60 Bible Verses About Justice
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
6 Da me zan zo a gaban Ubangiji
in rusuna a gaban Maɗaukaki Allah?
Shin, zan zo ne a gabansa da hadaya ta ƙonawa,
da ɗan maraƙi bana ɗaya?
7 Ubangiji zai ji daɗin hadayar raguna dubbai
da kuma rafuffukan mai dubbai goma?
Zan ba da ɗan farina ne don laifina,
ko ’ya’yan jikina domin zunubin raina?
8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
9 Ku saurara! Ubangiji yana kira ga birni,
a ji tsoron sunana kuwa hikima ce,
“Ku kasa kunne ga sandan nan da kuma wannan wanda ya naɗa.
-
19 Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya. 20 Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.
-
16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku.
Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana;
Ku daina aikata mugunta.
17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci.
Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta.
Ku ba wa marayu hakkinsu,
ku taimaki gwauruwa.
18 Ubangiji ya ce,
“Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare,
Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura,
za su zama fari kamar ƙanƙara;
ko da sun yi ja kamar mulufi,
za su zama kamar ulu.
-
21 Amma yanzu an bayyana wani adalci daga Allah, wannan adalcin bai danganta ga doka ba, Doka da Annabawa suna ba da shaida game da wannan adalci. 22 Wannan adalcin Allah yana zuwa ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi ga dukan waɗanda suka ba da gaskiya ne. Ba bambanci, 23 gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, 24 an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. 25 Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba 26 ya yi haka domin yă nuna adalcinsa a wannan lokaci, saboda yă zama mai adalci da mai kuɓutar da waɗanda suke ba da gaskiya a cikin Yesu.
-
2 “Har yaushe za ku kāre marasa adalci
ku kuma goyi bayan mugaye? Sela
3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;
ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;
ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.
-
8 “Yi magana domin bebaye,
domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;
a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”
-
8 “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;
na ƙi fashi da aikata laifi.
Cikin adalcina zan sāka musu
in kuma yi madawwamin alkawari da su.
9 Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai
’ya’yansu kuma a cikin mutane.
Dukan waɗanda suka gan su za su san
cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”
-
9 “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku yi shari’ar gaskiya; ku nuna jinƙai da tausayi ga juna. 10 Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’
-
6 “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a. 7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.
8 “Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.
9 “Kada ka zalunci baƙo, ku kanku kun san halin baƙunci, gama dā ku baƙi ne a Masar.
-
13 Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 14 Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 15 Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16 Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.
-
3 Zan yi shelar sunan Ubangiji.
Ku yabi girman Allahnmu!
4 Shi Dutse ne, ayyukansa cikakku ne,
dukan hanyoyinsa kuwa masu adalci ne.
Allah mai aminci, wanda ba ya yin rashi gaskiya,
shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
-
11 Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12 zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.
-
3 Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci,
waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.
4 Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka,
ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
-
1 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Ku riƙe gaskiya
ku yi abin da yake daidai,
gama cetona yana kusa
za a kuma bayyana adalcina nan da nan.
-
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya;
yana da aminci cikin kome da yake yi.
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci
duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
-
3 Yin abin da yake daidai da kuma nagari
Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
-
13 “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace.
“ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
14 “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
15 “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
-
27 Ku juyo daga mugunta ku yi alheri;
sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
28 Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai
kuma ba zai yashe amintattunsa ba.
Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,
’ya’yan mugaye za su hallaka.
29 Masu adalci za su gāji ƙasar
su kuma zauna a cikinta har abada.
-
15 Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci
amma fargaba ga masu aikata mugunta.
-
1 “Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.
2 “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.
-
16 Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai. 17 Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci. 18 Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi. 19 Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.
-
23 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.
-
35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
37 “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ”
-
6 Ubangiji yana aikata adalci
da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.
-
13 Hannunka mai iko ne;
hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.
14 Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka;
ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.
-
16 Sai na ga wani abu kuma a duniya,
a wurin shari’a, akwai mugunta a can,
a wurin adalci, akwai mugunta a can.
17 Sai na yi tunani a zuciyata,
“Allah zai shari’anta
masu adalci da masu mugunta,
gama za a kasance da lokaci domin kowane aiki,
lokaci domin kowane abu.”
-
3 zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.
Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,
ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
4 amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,
da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.
Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;
da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
5 Adalci ne zai zama abin ɗamararsa
aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
-
1 “Ga bawana, wanda na ɗaukaka,
zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi;
Zan sa Ruhuna a cikinsa
zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
2 Ba zai yi ihu ko ya tā da murya,
ko ya daga muryarsa a tituna ba.
