38 Bible Verses About Sorcery

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Sorcery
  1. 9 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can. 10 Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri, 11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu. 12 Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku. 13 Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.

    14 Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba.

  2. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

  3. 9 Duk waɗannan za su sha kanki

    cikin farat ɗaya, a rana guda,

    rashin ’ya’ya da gwauranci.

    Za su zo a kanki da cikakken minzani,

    duk da yawan masu dubanki

    da kuma dukan sihirinki.

    10 Kin dogara a muguntarki

    kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’

    Hikimarki da saninki sun ɓad da ke

    sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’

    11 Bala’i zai fāɗo a kanki,

    kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba.

    Masifa za tă fāɗo a kanki

    da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba;

    lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba

    za tă auko miki nan da nan.

    12 “Ki dai ci gaba, da sihirinki

    da kuma makarunki masu yawa,

    waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya.

    Mai yiwuwa ki yi nasara,

    mai yiwuwa ki jawo fargaba.

    13 Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!

    Bari masananki na taurari su zo gaba,

    waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,

    bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.

    14 Tabbas suna kama da bunnu;

    wuta za tă cinye su ƙaf.

    Ba za su ma iya ceton kansu

    daga ikon wutar ba.

    Ba wutar da wani zai ji ɗumi;

    ba wutar da za a zauna kusa da ita.

    15 Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,

    waɗannan da kika yi ta fama da su

    kika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.

    Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;

    babu ko ɗayan da zai cece ki.

  4. 10 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. 11 Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. 12 Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu.

  5. 9 To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne, 10 dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma” 11 Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa. 12 Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata. 13 Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.

    14 Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna. 15 Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki, 16 domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu. 17 Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.

    18 Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, 19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”

    20 Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! 21 Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22 Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23 Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”

    24 Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”

  6. 11 Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, 12 har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

    13 Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.” 14 ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka. 15 Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?” 16 Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.

    17 Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai. 18 Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. 19 Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin. 20 Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.

  7. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

  8. 6 Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7 wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. 8 Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9 Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10 “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11 Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.”

    Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. 12 Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.

  9. 1 Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar. 2 Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. 3 Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada. 4 Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.” 5 Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari. 6 Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.

    7 Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

  10. 23 Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa

    a cikinki ba.

    Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya

    a cikinki ba.

    Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya.

    Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.

  11. 18 “Kada ku bar maiya da rai.

  12. 19 Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai? 20 Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani. 21 Cikin matsuwa da yunwa, za su yi ta kai komo ko’ina a ƙasar; sa’ad da suka ji yunwa, za su yi fushi su tā da idanu sama, su zagi sarkinsu da Allahnsu. 22 Sa’an nan za su zura wa ƙasa idanu, abin da za su gani kawai shi ne matsuwa da duhu da kuma abin banrazana, za a kuma jefa su cikin baƙin duhu.

  13. 16 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Miƙa hannunka ka bugi ƙurar ƙasa,’ dukan ƙurar ƙasar Masar kuwa za tă zama ƙwari masu cizo.” 17 Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku. 18 Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa.

    Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi. 19 Sai bokaye suka ce wa Fir’auna, “Wannan fa da hannun Allah a ciki.” Amma zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurara ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

  14. 31 “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  15. 6 “ ‘Zan yi gāba da mutumin da ya juyo ga masu duba da bokaye, don yă yi karuwanci ta wurin bin su, zan kuma raba shi daga mutanensa.

  16. 1 Ɗana, kada ka manta da koyarwata,

    amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,

    2 gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa

    su kuma kawo maka wadata.

    3 Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai;

    ka ɗaura su kewaye da wuyanka,

    ka rubuta su a allon zuciyarka.

    4 Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau

    a gaban Allah da kuma a gaban mutane.

    5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  17. 9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’ 10 Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.

  18. 26 Ku zama tsarkakakke gare ni, gama Ni Ubangiji, mai tsarki ne, na kuma keɓe ku daga al’ummai don ku zama nawa.

    27 “ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ”

  19. 13 Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, 14 bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.

  20. 10 “A wannan rana,” in ji Ubangiji

    “Zan hallaka dawakanku daga cikinku,

    in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.

    11 Zan hallaka biranen ƙasarku

    in yi rugu-rugu da dukan katangunku.

    12 Zan kawar da maitarku,

    ba za a ƙara yin sihiri ba.

  21. 16 Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi. 17 Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” 18 Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.

  22. 12 “Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi. 13 Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.

    14 “Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi. 15 Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.

  23. 22 Amma Sama’ila ya ce,

    “Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya

    fiye da biyayya ga maganar Ubangiji?

    Yin biyayya ta fi hadaya

    a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna.

    23 Gama tawaye yana kama da zunubi na duba,

    girman kai kuma yana kama da bautar gumaka.

    Saboda ka ƙi maganar Ubangiji,

    shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”

  24. 23 Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub,

    ba sihiri da zai cuci Isra’ila.

    Yanzu za a ce game da Yaƙub

    da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’

    24 Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya;

    sun tā da kansu kamar zaki

    wanda ba ya hutawa

    sai ya cinye naman abin da ya kama

    ya kuma sha jinin abin da ya kama.”

    25 Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”

    26 Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”

    27 Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.”

  25. 6 Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

  26. 2 Gumaka suna maganganun ruɗu,

    masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,

    suna faɗa mafarkan ƙarya

    suna ba da ta’aziyyar banza.

    Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki

    waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.

  27. 17 “To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan ’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu 18 ka kuma ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton matan da suke ɗinka kambuna a hannuwansu suna kuma yin gyale masu tsawo dabam-dabam wa kawunansu don su farauci mutane. Za ku farauci rayukan mutanena ku bar naku? 19 Kun jawo mini kunya a cikin mutanena don a tafa muku sha’ir da ɗan dunƙulen burodi. Ta wurin yin ƙarya wa mutanena, waɗanda suke jin ƙarairayi, kuka kashe waɗanda bai kamata su mutu ba kuka bar waɗanda ya kamata su mutu.

    20 “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kambunanku waɗanda kuke farautar mutane da su kamar tsuntsaye don haka zan kuma tsintsinke su daga hannuwanku; zan ’yantar da mutanen da kuka farauto kamar tsuntsaye. 21 Zan kyakketa gyalenku in ceci mutanena daga hannuwanku, ba za su kuma ƙara zama ganima a hannunku ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji 22 Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu, 23 saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  28. 20 Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. 21 Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.

  29. 20 Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarta. Ya ɗaga sandansa a gaban Fir’auna da bayinsa, ya bugi ruwan Nilu, dukan ruwan kuwa ya zama jini. 21 Kifin da suke cikin Nilu suka mutu, kogin kuwa ya yi wari sosai yadda Masarawa ba su iya shan ruwan ba. Jini ya bazu ko’ina a Masar.

    22 Amma bokayen Masar ma suka yi abubuwan nan da sihirinsu, sai zuciyar Fir’auna ta taurare; bai saurari Musa da Haruna ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

  30. 5 “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  31. 16 Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. 17 Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.

  32. 6 Ka rabu da mutanenka,

    gidan Yaƙub.

    Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;

    suna yin duba kamar Filistiyawa

    suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.

  33. 27 Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi, 28 amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,

  34. 1 Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2 Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. 3 Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

  35. 9 Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, 10 da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. 11 Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya 12 don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.

  36. 4 Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

  37. 24 Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.

  38. 7 Masu gani za su ji kunya,

    masu duba kuma za su ji taƙaici.

    Dukansu za su rufe fuskokinsu

    gama ba amsa daga Allah.”