32 Bible Verses About Winter

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Winter
  1. 5 Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi;

    yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.

    6 Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’

    ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’

    7 Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa,

    ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.

    8 Dabbobi sun ɓoye;

    sun zauna cikin kogunansu.

    9 Guguwa tana fitowa daga inda take,

    sanyi kuma daga iska mai sanyi.

    10 Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara

    sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.

    11 Yana cika gizagizai da lema;

    yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.

    12 Bisa ga bishewarsa suke juyawa

    a kan fuskar duniya,

    suna yin dukan abin da ya

    umarce su su yi.

    13 Yana aiko da ruwa domin horon mutane,

    ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.

  2. 16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.

    Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;

    Ku daina aikata mugunta.

    17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.

    Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.

    Ku ba wa marayu hakkinsu,

    ku taimaki gwauruwa.

    18 Ubangiji ya ce,

    “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,

    Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,

    za su zama fari kamar ƙanƙara;

    ko da sun yi ja kamar mulufi,

    za su zama kamar ulu.

  3. 12 Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima;

    ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.

    13 Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki

    yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.

    14 Yana ba da salama ga iyakokinki

    yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

    15 Yana ba da umarninsa ga duniya;

    maganarsa tana tafiya da sauri.

    16 Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu

    yă kuma watsar da hazo kamar toka.

    17 Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu.

    Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?

    18 Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su;

    yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.

    19 Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub,

    dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.

    20 Bai yi wannan ga wata al’umma ba;

    ba su san dokokinsa ba.

    Yabi Ubangiji.

  4. 10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke

    saukowa daga sama,

    ba sa komowa

    ba tare da sun jiƙe duniya

    sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,

    don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,

    11 haka maganata da take fitowa daga bakina.

    Ba za tă koma gare ni wofi ba,

    amma za tă cika abin da nake so

    ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.

    12 Za ku fita da farin ciki

    a kuma bi da ku da salama;

    duwatsu da tuddai

    za su ɓarke da waƙa a gabanku,

    dukan itatuwan jeji kuma

    za su tafa hannuwansu.

  5. 6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;

    ka koya mini hikima a wuri can ciki.

    7 Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;

    ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

  6. 20 Sai Nuhu ya gina bagaden hadaya ga Ubangiji, ya ɗiba waɗansu dabbobi da tsuntsaye masu tsabta, ya yi hadaya ta ƙonawa da su a kan bagaden. 21 Da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce a zuciyarsa, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa saboda mutum ba, ko da yake dukan tunanin zuciyar mutum mugu ne tun yana ƙarami. Ba kuwa zan ƙara hallaka dukan halittu masu rai, kamar yadda na yi ba.

    22 “Muddin duniya tana nan,

    lokacin shuki da na girbi,

    lokacin sanyi da na zafi,

    lokacin damina da na rani,

    dare da rana

    ba za su daina ba.”

  7. 20 Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

  8. 9 “Ina cikin dubawa,

    “sai aka ajiye kursiyoyi,

    sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.

    Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;

    gashin kansa sun yi fari kamar ulu.

    Kursiyinsa kuma harshen wuta,

    dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.

  9. 11 Kalmar da aka faɗa daidai

    tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.

    12 Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla

    haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.

    13 Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi

    haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika;

    ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi.

  10. 20 Takan marabci talakawa

    takan kuma taimaki masu bukata.

    21 Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta;

    gama dukansu suna da tufafi masu kauri.

  11. 22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara

    ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara

    23 waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala,

    domin kwanakin yaƙi da faɗa?

    24 Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya,

    ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?

    25 Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,

    da kuma hanyar walƙiyar tsawa

    26 don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin

    jeji inda ba mai zama ciki

    27 don a ƙosar da wurin da ya bushe

    a sa ciyawa ta tsiro a can?

  12. 16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;

    ka kafa rana da wata.

    17 Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya;

    ka yi rani da damina.

  13. 11 Duba! Damina ta wuce;

    ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare.

    12 Furanni sun hudo a duniya;

    lokaci yin waƙa ya zo,

    ana jin kukan kurciyoyi

    ko’ina a ƙasarmu.

  14. 22 A watan tara ne sarki kuwa yana zaune a gidansa na rani, wuta kuwa tana ci a kasko a gabansa.

  15. 16 A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. 17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. 18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

    19 Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus.

    20 Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus. 21 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina.

    Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa.

    22 Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.

  16. 1 Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.

    2 Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. 3 Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. 4 Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu.

    5 Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. 6 Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta.

  17. 14 Dusar ƙanƙarar Lebanon

    ta taɓa rabuwa da kan duwatsun Lebanon?

    Ruwan mai sanyinsa daga rafuffukansa masu nesa

    sun taɓa daina gudu?

  18. 7 Yabi Ubangiji daga duniya,

    ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

    8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,

    hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

  19. 15 Zan rushe gidan rani

    da na damina;

    gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su

    haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”

    in ji Ubangiji.

  20. 12 Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.

  21. 15 Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,

    kamar rafin da yakan bushe da rani,

    16 kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,

    yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,

  22. 20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21 Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.

  23. 2 Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. 3 Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su. 4 Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  24. 22 Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki.

  25. 1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,

    haka girmamawa bai dace da wawa ba.

  26. 8 A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.

  27. 4 Rago ba ya noma a lokacin noma;

    saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.

  28. 6 Duk za a bar su wa tsuntsayen dutse su ci

    da kuma namun jeji;

    tsuntsaye kuma za su ci rani a kansu,

    namun jeji kuma za su yi damina a kansu.

  29. 12 Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can.

  30. 18 Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.

  31. 9 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri, 10 gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisa. 13 Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

  32. 11 Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus.