98 Bible Verses About Animals
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. 25 Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. 30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
-
5 Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
6 Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago
damisa za tă kwanta tare da akuya,
ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;
ɗan yaro ne zai lura da su.
7 Saniya da beyar za su yi kiwo tare,
ƙananansu za su kwanta tare,
zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.
8 Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,
ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.
9 Ba za su yi lahani ko su hallaka
wani a dutsena mai tsarki ba,
gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji
kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
-
1 Sa’an nan Allah ya sa wa Nuhu da ’ya’yansa maza albarka, yana ce musu, “Ku haifi ’ya’ya, ku ƙaru, ku kuma cika duniya. 2 Dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifayen teku, za su riƙa jin tsoronku, suna fargaba. An sa su a cikin hannuwanku. 3 Kome da yake da rai wanda yake tafiya, zai zama abincinku. Kamar yadda na ba ku kowane irin ganye, haka na ba ku kome da kome.
4 “Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, wato, nama wanda jininsa yake cikinsa tukuna.
-
3 Kada ku ci wani haramtaccen abu. 4 Waɗannan su ne dabbobin da za ku iya ci, saniya, tunkiya, akuya, 5 mariri, barewa, mariya, makwarna, mazo, gada da kuma tunkiyar dutse. 6 Za ku iya cin duk dabbar da take da rababben kofato, wadda kuma take sāke tona abin da suka riga suka haɗiye. 7 Amma, cikin waɗanda suke sāke tona abin da suka riga suka haɗiye ɗin, ko suke da rababben kofato, ba za ku ci raƙumi, zomo ko rema ba. Ko da yake suna sāke tona abin da suka riga suka haɗiye, suna kuma da rababben kofato, su ɗin marar tsarki ne gare ku. 8 Alade ma marar tsarki ne; ko da yake yana da rababben kofato, shi ba ya sāke tona abin da ya riga ya haɗiye. Ba za ku ci namansu ko ku taɓa gawarsu ba.
-
18 Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba. 19 Ƙaddarar mutum ɗaya take da ta dabba; ƙaddara ɗaya ce take jiransu biyu. Yadda ɗayan yake mutuwa, haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne; mutum bai fi dabba ba. Kowane abu ba shi da amfani. 20 Duka wuri ɗaya za su tafi; gama duka daga turɓaya suka fito, kuma ga turɓaya duka za su koma. 21 Wa ya tabbatar cewa ruhun mutum yakan tashi sama sa’an nan na dabba yă sauka ƙasa?”
-
10 Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa,
amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
-
7 “Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka,
ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
8 Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka,
ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
9 Wane ne cikin waɗannan bai san
cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
10 Ran kowace halitta yana a hannunsa,
haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
11 Ko kunne ba ya gwada kalmomi
kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
12 Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba?
Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
-
19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu?
-
20 Ka yi duhu, sai ya zama dare,
sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.
21 Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta
suna kuma neman abincinsu daga Allah.
22 Rana ta fito, sai suka koma shiru;
suka koma suka kwanta a kogwanninsu.
23 Mutum yakan tafi aikinsa,
zuwa wurin aikinsa har yamma.
24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!
Cikin hikima ka yi su duka;
duniya ta cika da halittunka.
25 Akwai teku, babba da kuma fāɗi,
cike da halittun da suka wuce ƙirga,
abubuwa masu rai babba da ƙarami.
26 A can jiragen ruwa suna kai komo,
kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.
27 Waɗannan duka suna dogara gare ka
don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.
28 Sa’ad da ba su da shi,
sai su tattara shi;
sa’ad da ka buɗe hannunka,
sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.
29 Sa’ad da ka ɓoye fuskarka,
sai su razana;
sa’ad da ka ɗauke numfashinsu,
sai su mutu su kuma koma ga ƙura.
30 Sa’ad da ka aika da Ruhunka,
sai su halittu,
su kuma sabunta fuskar duniya.
-
4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,
ɗan mutum da kake lura da shi?
5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah
ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
6 Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;
ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
7 dukan shanu da tumaki,
da kuma namun jeji,
8 tsuntsayen sararin sama
da kifin teku,
da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9 Ya Ubangiji, shugabanmu,
sunanka da girma take a cikin dukan duniya!
-
15 Sa’an nan Allah ya ce wa Nuhu, 16 “Fito daga jirgin, kai da matarka da ’ya’yanka maza da matansu. 17 Ka fitar da kowane iri halitta mai rai da take tare da kai waje, tsuntsaye, dabbobi, da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, don su yi ta haihuwa, su yi yawa, su ƙaru a duniya.”
18 Sai Nuhu ya fito tare da matarsa da ’ya’yansa maza da matan ’ya’yansa, 19 da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abu da yake tafiya a bisa duniya, suka fito daga jirgi daki-daki bisa ga irinsu.
20 Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. 21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.
22 “Muddin duniya tana nan,
lokacin shuki da na girbi,
lokacin sanyi da na zafi,
lokacin damina da na rani,
dare da rana
ba za su daina ba.”
-
18 Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.
Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
-
1 Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 2 “Ku ce wa Isra’ilawa, ‘Cikin dabbobin da suke a doron ƙasa, waɗannan ne za ku ci. 3 Za ku iya cin dabbobin da suke da rababben kofato, waɗanda suke kuma tuƙa.
4 “ ‘Akwai waɗanda suke tuƙa ko kuwa suna da rababben kofato kawai, duk da haka ba za ku ci su ba. Waɗannan kuwa su ne, raƙumi, ko da yake yana tuƙa, amma ba shi da rababben kofato; saboda haka cin namansa haram ne gare ku. 5 Rema, ko da yake tana tuƙa, duk da haka ba ta da rababben kofato; saboda haka namanta haram ne gare ku. 6 Zomo, ko da yake yana tuƙa, duk da haka ba shi da rababben kofato; saboda haka namansa haram ne gare ku. 7 Alade, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa, saboda haka namansa haram ne gare ku. 8 Ba za ku ci namansu ba, ko ku taɓa gawawwakinsu, gama haram ne gare ku.
9 “ ‘Cikin dukan halittu masu rai da suke a cikin ruwan tekuna da rafuffuka, za ku iya cin kowane da yake da ƙege da kamɓori. 10 Amma kowace halittar da take cikin tekuna da koguna da ba ta da ƙege da kamɓori, ko cikin dukan abubuwa masu rai a ruwa ko kuma sauran halittu a cikin ruwa za ku ɗauka su marasa tsaki ne gare ku. 11 Da yake abubuwan ƙyama ne a gare ku, ba za ku ci namansu ba, kuma dole ku yi ƙyamar gawawwakinsu. 12 Duk abin da yake a ruwa amma ba shi da ƙege ko kamɓori, za ku yi ƙyamarsa.
13 “ ‘Waɗannan su ne tsuntsayen da za ku yi ƙyamarsu, ba za ku ci su ba domin sun zama abin ƙyama. Tsuntsayen kuwa su ne, gaggafa, ungulu, baƙin ungulu, 14 shirwa, da duk wani irin baƙin shirwa, 15 kowane irin hankaka, 16 mujiya mai ƙaho, jimina, shaho, da kowane irin shaho, 17 ƙaramin ƙururu, babba da jaka, zalɓe, 18 kazar ruwa, kwasakwasa, da ungulu, 19 shamuwa, kowane irin jinjimi, katutu da kuma jamage.
20 “ ‘Dukan ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu abin ƙyama ne gare ku. 21 Sai dai akwai ƙwarin da suke da fikafikai masu tafiya da ƙafafu huɗu da za ku ci; waɗanda suke da cinyoyin da suke sa su iya tsalle. 22 Za ku iya cin kowane irin fāra, gyare, ƙwanso da danginsu. 23 Amma sauran ƙananan ƙwari duka masu fikafikai, suna kuma jan ciki, abin ƙyama ne a gare ku.
24 “ ‘Duk wanda ya taɓa mushen waɗannan dabbobi, zai ƙazantu har fāɗuwar rana. 25 Duk wanda ya ɗauki ɗaya daga cikin gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har zuwa yamma.
26 “ ‘Kowace dabbar da ba ta da rababben kofato ko ba ta tuƙa, haram ce gare ku; duk wanda ya taɓa gawarsu zai ƙazantu. 27 Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma. 28 Duk wanda ya ɗauki gawawwakinsu dole yă wanke rigunansa, zai kuma ƙazantu har yamma. Waɗannan dabbobi za su zama marasa tsabta a gare ku.
