71 Bible Verses About Cheating

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Cheating
  1. 5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

    8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

  2. 1 Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2 Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. 3 Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. 4 Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.

    5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa 10 kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. 11 A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.

  3. 15 Ba za ka yi sata ba.

    16 Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  4. 22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya,

    amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

  5. 5 Aboki kan ruɗi aboki,

    ba mai faɗar gaskiya.

    Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya;

    sun gajiyar da kansu da yin zunubi.

    6 Kai kana zama a tsakiyar ruɗu;

    cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,”

    in ji Ubangiji.

    7 Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa,

    “Ga shi zan tace in kuma gwada su,

    gama me kuwa zan yi

    saboda zunubin mutanena?

    8 Harshensu kibiya ce mai dafi;

    yana magana da ruɗu.

    Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa,

    amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.

    9 Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?”

    In ji Ubangiji.

    “Bai kamata in ɗau fansa

    a kan irin al’umma kamar wannan ba?”

  6. 23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba

    haka leɓuna masu mugun zuciya.

    24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,

    amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

    25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,

    gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

    26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,

    duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.

    27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;

    in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.

    28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,

    daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

  7. 42 Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni. 43 Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi. 44 Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma. 45 Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata! 46 Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni? 47 Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”

  8. 9 Zuciya ta fi kome ruɗu

    ta fi ƙarfin warkewa.

    Wa zai iya gane ta?

    10 “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya

    in gwada tunani,

    don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,

    bisa ga ayyukansa.”

  9. 27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.

    31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.

    33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.

  10. 16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi,

    abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

    17 duban reni,

    harshe mai ƙarya,

    hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

    18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru,

    ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

    19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi,

    da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  11. 7 Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku? 8 Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga ’yan’uwanku ne kuke yi wannan. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  12. 20 Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi. 21 Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu, 22 sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. 23 A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. 24 Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

    25 Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.

  13. 12 Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13 Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.

  14. 10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?

    13 “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”

  15. 1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba,

    amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.

  16. 20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  17. 3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1

    wani abu marar kyau ba.

    Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci;

    ba za su manne mini ba.

    4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni;

    ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

    5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye

    shi za a kashe;

    duk mai renin wayo da mai girman kai,

    ba zan jure masa ba.

    6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar,

    don su zauna tare da ni;

    tafiyarsa ba ta da zargi

    zai yi mini hidima.

    7 Babu mai ruɗun

    da zai zauna a gidana;

    babu mai ƙaryan

    da zai tsaya a gabana.

    8 Kowace safiya zan rufe bakunan

    dukan mugaye a ƙasar;

    zan yanke kowane mai aikata mugunta

    daga birnin Ubangiji.

  18. 17 Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi,

    amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.

  19. 12 Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13 Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14 Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15 da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16 Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17 domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

  20. 19 ’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so. 21 Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.

    22 Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. 23 Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi 24 bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa. 25 Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.

    26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne. 27 Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

  21. 7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

    8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10 Gama,

    “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa,

    yă kuma ga kwanaki masu kyau

    dole yă ƙame harshensa daga mugunta

    leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

    11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta;

    dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

    12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

    kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu,

    amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”

  22. 7 Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. 8 Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

  23. 4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne;

    gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.

    5 Masu fariya ba za su iya tsaya

    a gabanka ba.

    Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.

    6 Kakan hallaka masu yin ƙarya.

    Masu kisankai da mutane masu ruɗu

    Ubangiji yana ƙyama.

  24. 7 Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;

    yana jin daɗin cuta.

    8 Efraim yana fariya yana cewa,

    “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.

    Da dukan wadatata ba za a sami

    wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”

  25. 4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata

    kuka kori matalautan ƙasar.

    5 Kuna cewa,

    “Yaushe Sabon Wata zai wuce

    don mu sayar da hatsi,

    Asabbaci ta wuce,

    don mu sayar da alkama?”

    Mu yi awo da ma’aunin zalunci

    mu ƙara kuɗin kaya

    mu kuma cutar da mai saya,

    6 mu sayi matalauta da azurfa

    masu bukata kuma da takalmi,

    mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

    7 Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.

  26. 10 Har yanzu zan manta, ya muguwar gida

    da dukiyarki da kika samu a muguwar hanya

    zan kuma manta da bugaggen mudun awo wanda ake zargi?

