46 Bible Verses About Bribery
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
6 “Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a. 7 Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.
8 “Kada ka karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta waɗanda suke gani, yakan kuma karkatar da maganar masu adalci.
-
19 Kada ku ɓata shari’a, ko ku nuna bambanci. Kada ku karɓi cin hanci, gama cin hanci yakan makanta idanu mai hikima, yă murɗe maganar mai gaskiya.
-
1 Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila. 2 Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba. 3 Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
-
9 Kada ka ɗauke raina tare da masu zunubi
raina tare da masu son yin kisankai
10 waɗanda akwai mugayen dabaru a hannuwansu,
waɗanda hannuwansu na dama suna cike da cin hanci.
-
23 Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce
don yă lalace yin adalci.
24 Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,
amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
-
22 Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi
da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
23 waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,
amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
24 Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara
kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta,
haka saiwarsu za su ruɓa
iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura;
gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki
suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
-
12 A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
13 “ ‘Tabbatacce zan tafa hannuwana a kan ƙazamar riba da kika ci da jinin da kin zubar a cikinki.
-
11 Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru. 12 Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. 13 Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ 14 In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” 15 Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau.
-
8 Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi;
ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
-
7 Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa,
cin hanci kuma yakan lalace hali.
-
15 Shi da yake tafiya cikin adalci
yana kuma magana abin da yake daidai,
wanda yake ƙin riba daga cuta
yana kuma kiyaye hannunsa daga karɓan cin hanci,
wanda yake hana kunnuwansa daga ƙulla kisa
ya kuma rufe idanunsa a kan tunanin aikata mugunta,
16 shi ne mutumin da zai zauna a bisa,
wanda mafakarsa za tă zama kagarar dutse.
Za a tanada abincinsa, kuma ruwa ba zai kāsa masa ba.
-
23 Masu mulkinki ’yan tawaye ne,
abokan ɓarayi;
dukansu suna ƙaunar cin hanci
suna bin kyautai.
Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a;
ba sa taimakon gwauruwa.
24 Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki,
Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta,
“Kai, zan sami hutu daga maƙiyana
in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.
-
34 Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya,
wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.
35 Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;
cikinsu yana cike da ruɗami.”
-
14 Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi,
kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
-
12 Gama na san yawan laifofinku
da kuma girman zunubanku.
Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci
kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.
-
25 “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.”
Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
-
1 Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki. 2 Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro. 3 Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”
4 Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”
5 Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.”
Suka ce, “I, shi ne shaida.”
-
17 Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci. 18 Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.
-
7 Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”
-
4 Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo
amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.
-
18 Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus. 19 Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
-
6 Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. 7 Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. 8 In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. 9 Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. 10 Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
-
27 Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa,
amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
-
5 Sai shugabannin Filistiyawa suka tafi wurinta suka ce, “Ki yi ƙoƙari ki ga ko za ki rarrashe shi yă nuna miki asirin ƙarfinsa da yadda za mu iya shan ƙarfinsa don mu ɗaura shi mu yi nasara a kansa. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu ɗari ɗaya na azurfa.”
-
9 In ya gamshi sarki, bari a yi doka, don a hallaka su, zan kuma sa talenti dubu goma na azurfa a cikin ma’ajin fada saboda mutanen da suka aikata wannan sha’ani.”
-
9 Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub,
ku masu mulkin gidan Isra’ila,
ku da kuke ƙyamar gaskiya,
kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya;
10 kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini,
Urushalima kuma ta wurin mugunta.
11 Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne,
firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su,
annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi.
Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa,
“Ba Ubangiji yana tare da mu ba?
Ba bala’in da zai zo mana.”
12 Don haka, saboda ku,
za a nome Sihiyona kamar gona,
Urushalima kuma ta zama tarin juji,
tudun haikali kuwa zai zama kurmin ƙayayyuwa.
-
24 Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 25 Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.” 26 A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
27 Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.
-
3 Dukan hannuwansu sun gwaninta wajen yin mugunta;
shugabanni suna nema a ba su kyautai,
alƙalai suna nema a ba su cin hanci,
masu iko suna faɗar son zuciyarsu,
duk suna ƙulla makirci tare.
-
14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.
-
3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”
Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”
5 Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.
6 Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” 7 Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8 Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. 9 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, 10 suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
-
10 Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”
11 Amma na ce, “Ya kamata mutum kamar ni yă gudu? Ko kuwa ya kamata wani kamar ni yă shiga cikin haikali don yă ceci ransa? Ba zan tafi ba!” 12 Na gane cewa Allah bai aike shi ba, ya yi annabci a kaina domin Tobiya da Sanballat sun yi hayarsa ne. 13 An yi hayarsa don yă sa in ji tsoro in yi zunubi ta yin haka, sa’an nan za su ba ni mugun suna, su wofinta ni.
-
16 Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa
yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
-
18 Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki;
kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
-
18 Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, 19 ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”
20 Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi! 21 Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba. 22 Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka. 23 Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”
24 Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”
-
21 Nuna sonkai ba shi da kyau,
duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.
-
10 “Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba. 11 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya? 12 In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?
13 “Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”
14 Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki. 15 Ya ce musu, “Ku ne masu mai da kanku marasa laifi a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abu mai daraja a gaban mutane, abin ƙyama ne a gaban Allah.
16 “An yi shelar Doka da Annabawa har zuwa lokacin Yohanna. Tun daga lokacin nan, bisharar mulkin Allah ne ake wa’azinta, kowa kuma yana ƙoƙarin kutsa kai ya shiga.
-
35 “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. 36 Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
-
23 Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba,
da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
-
33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.
-
19 Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”
-
15 In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi.
-
8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.
Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa
shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai
ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
-
2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
-
8 Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.
-
25 Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
-
18 Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.
19 Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba. 20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.
21 Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa. 22 Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”
Shows Read in context, Share and Copy.