29 “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa, 30 da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo. 31 Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma. 32 Duk abin da mushensu ya fāɗa a kai, zai ƙazantu. Ko a kan itace ne, ko a bisa tufafi, ko a fata, ko a buhu, ko cikin kowane irin abu da ake amfani da shi, to, tilas a sa shi cikin ruwa, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma, sa’an nan zai tsarkaka. 33 In waninsu ya fāɗi a cikin tukunyar laka, kome da yake a tukunyar zai ƙazantu, kuma dole a fashe tukunyar. 34 Duk abincin da aka yarda a ci, wanda ya taɓa ruwa daga irin tukunyan nan zai zama marar tsabta, kuma duk ruwan da za a sha daga irin tukunyan nan ƙazantacce ne. 35 Kowane irin abu da mushensu ya fāɗa a kai ya ƙazantu ke nan; ko a kan murhu, ko a tukunyar dahuwa, dole a farfashe su. Su haramtattu ne kuma dole ku ɗauke su haramtattu. 36 Maɓuɓɓuga ko tafki na tarin ruwa zai ci gaba da zauna mai tsabta, amma duk wanda ya taɓa ɗaya daga cikin waɗannan gawawwakin ya haramtu. 37 In gawa ta fāɗi a irin da za a shuka, irin zai ci gaba da zama mai tsabta. 38 Amma in an sa ruwa a irin sai kuma gawar ta fāɗi a kai, to, irin ya zama haram gare ku.
39 “ ‘In dabbar aka yarda a ci ta mutu, duk wanda ya taɓa gawarta zai ƙazantu har yamma. 40 Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.
41 “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba. 42 Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne. 43 Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu. 44 Ni ne Ubangiji Allahnku; ku tsarkake kanku ku kuma zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani halittar da take rarrafe a ƙasa. 45 Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku; saboda haka ku zama da tsarki, domin Ni mai tsarki ne.
46 “ ‘Waɗannan ne ƙa’idodi game da dabbobi, tsuntsaye, da kowane abu mai rai da yake motsi a cikin ruwa, da kowace halitta mai rarrafe a ƙasa.
-
34 Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita. 35 Nakan bi ta a baya in buga ta in kuma ƙwato tunkiyar daga bakinta. In kuma ta taso mini, nakan cafke ta a gashinta in buga ta in kashe. 36 Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.
-
1 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Nuhu. “Shiga jirgin, kai da dukan iyalinka, gama na ga kai mai adalci ne a wannan zamani. 2 Ka ɗauki bakwai na kowace iri tsabtaccen dabba tare da kai, namiji da ta mace, da kuma biyu na kowace dabba marar tsabta, namiji da ta mace, 3 da kuma bakwai na kowane iri tsuntsu, namiji da ta mace, domin a bar kowane irinsu da rai a dukan duniya.
-
9 Ba na bukatan bijimi daga turkenku
ko awaki daga garkunanku,
10 gama kowace dabbar kurmi nawa ne,
da kuma shanu a kan dubban tuddai.
11 Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu
kuma halittun filaye nawa ne.
12 Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba,
gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.
-
25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?
-
8 Sai Allah ya ce wa Nuhu da ’ya’yansa, 9 “Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku, 10 da kowace halitta mai rai wadda ta kasance tare da kai; wato, tsuntsaye da dabbobin gida da kuma dukan namun jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin; wato, kowane mai rai na duniya. 11 Na kafa alkawarina da ku, ba za a ƙara hallaka dukan rayuka da ambaliyar ruwa ba; ba za a ƙara yin ambaliya don a hallaka duniya ba.”
12 Allah ya kuma ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na yi tsakanina da ku, da kowace halitta tare da ku; alkawari na dukan zamanai masu zuwa. 13 Na sa bakan gizona cikin gizagizai, shi ne kuwa zai zama alamar alkawari tsakanina da duniya. 14 Duk sa’ad da na kawo gizagizai a bisa duniya, bakan gizo kuma ya bayyana a ciki gizagizan, 15 zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. 16 Duk sa’ad da bakan gizo ya bayyana cikin gizagizan, zan gan shi in kuma tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da dukan halittu masu rai, na kowane iri a duniya.”
17 Saboda haka Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawarin da na kafa tsakanina da dukan masu rai a duniya.”
-
18 Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai. 19 Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi; 20 karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa. 21 Duk wanda ya kashe dabba, dole yă biya, amma duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
-
4 Kada ku yi wa saniya takunkumi sa’ad da take tattaka hatsi.
-
29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
-
7 Kowace irin dabba, tsuntsu, masu ja da ciki da kuma halittun da suke cikin teku an sarrafa su kuma mutum ne ya sarrafa, 8 amma ba mutumin da zai iya ya sarrafa harshe. Mugu ne marar hutu, cike da dafi mai kisa.
