78 Bible Verses About Stars
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima 2 suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”
3 Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. 4 Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. 5 Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta.
6 “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda,
ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba,
gama daga cikinki mai mulki zai zo,
wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”
7 Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, yă gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, “Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada.”
9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12 Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.
-
14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
-
7 Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske;
yana hana taurari yin haske.
8 Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai
ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.
9 Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza,
da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.
10 Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa,
mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
-
16 A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
17 Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe. 18 Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.
19 “Saboda haka, ka rubuta abin da ka gani, abin da yake yanzu, da abin da zai faru nan gaba. 20 Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.
-
9 Duba, ranar Ubangiji tana zuwa,
muguwar rana, mai hasala da zafin fushi,
don ta mai da ƙasar kango
ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
10 Taurarin sama da ƙungiyoyinsu
ba za su ba da haskensu ba.
Rana za tă yi duhu
wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
-
2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,
yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
3 Yabe shi, rana da wata,
yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
4 Yabe shi, ku bisa sammai
da kuma ku ruwan bisa sarari.
5 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama ya umarta aka kuwa halicce su.
6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin;
ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
-
3 Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
4 Ya lissafta yawan taurari
ya kuma kira kowannensu da suna.
5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka;
ganewarsa ba shi da iyaka.
-
3 Sa’ad da na dubi sammai,
aikin yatsotsinka,
wata da taurari
waɗanda ka ajiye a wurarensu,
4 wane ne mutum da kake tunawa da shi,
ɗan mutum da kake lura da shi?
5 Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah
ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
-
3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
-
17 “Na gan shi, amma ba yanzu ba;
na hange shi, amma ba kusa ba.
Tauraro zai fito daga Yaƙub;
sandan mulki zai fito daga Isra’ila.
Zai ragargaje goshin Mowab,
kawunan dukan ’ya’yan Set.
-
6 Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
7 Wanda ya yi manyan haskoki,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
8 Rana don tă yi mulkin yini,
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
9 Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare;
Ƙaunarsa madawwamiya ce.
-
1 Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,
“Kada ka ji tsoro, Abram.
Ni ne garkuwarka,
kuma ladanka zai zama mai girma.”
2 Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” 3 Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”
4 Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” 5 Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
6 Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.
-
16 “Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”
-
8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,
wanda ya mai da duhu ya zama haske
ya kuma baƙanta rana ta zama dare,
yakan kwashe ruwan teku
ya zubar a ƙasa,
Ubangiji ne sunansa,
9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi
yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).
-
39 Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu. 40 Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take. 41 Rana tana da wata irin daraja, wata yana da wata darajar dabam, taurari kuma suna da tasu dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen daraja.
-
10 Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa 11 sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
12 Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.
-
15 Ba ku ga wata siffa a ranar da Ubangiji ya yi magana da ku a Horeb daga wuta ba. Saboda haka ku lura da kanku sosai, 16 don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace, 17 ko a kamannin wata dabba a duniya, ko na wani tsuntsun da yake tashi a sama, 18 ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi. 19 Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama. 20 Amma ku, Ubangiji ya ɗauke ku, ya fid da ku daga matuya mai narken ƙarfe, wato, daga Masar, domin ku zama jama’arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.
-
1 Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. 2 Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. 3 Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. 4 Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.
-
42 Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa,
“ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?
43 Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek,
da tauraron allahnku Refan,
gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada.
Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.
-
26 Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai. 27 ‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’ kamar yadda na karɓi iko daga Ubana. 28 Zan kuma ba shi tauraron asubahi.
-
31 “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta?
Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
32 Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu
ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?
33 Ka san dokokin sammai?
Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
-
26 Ku ɗaga idanunku ku duba sammai.
Wane ne ya halicce dukan waɗannan?
Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya,
yana kiransu, kowanne da sunansa.
Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma,
babu ko ɗayansu da ya ɓace.
27 Ya Yaƙub, ya Isra’ila, me ya sa kake ce
kana kuma gunaguni cewa,
“Hanyata tana a ɓoye daga Ubangiji;
Allah bai kula da abin da yake damuna ba”?
28 Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29 Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
-
25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki
shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?
26 Kun ɗaga masujadar sarkinku,
siffofin gumakanku,
tauraron allahnku,
wanda kuka yi wa kanku.
27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,”
in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.
-
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.
1 Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;
sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2 Kowace rana tana yin jawabi;
kowane dare yana nuna sani.
3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta,
ba wani amon da aka ji daga gare su.
4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya,
kalmominsu zuwa iyakokin duniya.
A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa,
kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6 Takan taso daga ƙarshen sammai
ta kewaye zuwa wancan;
babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
-
12 Yaya aka yi ka fāɗo daga sama
Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba!
