69 Bible Verses About Harvest
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
35 Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. 37 Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38 Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”
-
34 Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa. 35 Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi. 36 Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare. 37 Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’ 38 Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
-
7 Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. 8 Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. 9 Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. 10 Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.
-
18 “Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar.
19 “Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. 20 Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza.
“Kada wani yă zo gabana hannu wofi.
21 “Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta.
22 “Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara.
-
9 Ubangiji ya ce wa Musa, 10 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, kuka kuma girbe amfanin gonarta, sai ku kawo wa firist damin hatsi na farko da kuka girbe.
-
13 Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.”
“I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
14 Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” 16 Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
17 Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. 18 Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” 19 Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. 20 Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.
-
22 “Muddin duniya tana nan,
lokacin shuki da na girbi,
lokacin sanyi da na zafi,
lokacin damina da na rani,
dare da rana
ba za su daina ba.”
-
5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima,
amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
-
3 Ka fadada al’umma
ka kuma ƙara farin cikinsu;
suna farin ciki a gabanka
yadda mutane sukan yi murna a lokacin girbi,
kamar yadda mutane sukan yi farin ciki
sa’ad da suke raba ganima.
-
24 Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu,
wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara,
wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’
-
36 Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”
37 Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum. 38 Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan, 39 abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.
40 “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.
-
2 Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa. 3 Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai. 4 Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.
-
9 “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. 10 Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
-
17 Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.
18 Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.
-
12 “Bari a tā da dukan al’ummai;
bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat
gama a can zan zauna
in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.
13 Ku fito da lauje,
gama girbi ya nuna.
Ku zo, ku tattaka inabin,
gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika
randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba,
muguntarsu da girma take!”
-
30 Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”
-
10 Kun manta da Allah Mai Cetonku;
ba ku tuna da Dutse, kagararku ba.
Saboda haka, ko da yake kun fita ku shuka tsire-tsire mafi kyau
kuka kuma shuka inabin da aka sayo daga waje,
11 ko da yake a ranar kun shuka su, kuka sa su yi girma,
da safe kuma sa’ad da kuka shuka su, kuka sa suka yi toho suka yi fure,
duk da haka girbin ba zai zama kome ba
a ranar cuta da zafin da ba ta da magani.
-
7 “Na kuma hana muku ruwan sama
tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi.
Na sa aka yi ruwan sama a wani gari,
sai na hana a yi a wani gari.
Wata gona ta sami ruwan sama;
wata gona kuma ta bushe.
-
19 Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku. 20 Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa. 21 Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.
-
4 Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,
“Zan yi shiru in kuma duba a hankali daga mazaunina,
kamar ƙuna mai zafi a hasken rana,
kamar girgijen raba a lokacin girbi.”
5 Gama kafin girbi, sa’ad da furanni suka karkaɗe
furanni kuma suka zama ’ya’yan inabin da suka nuna,
zai faffalle rassan kuringar inabi da wuƙa,
ya yanke ya kuma kwashe rassan da suka bazu.
-
26 Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona. 27 A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba. 28 Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya. 29 Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”
-
5 Waɗanda suka yi shuka da hawaye
za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.
6 Shi da ya fita yana kuka,
riƙe da iri don shuki,
zai dawo da waƙoƙin farin ciki,
ɗauke da dammuna.
-
1 Ubangiji ya yi magana da Musa a kan Dutsen Sinai ya ce, 2 “Yi wa Isra’ilawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da zan ba ku, dole ƙasar kanta ta kiyaye Asabbaci ga Ubangiji. 3 Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. 4 Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. 5 Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu. 6 Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba, 7 haka ma zai zama abinci domin dabbobinku, da kuma namun jeji a ƙasarku. Duk abin da ƙasar ta bayar za a ci.
-
1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,
haka girmamawa bai dace da wawa ba.
-
33 Ni Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila na ce,
“’Yar Babilon kamar daɓen masussuka
a lokacin da ake sussuka,
ba da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.”
-
22 “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”
-
9 Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka,
saboda inabin Sibma.
Ya Heshbon, ya Eleyale,
na cika ku da hawaye!
Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna
da kuma girbinku sun ɓace.
-
11 “Ku kuma, ya mutanen Yahuda,
na shirya muku ranar girbi.
“A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,
-
11 Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa,
adalci kuma yă duba daga sama.
12 Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau,
ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
13 Adalci na tafiya a gabansa
yana shirya hanya domin ƙafafunsa.
-
13 Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi
haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika;
ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.
-
10 To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. 11 Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
12 Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. 13 Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake. 14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku. 15 Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!
-
3 “ ‘In kuka kiyaye farillaina, kuka yi biyayya da umarnaina, 4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu. 5 Masussukanku za su ci gaba har lokacin girbin inabi, girbin inabi kuma zai ci gaba har lokacin shuki, za ku kuma ci duk abincin da kuke so cikin salama a ƙasarku.
-
4 Rago ba ya noma a lokacin noma;
saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
-
11 Ku fid da zuciya, ku manoma,
ku yi ihu, ku masu noma inabi;
ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,
saboda an lalata girbin filaye.
-
7 Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. 8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
-
10 “Shekara shida za ku nome gonakinku ku girbe amfanin gonar, 11 amma a shekara ta bakwai za ku bar ƙasa tă huta. Sa’an nan matalautan da suke cikinku za su sami abinci daga cikinta, namun jeji kuma za su ci abin da aka bari. Ku yi haka da gonakinku na inabi, da na itatuwan zaitun.
-
11 Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba. 12 Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.
-
5 Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye
ya kuma girbe hatsin da hannunsa
kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi
a Kwarin Refayim.
-
18 Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.
-
6 Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
-
5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah;
bari dukan mutane su yabe.
6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta
Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu.
7 Allah yă sa mana albarka,
dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.
-
16 Ku datse wa Babilon mai shuka,
da mai girbi lauje a lokacin girbi.
Saboda takobin mai zalunci
bari kowa ya koma ga mutanensa,
bari kowa ya gudu zuwa ga ƙasarsa.
-
9 Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka? 10 Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin. 11 In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba?
-
12 “Na ba ka duk man zaitun mafi kyau, da ruwan inabi mafi kyau duka, da hatsi mafi kyau duka na nunan farinsu da suke bayarwa ga Ubangiji. 13 Dukan nunan fari na ƙasar da suke kawo wa Ubangiji, zai zama naka. Kowa da yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
-
1 Daga baya, a lokacin girbin alkama, Samson ya ɗauki ɗan akuya ya tafi yă ziyarci matarsa. Sai ya ce, “Zan in shiga ɗakin matata.” Amma mahaifinta ya hana shi shiga.
-
13 A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa.
-
17 Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku,
za su cinye ’ya’yanku maza da mata;
za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku,
za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku.
Da takobi za su hallaka
biranenku masu katanga.
-
13 Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa;
za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba.
Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbe
saboda zafin fushin Ubangiji.”
-
11 Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
-
4 Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome,
amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.
-
3 Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji,
nunan fari na girbinsa;
dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi,
masifa kuwa ta same su,’ ”
in ji Ubangiji.
-
13 Ina so ku sani ’yan’uwa cewa na yi shirin zuwa wurinku sau da dama (amma aka hana ni yin haka sai yanzu). Na so in zo domin in sami mutane wa Kiristi a cikinku, kamar yadda na yi a cikin sauran Al’ummai.
-
5 Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.
6 Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. 7 Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.
-
4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki.
-
5 Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6 Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. 7 Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
8 Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
-
14 A lokacin cin abinci Bowaz ya ce mata, “Zo nan. Ki ɗebo burodi ki tsoma cikin ruwan inabi.”
Da ta zauna tare da masu girbin, sai ya ba ta gasasshe hatsi. Ta ci duk abin da take so har ta bar ragowa.
-
6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;
ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
7 Ba shi da jagora
ba shugaba ko mai mulki,
8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani
ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?
Yaushe za ku farka daga barcinku?
10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,
ɗan naɗin hannuwa don a huta,
11 talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari
rashi kuma kamar ɗan fashi.
-
20 Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika;
girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
-
13 Haka zai zama a duniya
da kuma a cikin al’ummai,
kamar sa’ad da akan karkaɗe itacen zaitun,
ko kuma kamar sa’ad da ake barin kala bayan an girbe inabi.
-
4 Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa,
da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,
zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari,
da zarar wani ya gani ya kuma tsinka,
zai haɗiye shi.
-
10 Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda
ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki;
girbin ’ya’yan inabi zai kāsa,
girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.
-
13 “ ‘Zan ƙwace girbinsu,
in ji Ubangiji.
Ba a za sami inabi a kuringa ba.
Ba za a sami ’ya’ya a itacen ɓaure ba,
ganyayensu kuwa za su bushe.
Abin da na ba su
za a ƙwace.’ ”
-
4 Abin da ɗango ya bari
fāri masu girma sun cinye;
abin da fāri masu girma suka bari,
burduduwa ta cinye;
abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.
-
23 “ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba. 24 A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji. 25 Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
-
9 Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,
ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
10 ta haka rumbunanka za su cika har su zuba,
randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
-
4 Ganimarku, ya al’ummai ƙanana fāri sun girbe;
kamar tarin fārin da mutane sun fāɗa wa.
-
19 Ka saurari kukan mutanena
daga ƙasa mai nisa suna cewa,
“Ubangiji ba ya a Sihiyona ne?
Sarkinta ba ya can ne kuma?”
“Me ya sa suka tsokane ni da gumakansu har na yi fushi,
da baƙin gumakansu marasa amfani?”
20 “Girbi ya wuce,
damuna ta ƙare,
ba a kuwa cece mu ba.”
-
15 Za ku yi shuki amma ba za ku girba ba;
za ku matse zaitun amma ba za ku yi amfani da mai wa kanku ba,
za ku tattaka ’ya’yan inabi amma ba za ku sha ruwan inabin ba.
-
6 Kun shuka da yawa, amma kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha, amma ba ku kashe ƙishirwa ba. Kun sa tufafi, amma ba ku ji ɗumi ba. Kuna karɓar albashi, ya zama sai ka ce kuna zuba a hudajjen aljihu.”
Shows Read in context, Share and Copy.