-
6 Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi.
A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. 8 Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
“ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki
shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’
wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”
9 Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, 10 sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,
11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,
ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,
domin ka halicci dukan abubuwa,
kuma ta wurin nufinka aka halicce su
suka kuma kasance.”
-
7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
-
7 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
-
17 Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka. 18 Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da ’ya’yanka maza da matarka da matan ’ya’yanka tare da kai. 19 Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai. 20 Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai. 21 Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
22 Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.
-
7 Yabi Ubangiji daga duniya,
ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,
hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
9 ku duwatsu da dukan tuddai,
itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,
10 namun jeji da dukan dabbobin gida,
ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
11 sarakunan duniya da dukan al’ummai,
ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
12 samari da ’yan mata,
tsofaffi da yara.
-
25 Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare,
zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi,
amma ƙura ce za tă zama abincin maciji.
Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna
a kan dukan dutsena mai tsarki ba,”
in ji Ubangiji.
-
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
-
12 “Kwana shida za ku yi aikinku, amma a rana ta bakwai, kada ku yi aiki, saboda saniyarku da jakinku su huta, haka kuma bawan da aka haifa a gidanku, da kuma baƙon da yake a cikinku yă wartsake.
-
21 Amma halittun hamada za su kwanta a can,
diloli za su cika gidajenta;
a can mujiyoyi za su zauna,
a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
22 Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta,
diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma.
Lokacinta ya yi kusa,
kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.
-
5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa. 6 Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba. 7 Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.
-
8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. 9 Suka rera sabuwar waƙa,
“Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin
ka kuma buɗe hatimansa,
domin an kashe ka,
da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah,
daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
10 Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima,
kuma za su yi mulki a duniya.”
11 Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. 12 Da babbar murya suka rera,
“Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe,
don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi
da girma da ɗaukaka da kuma yabo!”
13 Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,
“Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon
yabo da girma da ɗaukaka da iko,
sun tabbata har abada abadin!”
-
15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.
-
12 Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama;
shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
-
23 Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka,
ka mai da hankali ga garken shanunka;
-
22 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa. 23 Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!
-
9 Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a. 10 Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa. 11 Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu. 12 Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama. 13 Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”
14 Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”
15 Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”
-
15 Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi.
-
20 Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin. 21 Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane. 22 Kome a busasshiyar ƙasa da yake numfashi a hancinsa ya mutu. 23 Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.
-
8 Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9 Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10 amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.
-
1 “ ‘In hadayar wani mutum, hadaya ta salama ce, ya kuma miƙa ’yar dabba daga garke, ko namiji ko ta mace ce, sai yă miƙa dabbar da ba ta da lahani a gaban Ubangiji.
-
28 Ubangiji ya buɗe bakin jakar, sai jakar ta ce wa Bala’am, “Me na yi maka da ka buge ni har sau uku?”
29 Bala’am ya ce wa jakar “Domin kin wulaƙanta ni! Da a ce ina da takobi a hannuna da zan kashe ki nan take.”
30 Jakar ta ce wa Bala’am, “Ni ba jakarka ba ce wadda kake hawa kullum, har yă zuwa yau? Na taɓa yin maka haka?”
Bala’am ya ce, “A’a.”
-
15 Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka
da kuma baye-baye na raguna;
zan miƙa bijimai da awaki. Sela
-
6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
7 Ba shi da jagora
ba shugaba ko mai mulki,
8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
Yaushe za ku farka daga barcinku?
10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
rashi kuma kamar ɗan fashi.
-
8 Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji Ubangiji Maɗaukaki.
-
2 Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki.
-
4 Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. 5 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”
6 Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.
-
15 Sa’ad da Fir’auna ya taurare zuciyarsa, bai yarda ya sallame mu ba, sai Ubangiji ya kashe dukan ’ya’yan farin ƙasar Masar, na mutum da na dabba, gaba ɗaya. Domin haka nake yin hadaya ga Ubangiji da ’ya’yan fari, maza, da suka fara buɗe mahaifa, amma nakan fanshi dukan ’ya’yan farina maza.’
-
19 “Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi.