An fyaɗa ka da ƙasa,
kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
13 Ka yi tunani a ranka ka ce,
“Zan hau zuwa sama;
zan ɗaga kursiyina
sama da taurarin Allah;
zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro,
a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.
-
13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!
Bari masananki na taurari su zo gaba,
waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,
bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.
14 Tabbas suna kama da bunnu;
wuta za tă cinye su ƙaf.
Ba za su ma iya ceton kansu
daga ikon wutar ba.
Ba wutar da wani zai ji ɗumi;
ba wutar da za a zauna kusa da ita.
15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,
waɗannan da kika yi ta fama da su
kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.
Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;
babu ko ɗayan da zai cece ki.
-
4 “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?
Gaya mini, in ka sani.
5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!
Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
6 A kan me aka kafa tushenta,
ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare
dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
-
8 Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama. 9 Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” 10 Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.
11 Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.
12 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13 Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.
-
7 Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu;
zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.
8 Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka;
zan kawo duhu a kan ƙasarka,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
-
29 “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan
“ ‘sai a duhunta rana,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,
za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
-
10 A gabansu duniya takan girgiza,
sararin sama kuma yakan jijjigu,
rana da wata su yi duhu,
taurari kuma ba sa ba da haske.
11 Ubangiji ya yi tsawa
wa shugaban mayaƙansa;
sojojinsa sun fi a ƙirge
masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa.
Ranar Ubangiji da girma take;
mai banrazana.
Wa zai iya jure mata?
-
24 “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan,
“ ‘rana za tă yi duhu,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25 taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.
Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
26 “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. 27 Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.
-
19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. 21 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.
-
4 Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel. 5 Ya kawar da firistocin gumakan da sarakunan Yahuda suka naɗa don su ƙona turare a masujadan kan tuddai na garuruwan Yahuda, da kuma waɗanda suke kewaye da Urushalima, masu ƙona turare wa Ba’al, rana da wata, ga rukunin taurari, da kuma ga dukan rundunan taurari.
-
12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. 14 Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.
-
15 Za a duhunta rana da wata,
taurari kuma ba za su ba da haske ba.
-
10 “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba, 11 ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri. 12 Ga abin da zan yi wa wannan wuri da waɗanda suke zaune a nan, in ji Ubangiji. Zan mai da wannan birni kamar Tofet. 13 Gidaje a Urushalima da waɗannan na sarakunan Yahuda za su ƙazantu kamar wannan wuri, Tofet, dukan gidajen da suke ƙone turare a kan rufi wa duk rundunan taurari suna kuma zuba hadayun sha ga sauran alloli.’ ”
-
35 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
shi da ya kafa rana
don tă yi haske a yini
shi da ya sa wata da taurari
su yi haske da dare,
shi da yake dama teku
don raƙuman ruwansa su yi ruri
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
36 “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,”
in ji Ubangiji,
“to, sai zuriyar Isra’ila ta daina
zama al’umma a gabana.”
37 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“In a iya auna sammai
a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas
to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan
saboda dukan abin da suka yi,”
in ji Ubangiji.
-
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna;
ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji;
bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
-
1 Ku zo kusa, ku al’ummai, ku kuwa saurara
ku kasa kunne, ku mutane!
Bari duniya ta ji, da kuma dukan abin da yake cikinta,
duniya, da dukan abin da yake fitowa daga gare ta!
2 Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai;
hasalarsa tana a kan mayaƙansu.
Zai hallaka su tas,
zai ba da su a karkashe.
3 Za a jefar da waɗanda aka kashe
gawawwakinsu za su yi wari;
duwatsu za su jiƙu da jininsu.
4 Za a tumɓuke dukan taurarin sammai
za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi;
dukan rundunar sama za su fāffāɗi
kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa,
kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
-
16 Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. 17 Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.
18 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari, 19 ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo. 20 Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.
-
1 “ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura. 2 Za a shimfiɗa su a rana da wata da kuma dukan taurarin sammai, waɗanda suka ƙaunata suka kuma bauta wa, waɗanda suka bi suka nemi shawarar suka kuma yi wa sujada. Ba za a tattara su ko a binne su ba, amma za su zama kamar juji a jibge a ƙasa. 3 Duk inda na kore su zuwa, dukan waɗanda suka ragu na wannan muguwar al’umma za su gwammaci mutuwa da rai, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
-
10 Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su.
-
15 Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu 16 ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, 17 tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, 18 ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”
-
1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
2 “Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;
yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.
3 Za a iya ƙirga rundunarsa?
A kan wane ne ba ya haska haskensa?
4 Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?
5 In har wata da taurari
ba su da tsarki a idanunsa,
6 mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.
Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”
-
4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda
da kuma dukan mazaunan Urushalima.
Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri,
da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,
5 waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki
don su yi sujada ga rundunar taurari.
Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji
suke kuma rantsuwa da sunan Molek.
6 Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji,
ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”
-
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.
-
22 Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.
-
2 In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa, 3 wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama, 4 in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila, 5 sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu. 6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba. 7 Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
-
1 Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba. 2 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. 3 Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada. 4 Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.” 5 Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari. 6 Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.
-
23 Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.
-
6 Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
-
8 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, sa’ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba. 9 Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi. 10 Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne. 11 Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce, Saratu kanta kuma bakararriya ce ya iya zama mahaifi domin ya amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne. 12 Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.
-
9 Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
10 Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
-
1 Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis.
-
11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa.
Game da abubuwan da ke zuwa,
kun tambaye ni game da ’ya’yana,
ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana?
12 Ai, ni ne wanda ya yi duniya
na kuma halicci mutum a kanta.
Hannuwana ne sun miƙe sammai;
na umarci rundunar sararin sama.
-
1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
2 Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne. 3 Kai kam ka daure ka kuma jimre da wahala saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.
4 Duk da haka ina riƙe da wannan game da kai. Ka watsar da ƙaunarka ta farko. 5 Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake. 6 Sai dai kana da wannan abu mai kyau. Ka ƙi ayyukan Nikolaitawa da ni ma nake ƙi.
7 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.
-
21 Saboda haka muka ci gaba da aiki, rabin mutane suna riƙe da māsu, daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari. 22 A wannan lokaci na kuma ce wa mutane, “A sa kowane mutum da mataimakinsa su zauna a Urushalima da dare, domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.” 23 Saboda haka ni, da ’yan’uwana, da bayina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa; kowa ya rataye makaminsa, ko ya je shan ruwa ma.
-
9 Bari taurarinta na safe su zama duhu;
bari ranar tă yi ta jiran ganin haske
amma kada tă gani,
-
12 “Ba Allah ne a can sama ba?
Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
-
22 Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ”
-
25 “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. 26 Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama. 27 A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.
-
20 Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.
-
4 Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya,
-
1 Ka tuna da Mahaliccinka
a kwanakin ƙuruciyarka,
kafin lokacin wahala ta zo
shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,
“Ba na jin daɗinsu,”
2 kafin rana da haske
wata da taurari su daina haske,
gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;
3 sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,
majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,
sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,
idanun da suke duba ta taga suka duhunta;
4 sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna
ƙarar niƙa kuma ya tsagaita;
sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane,
ba a kuwa jin waƙoƙinsu,
5 sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu
da kuma hatsarori a tituna;
sa’ad da itacen almon ya toho,
fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar,
sha’awace-sha’awace sun kafe.
Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa
ya bar masu makoki suna ta yi.
6 Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse,
ko tasar zinariya ta fashe;
kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula,
ko guga ta tsinke a rijiya,
7 turɓaya ta koma ƙasar da ta fito,
rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.
8 “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami,
“Gaba ɗaya ba amfani!”
-
13 Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ”
-
1 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta,
Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai.
Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne.
-
10 Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari.
-
1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.
-
16 Yini naka ne, dare kuma naka ne;
ka kafa rana da wata.
-
19 Wata ne ke ƙididdigar lokuta,
rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.
-
16 Sa’an nan ya kawo ni cikin fili na cikin gidan Ubangiji, a can kuwa a ƙofar haikali, tsakanin shirayi da bagade, akwai kamar mutum ashirin da biyar. Suka ba haikalin Ubangiji baya suna fuskanta wajen gabas, suna rusuna wa rana a gabas.
17 Ya ce mini, “Ka ga wannan, ɗan mutum? Ƙaramin abu ne gidan Yahuda su yi abubuwan banƙyamar da suke yi a nan? Dole ne su cika ƙasar da rikici su kuma ci gaba da tsokane ni in yi fushi? Dube su suna tsokanata! 18 Saboda haka zan hukunta su cikin fushi; Ba zan dube su da tausayi ko kuwa in ƙyale su ba. Ko da yake suna ihu a kunnuwana, ba zan saurare su ba.”
-
3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
-
1 Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu.
2 Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. 3 Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
-
26 In na dubi rana cikin haskenta,
ko kuma wata yana tafiyarsa,
27 zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye,
hannuna kuma ya sumbace su.
28 Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan
don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
-
5 Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji,
amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.
-
31 Rana za tă duhunta
wata kuma yă zama jini
kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.
-
1 Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. 2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa. 3 Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
Shows Read in context, Share and Copy.