3 Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba,
ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba.
Cikin aminci zai kawo adalci;
4 ba zai kāsa ko ya karai ba
sai ya kafa adalci a duniya.
Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
-
26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. 28 Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29 Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30 Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” 31 Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
-
12 Ka tashi, Ubangiji! Ka hukunta miyagu, ya Allah.
Kada ka manta da marasa ƙarfi.
13 Don me mugun mutum zai ƙi Allah?
Don me yakan ce wa kansa,
“Allah ba zai nemi hakki daga gare ni ba”?
14 Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki;
kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu.
Marar taimako kan danƙa kansa gare ka;
kai ne mai taimakon marayu
15 Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum;
ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar
da ba za a gane ba.
16 Ubangiji Sarkin har abada abadin ne;
al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.
17 Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala;
kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,
18 kana kāre marayu da waɗanda aka danne,
domin mutum, wanda yake na duniya
kada ƙara haddasa wata razana.
-
5 Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri
ko ka hana wa marar laifi adalci.
-
5 Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. 6 Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala 7 yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. 8 Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. 9 Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa 10 a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.
-
1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,
amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
-
Ƙarin maganganun hikima
23 Waɗannan ma maganganun masu hikima ne,
Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
24 Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”,
mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
25 Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi,
kuma babban albarka zai zo a kansu.
-
14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba;
don ku rayu
sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,
kamar yadda kuka ce zai yi.
15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta;
ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a.
Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin
raguwar Yusuf.
-
23 Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba. 24 Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa. 25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
-
23 Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? 24 Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? 25 Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”
26 Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.”
-
11 Duk wanda ya ji ni ya yaba mini
waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
12 domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako,
da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
13 Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka.
Na faranta wa gwauruwa zuciya.
14 Na yafa adalci ya zama suturata;
gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15 Ni ne idon makafi
kuma ƙafa ga guragu.
16 Ni mahaifi ne ga masu bukata;
na tsaya wa baƙo.
17 Na karya ƙarfin mugaye
na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.
-
7 Gama Ubangiji mai adalci ne,
yana ƙaunar gaskiya
masu adalci za su ga fuskarsa.
-
5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa,
wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.
6 Mahaliccin sama da ƙasa,
teku, da kome da yake cikinsu,
Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.
7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne
ya kuma ba da abinci ga mayunwata.
Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,
8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido,
Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,
Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.
9 Ubangiji yana tsaron baƙi
yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa,
amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.
-
26 Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki,
amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.
27 Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya;
mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.
-
3 Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka yi abin da yake gaskiya da kuma daidai. Ka kuɓutar da wannan da aka yi masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka yi abin da ba daidai ba ko ka cuci baƙo, maraya ko gwauruwa, kuma kada ka zub da jini marar laifi a wannan wuri.
-
1 Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2 Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. 3 Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. 4 Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.
-
1 Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.
-
17 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18 Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19 sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
-
5 Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce,
“Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai,
kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;
6 gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka,
ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”
7 Na kuma ji bagaden ya amsa,
“I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki,
hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”
-
11 Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.
-
Zabura ta Dawuda.
1 Ya Ubangiji, ka ji addu’ata,
ka saurari kukata don neman jinƙai;
cikin amincinka da adalcinka
ka amsa mini.
2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a,
gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka.
-
5 Mugaye ba su san gaskiya ba,
amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.
-
14 In sarki yana hukunta talakawa da adalci
kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.
-
14 Saboda haka aka kau da yin gaskiya
adalci kuma ya tsaya can da nesa;
gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna,
sahihanci ba zai shiga ba.
15 Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya,
kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima.
Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi
cewa babu adalci ba.
-
5 “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
-
19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,
“In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;
in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.
Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”
-
8 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
-
27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
-
7 Ubangiji yana mulki har abada;
ya kafa kujerarsa don shari’a.
8 Zai hukunta duniya da adalci;
zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
-
13 Allah na Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub, Allah na kakanninmu, ya ɗaukaka bawansa Yesu. Ku kuka ba da shi domin a kashe, kuka yi mūsun saninsa a gaban Bilatus, ko da yake ya yi niyya ya sake shi. 14 Kuka yi mūsun sanin Mai Tsarki da Mai Adalci kuka roƙa a sakar muku mai kisankai. 15 Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan.
-
3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne? 4 Ko kuma kana rena wadatar alherinsa, haƙurinsa, da kuma jimrewarsa ne ba tare da sanin cewa alherin Allah yana kai ka ga tuba ba ne?
5 Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. 6 Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” 7 Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. 8 Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.
-
2 Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, 3 yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.
-
9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
Shows Read in context, Share and Copy.