    11 Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya,

    da kuma buhun ma’aunan ƙarya?

    12 Attajiranta masu fitina ne;

    mutanenta kuma maƙaryata ne

    harsunansu kuwa suna yaudara.

  27. 11 “ ‘Kada ku yi sata.

    “ ‘Kada ku yi ƙarya.

    “ ‘Kada ku ruɗe juna.

    12 “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.

  28. 1 Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna. 2 Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, 3 yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

  29. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, 3 ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi, 4 sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta. 5 Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  30. 5 Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba

    in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.

    6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya

    tarin tururi ne da kuma mugun tarko.

  31. 4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

  32. 7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

  33. 13 Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 14 Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. 15 Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. 16 Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.

  34. 7 Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana;

    wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.

  35. 23 Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba,

    da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.

  36. 28 Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. 29 Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, 30 da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; 31 su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. 32 Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

  37. 17 Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18 Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo. 19 Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.

    20 Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku.

    Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

  38. 1 Saboda haka, da yake ta wurin jinƙan Allah ne muke da wannan hidima, ba za mu fid da zuciya ba. 2 Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.

  39. 13 Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; 14 amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. 15 Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.

    16 Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu. 17 Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

  40. 1 Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. 2 Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. 3 Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. 4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. 5 Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. 6 Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.

  41. 14 Ba za ka yi zina ba.

  42. 5 Shirye-shiryen masu adalci daidai ne,

    amma shawarar mugaye ruɗu ne.

  43. 25 Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka,

    amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.

  44. 12 “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ 13 Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

    “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji Ubangiji. 14 “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  45. 12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

    14 Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.

  46. 35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.

  47. 32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;

    duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.

    33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,

    kuma kunyarsa za tă dawwama.

  48. 9 Mai mutunci yana tafiya lafiya,

    amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.

  49. 19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada,

    amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.

    20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta,

    amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.

  50. 15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17 Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 18 Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 19 Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20 Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

    21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

    24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

  51. 3 Wa zai iya hawan tudun Ubangiji?

    Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?

    4 Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya,

    wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki

    ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.

    5 Zai sami albarka daga Ubangiji

    da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.

  52. 6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;

    ka koya mini hikima a wuri can ciki.

  53. 2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

    daga leɓuna masu ƙarya

    da kuma daga harsuna masu yaudara.

  54. 17 Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne. 18 Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. 19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,

    “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;

    in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.

    Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”

    21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.

  55. 13 “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne,

    harsunansu suna yin ƙarya.”

    “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”

  56. 8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu,

    amma wautar wawaye ruɗu ne.

  57. 18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. 19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; 20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.

  58. 6 Kun san cewa na yi aiki wa mahaifinku da dukan ƙarfina, 7 duk da haka mahaifinku ya cuce ni ta wurin sauya albashina sau goma. Amma dai, Allah bai yardar masa yă yi mini lahani ba. 8 In ya ce, ‘Dabbare-dabbare ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi dabbare-dabbare, in kuma ya ce, ‘Masu zāne-zāne ne za su zama ladanka,’ sai dukan garkunan su haifi ƙananan masu zāne-zāne. 9 Ta haka Allah ya kwashe dabbobin mahaifinku ya ba ni.

  59. 18 Mugun mutum kan sami albashin ƙarya

    amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.

  60. 17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya,

    amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.

  61. 13 “Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci,

    ɗakunansa na sama kuma ta hanyar rashin gaskiya,

    yana sa mutanen ƙasarsa suna aiki a banza

    ba ya biyansu wahalarsu.

  62. 18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum. 19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa. 20 Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

  63. 1 To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. 2 Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.

    3 Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? 4 Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

    5 Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.

  64. 13 Ina rubuta muku, ubanni,

    domin kun san shi wanda yake tun farko.

    Ina rubuta muku, samari,

    domin kun ci nasara a kan mugun nan.

    14 Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,

    domin kun san Uba.

    Ina rubuta muku, ubanni,

    domin kun san shi wanda yake tun farko.

    Ina rubuta muku, samari,

    domin kuna da ƙarfi,

    maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,

    kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

    15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

  65. 10 Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba,

    Ubangiji ya ƙi su duka.

  66. 22 Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.

  67. 8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

    11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.

  68. 19 Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20 bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21 da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

    22 Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23 sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. 24 Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa.

  69. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

  70. 13 “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace.

    “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.

  71. 12 Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu,

    waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni;

    yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.