shi,

    gama an girmama ni a gaban Ubangiji

    Allahna kuma ne ƙarfina

  21. 13 Ga abin da Ubangiji ya ce,

    “Saboda zunubai uku na Ammon,

    har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.

    Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu

    don kawai yă ƙwace ƙasar.

  22. י Yod

    73 Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni;

    ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.

  23. 8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

  24. 11 Ka rufe ni da tsoka da fata,

    ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?

    12 Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri,

    kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.

  25. 1 “Amma yanzu ka saurara, ya Yaƙub, bawana,

    Isra’ila, wanda zaɓa.

    2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa,

    wanda kuma zai taimake ka.

    Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana,

    Yeshurun, wanda na zaɓa.