48 Bible Verses About Greed

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About Greed
  1. 6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

  2. 15 Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”

  3. 3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. 4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. 5 Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.

  4. 27 Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa,

    amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.

  5. 1 Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. 2 Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. 3 Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe. 4 Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. 5 Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka. 6 Kun hukunta kun kuma kashe mutane marasa laifi, waɗanda ba su yi gāba da ku ba.

  6. 10 Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;

    duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu.

    Wannan ma ba shi da amfani.

    11 Kamar yadda kaya suke haɓaka,

    haka ma masu amfani da su.

    Kuma wane amfani ne suke ga mai shi

    in ba ciyar da idanunsa a kansu ba?

    12 Barcin ma’aikaci daɗi gare shi,

    ko yă ci kaɗan ko da yawa,

    amma yalwar mai arziki

    ba ta barinsa yă iya yin barci.

  7. 9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, 10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. 11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

  8. 25 Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye,

    amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.

    26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne,

    amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.

    27 Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba,

    amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.

    28 Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya;

    amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya.

  9. 24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

  10. 5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.

  11. 19 Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau;

    ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.

  12. 3 Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi

    gama wannan abinci ruɗu ne.

    4 Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki;

    ka kasance da hikimar dainawa.

    5 Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace,

    gama tabbatacce sukan yi fikafikai

    sukan tashi sama kamar gaggafa.

  13. 5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

    “Ba zan taɓa bar ka ba;

    ba zan taɓa yashe ka ba.”

  14. 15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

  15. 20 Mutum mai aminci zai cika da albarka,

    amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.

    21 Nuna sonkai ba shi da kyau,

    duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.

    22 Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki

    bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.

  16. 3 Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

  17. 3 Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa;

    yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.

  18. 19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20 Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.

  19. 11 Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.

  20. 16 wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.

    17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  21. 1 Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. 2 Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; 3 ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.

  22. 5 ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi;

    yana fariya kuma ba ya hutu.

    Domin shi mai haɗama ne kamar kabari

    kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi;

    yakan tattara dukan al’ummai wa kansa

    yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.

    6 “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa,

    “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata

    ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace!

    Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’

  23. 5 Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.

  24. 2 To, dole mai kula da Ikkilisiya yă kasance marar abin zargi, mijin mace guda, mai sauƙinkai, mai kamunkai, wanda ake girmama, mai karɓan baƙi, mai iya koyarwa, 3 ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba sai dai mai hankali, ba mai yawan faɗa ba, ba kuma mai yawan son kuɗi ba.

  25. 10 Kada ku dogara a kan ƙwace

    ko yin fariya a kayan sata;

    ko arzikinku ya ƙaru,

    kada ku sa zuciyarku a kansu.

  26. 13 “Daga ƙarami zuwa babba,

    dukansu masu haɗama ne don riba;

    har da annabawa da firistoci,

    dukansu suna aikata rashin gaskiya.

  27. 20 Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21 Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22 kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23 Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  28. 28 Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi,

    amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.

  29. 25 Marmarin rago zai zama mutuwarsa,

    domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.

    26 Dukan yini yana marmari ya sami ƙari,

    amma mai adalci yakan bayar hannu sake.

  30. 10 Matsaran Isra’ila makafi ne,

    dukansu jahilai ne;

    dukansu bebayen karnuka ne

    ba za su iya haushi ba;

    suna kwance ne kawai suna mafarki,

    suna son barci ba dama.

    11 Su karnuka ne masu kwaɗayi;

    ba su taɓa ƙoshi.

    Su makiyaya ne marasa ganewa;

    duk sun nufi inda suka ga dama,

    kowa yana nemar wa kansa riba.

  31. 10 Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu

    gonakinsu kuma ga waɗansu da suka ci da yaƙi.

    Tun daga ƙarami har zuwa babba,

    kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba;

    har da annabawa da firistoci ma,

    kowannensu yana ƙarya.

  32. 36 Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?

  33. 11 Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,

    amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.

    12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,

    amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.

  34. 21 Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa

    ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.

  35. 1 An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;

    tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.

  36. 25 “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.

  37. 39 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.

  38. 8 Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.

  39. 17 Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

  40. 35 Ka bi da ni a hanyar umarnanka,

    gama a can zan sami farin ciki.

    36 Ka juye zuciyata wajen farillanka

    ba wajen riba ta sonkai ba.

    37 Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani;

    ka kiyaye raina bisa ga maganarka.

  41. 8 Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali

    yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.

  42. 4 Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo

    amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.

  43. 31 Mutanena sukan zo wurinka, yadda suka saba su zauna a gabanka don su saurari maganarka, amma ba sa aiki da abin da suka ji. Da bakunansu suna nuna ƙauna, amma zukatansu cike da haɗama suke don ƙazamar riba.

  44. 1 Ana nan sa’ad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci. 2 Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba. 3 Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.

  45. 4 Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, 5 “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” 6 Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.

  46. 18 Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. 19 Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

  47. 11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.

  48. 7 Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.