-
9 “ ‘In abin da ya yi alkawarin yardajje ne a matsayin hadaya ga Ubangiji, wannan dabbar da aka bayar ga Ubangiji, za tă zama mai tsarki. 10 Kada yă yi musayarta ko yă yi musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau; in lalle ne yă yi musayar dabbar da wata, to, duk wannan da kuma wanda zai yi musayar da ita za su zama masu tsarki. 11 In abin da ya yi alkawari dabba ce marar tsarki, wadda ba yardajje ba ce, a matsayin hadaya ga Ubangiji, dole a kai dabbar wa firist, 12 wanda zai yanke hukunci dacewarta, ko mai kyau ce, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama. 13 In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.
-
15 Kowane haihuwar fari, ta mutum, ko ta dabba da suka miƙa wa Ubangiji, naka ne. Amma ka fanshi kowace haihuwar fari ta mutum, ko ta dabbar da take haram.
-
6 In kuka ga gidan tsuntsu kusa da hanya, ko a kan itace, ko kuma a ƙasa, mahaifiyar tsuntsun kuwa tana kwance a kan ’ya’yanta, ko kuwa a kan ƙwanta, kada ku kama mahaifiyar duk da ’ya’yan. 7 Za ku iya kwashe ’ya’yan, amma ku tabbata kun bar mahaifiyar tă tafi. Yin haka zai sa ku sami zaman lafiya da tsawon rai.
-
17 Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa
haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
-
24 “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana,
duk da haka suna da hikima ƙwarai.
25 Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai,
duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;
26 remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai,
duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;
27 fāra ba su da sarki,
duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;
28 ana iya kama ƙadangare da hannu,
duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.
-
6 Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa,
Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari
inda zakoki da zakanya,
inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke,
jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna,
dukiyarsu a kan raƙuma,
zuwa ƙasan nan marar riba,
-
31 Firistoci ba za su ci mushen tsuntsu ko na dabba ba, ba kuwa za su ci waɗanda namun jeji suka kashe ba.
-
6 Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama.
-
20 In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. 21 Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su. 22 A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”
-
1 Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” 2 Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila.
Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. 3 Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. 4 Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, 5 amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.
-
9 Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”
-
15 Amma kwa iya yanka nama ku ci a garuruwanku, a duk lokacin da ranku yake so, kamar yadda ake yi da gada ko barewa, bisa ga albarkar da Ubangiji Allahnku yake sa muku. Marar tsarki da mai tsarki, duka za ku iya ci. 16 Amma kada ku ci jini, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.
-
43 Ya ce masa, “Kana tsammani ni kare ne da za ka zo mini da sanda?” Sai ya la’anci Dawuda da sunayen allolin Filistiyawa.
-
1 Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. 2 Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, 3 amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi.
4 “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”
5 Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! 6 Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”
7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu.
-
6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji.
Yabi Ubangiji.
-
14 Halittun hamada za su sadu da kuraye,
awakin jeji za su yi ta kiran juna;
a can halittun dare su ma za su huta
su kuma nemi wurin hutu wa kansu.
-
17 “Ga shi, na halicci
sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.
Abubuwa na dā za a manta da su,
ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
-
7 Saboda haka zan hau kansu kamar zaki,
zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
8 Kamar beyar da aka ƙwace mata ’ya’yanta,
zan fāɗa musu in ɓarke su.
Kamar zaki zan cinye su;
kamar naman jeji zan yayyage su.
-
20 Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
-
33 “In mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai kuma rufe ba, sai saniya ko jaki ya fāɗi a ciki, 34 Mai ramin zai biya rashin da aka yi wa mai shi, matacciyar saniyan ko jakin, zai zama na mai ramin.
35 “In bijimin mutum ya raunana bijimin wani, har ya mutu, sai mutanen biyu su sayar da mai ran, su raba kuɗin daidai, haka ma su yi da mai ran. 36 Amma fa, in tun can, an san bijimin yana da wannan halin faɗa, duk da haka mai shi bai ɗaura shi ba, dole mai shi yă biya, dabba domin dabba, matacciyar dabbar kuwa tă zama nasa.
-
4 “In ka ga saniyar abokin gābanka, ko jakinsa ya ɓace, ka yi ƙoƙari ka mai da shi wurinsa. 5 In ka ga jakin wani maƙiyinka ya fāɗi a ƙarƙashin kayan da ya ɗauka, kada ka bar shi can, ka yi ƙoƙari ka taimake shi.
-
19 “ ‘Ku kiyaye farillaina.
“ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara.
“ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku.
“ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
-
8 Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;
Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
9 Kada ka zama kamar doki ko doki,
wanda ba su da azanci
wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama
in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
10 Azaban mugu da yawa suke,
amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa
kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.
11 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;
ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!
-
10 Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka;
yana gudu tsakanin duwatsu.
11 Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji;
jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.
12 Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan;
suna rera cikin rassa.
13 Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama;
ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.
-
30 Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi,
waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.
-
15 Idanun kowa yana dogara gare ka,
kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
16 Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
-
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya;
ku kada garaya ga Allahnmu.
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai;
yana tanada wa duniya ruwan sama
yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
9 Yakan tanada wa shanu abinci
da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
-
4 Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiya
ciyawar kowane fili ta bushe?
Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne,
dabbobi da tsuntsaye sun hallaka.
Ban da haka ma, mutane suna cewa,
“Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”
-
18 Ji yadda dabbobi suke nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
saboda ba su da ciyawa,
har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19 A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,
gama wuta ta cinye wurin kiwo
harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20 Har ma namun jeji suna haki gare ka;
rafuffuka sun bushe
wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.
-
2 “Zan hallaka kome
a fuskar duniya,”
in ji Ubangiji.
3 “Zan hallaka mutane da dabbobi;
zan kuma hallaka tsuntsayen sama
da kifayen teku,
da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.”
“Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,”
in ji Ubangiji.
-
1 Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2 yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3 In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”
4 Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
5 “Ku ce wa Diyar Sihiyona,
‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,
mai tawali’u yana a kan jaki,
a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”
-
13 ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.
-
5 Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?”
-
9 Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka? 10 Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin.
-
39 Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.
-
9 Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,
ka dawo daga farauta, ɗana.
Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,
kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
10 Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,
ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,
sai ya zo ga wanda yake mai shi.
Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
11 Zai daure jakinsa a kuringa,
aholakinsa a rassa mafi kyau;
zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi
rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
12 Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,
haƙorarsa farare kamar madara.
13 “Zebulun zai zauna a bakin teku,
yă zama tasar jiragen ruwa;
iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
14 “Issakar doki mai ƙarfi,
kwance tsakanin buhunan sirdi.
-
4 Amma Ubangiji zai raba tsakanin dabbobin Isra’ila da na Masar, saboda kada wata dabbar Isra’ilawa ta mutu.’ ”
5 Sai Ubangiji ya sa lokaci ya ce, “Gobe Ubangiji zai yi wannan a ƙasar.” 6 Kashegari Ubangiji ya yi haka. Dukan dabbobin Masarawa suka mutu, amma babu dabba guda ta Isra’ilawan da ta mutu.
-
2 “ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi.
-
25 “ ‘Saboda haka sai ku bambanta tsakanin dabbobi masu tsarki da marasa tsarki, da kuma tsakanin tsuntsaye masu tsarki da marasa tsarki. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wata dabba, ko tsuntsu, ko wani abin da yake rarrafe a ƙasa, waɗanda na keɓe a matsayi marasa tsarki a gare ku. 26 Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.
-
21 “ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku. 22 Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku.
-
15 Kama mana ɓeraye,
ƙananan ɓerayen
da suke lalatar da gonakin inabi,
gonakin inabinmu da suke cikin yin fure.
-
3 Amma duk ya miƙa hadayar bijimi
yana kama da wanda ya kashe mutum,
kuma duk wanda ya miƙa ɗan rago,
kamar wanda ya karye wuyan kare;
duk wanda ya miƙa hadaya ta gari
yana kama da wanda ya yi sadakar jinin alade,
kuma duk wanda ya ƙone turaren tuni,
kamar wanda yake bauta gunki ne.
Sun zaɓi hanyoyinsu,
rayukansu kuma suna jin daɗin abubuwan banƙyamarsu;
-
7 Ko shamuwa ta sararin sama ma
takan san lokutan da aka tsara mata,
kurciya, mashirare da kuma zalɓe
sukan lura da lokacin ƙauransu.
Amma mutanena ba su san
abubuwan da Ubangiji yake bukata ba.
-
5 Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
-
11 Zan sa mutane da dabbobi su yi yawa a kanku, za su kuma ba da ’ya’ya su kuma yi yawa. Zan zaunar da mutane a kanku kamar dā zan kuma sa ku wadaita fiye da dā. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
-
22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,
gama wuraren kiwo sun yi kore shar.
Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;
itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
-
15 Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani.
-
12 Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.
13 Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku. 14 Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri! 15 Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta. 16 Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.
Shows Read in context, Share and Copy.