88 Bible Verses About God's Will

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bible Verses About God's Will
  1. 1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu,

    Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.

    2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

    3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

    11 A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12 Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. 13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

  2. 1 Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. 2 Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.

    3 Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa. 4 Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5 haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.

  3. 3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

  4. 16 Ku riƙa farin ciki kullum; 17 ku ci gaba da yin addu’a; 18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

  5. 6 Gama a cikin Nassi an ce,

    “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,

    zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,

    wanda kuma ya dogara gare shi

    ba zai taɓa kunyata ba.”

    7 A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,

    “Dutsen da magina suka ƙi

    ya zama dutsen kusurwar gini,

    8 kuma,

    “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe

    kuma fā ne da yake sa su fāɗi.”

    Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

    9 Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. 10 Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

    11 Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. 12 Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

    13 Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, 14 ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. 15 Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. 16 Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. 17 Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

    18 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma. 19 Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. 20 Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah.

  6. 38 Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni. 39 Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe. 40 Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”

  7. 15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.

    21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.

  8. 27 Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.

    28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.

    31 Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

  9. 9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

    “ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

    a tsarkake sunanka,

    10 mulkinka yă zo

    a aikata nufinka a duniya

    kamar yadda ake yi a sama.

    11 Ka ba mu yau abincin yininmu.

    12 Ka gafarta mana laifofinmu,

    kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

    13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

    amma ka cece mu daga mugun nan. ’

  10. 39 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

    40 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? 41 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

    42 Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

  11. 10 Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri. 11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. 13 Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. 14 Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”

  12. 13 “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. 14 Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.

    15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17 Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 18 Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 19 Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20 Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

    21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

  13. 1 Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum 2 da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3 Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4 wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya.

  14. 9 Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

  15. 7 Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo,

    kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.

    8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna;

    dokar tana cikin zuciyata.”

  16. 16 Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa.

  17. 13 Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” 14 Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. 15 A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.”

  18. 15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

  19. 10 Ka koya mini in yi nufinka,

    gama kai ne Allahna;

    bari nagarin Ruhunka

    yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

    11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina;

    a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala.

  20. 34 Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.

  21. 5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. 6 Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. 7 Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. 8 Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.

  22. 20 Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, 21 yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.

  23. 35 Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. 36 Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”

  24. 1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, 2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. 3 Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. 4 Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

    5 A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

    6 Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,

    bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

    7 amma ya mai da kansa ba kome ba,

    yana ɗaukan ainihin surar bawa,

    aka yi shi cikin siffar mutum.

    8 Aka kuma same shi a kamannin mutum,

    ya ƙasƙantar da kansa

    ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,

    mutuwar ma ta gicciye!

    9 Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri

    ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

    10 don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,

    a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

    11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,

    don ɗaukakar Allah Uba.

  25. 5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

    kada kuma ka dangana ga ganewarka;

    6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

    zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

  26. 21 Da yawa ne shirye-shiryen zuciyar mutum,

    amma manufar Ubangiji ce takan cika.

  27. 9 Ku tuna da abubuwan da suka riga suka faru, waɗannan na tun dā;

    ni ne Allah, kuma babu wani;

    ni ne Allah kuma babu wani kamar ni.

    10 Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko,

    daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba.

    Na ce nufina zai tabbata,

    kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.

    11 Daga gabas na kira tsuntsun da yake farauta;

    daga can ƙasa mai nesa, wani mutumin da zai cika nufina.

    Abin da na riga na faɗa, shi zan sa ya faru;

    abin da na shirya, shi zan aikata.

  28. 30 Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni. 31 Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, 32 don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. 33 Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.

  29. 19 Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

  30. 30 Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.

  31. 7 Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina. 8 Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali. 9 An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. 10 Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya. 11 Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. 12 A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi. 13 Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

  32. 14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.” 15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, 16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.

  33. 10 Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala,

    kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi,

    zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai,

    nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.

  34. 33 Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da ’yan’uwana?”

    34 Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da ’yan’uwana! 35 Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”

  35. 17 Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.

  36. 1 Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,

  37. 3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku. 4 Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu,

  38. 35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.

    36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37 Gama,

    “A cikin ɗan lokaci kaɗan,

    mai zuwan nan zai zo

    ba kuwa zai yi jinkiri ba.

    38 Amma,

    “Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.

    In kuwa ya ja da baya,

    ba zan ji daɗinsa ba.”

    39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.

  39. 5 Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka. 6 Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba. 7 Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.

    8 “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar. 9 Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.

  40. 9 Allah, wanda nake bauta wa da dukan zuciyata cikin wa’azin bisharar Ɗansa, shi ne shaidata a kan yadda kullum ina tunawa da ku 10 cikin addu’o’ina a kowane lokaci; ina kuma addu’a cewa a ƙarshe in Allah ya yarda hanya za tă buɗe mini in zo wurinku.

  41. 33 Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!

    Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,

    hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!

    34 “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?

    Ko kuwa yă ba shi shawara?”

    35 “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,

    da Allah zai sāka masa?”

    36 Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.

    Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.

  42. 4 Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa,

    har ma da mugaye domin ranar masifa.

  43. 6 Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;

    ku yi kira gare shi tun yana kusa.

    7 Bari mugu ya bar irin halinsa

    mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

    Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

    ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

    8 “Gama tunanina ba tunaninku ba ne,

    yadda kuke yin abubuwa ba yadda nake yin abubuwa ba ne,”

    in ji Ubangiji.

    9 “Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

    haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

    tunanina kuma dabam da naku.

    10 Kamar yadda ruwan sama da dusar ƙanƙara suke

    saukowa daga sama,

    ba sa komowa

    ba tare da sun jiƙe duniya

    sun kuma sa su yi ’ya’ya su kuma yi toho,

    don su ba da iri ga mai shuki da kuma abinci ga mai ci,

    11 haka maganata da take fitowa daga bakina.

    Ba za tă koma gare ni wofi ba,

    amma za tă cika abin da nake so

    ta kuma cika abin da na aike ta tă yi.

    12 Za ku fita da farin ciki

    a kuma bi da ku da salama;

    duwatsu da tuddai

    za su ɓarke da waƙa a gabanku,

    dukan itatuwan jeji kuma

    za su tafa hannuwansu.

    13 A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro,

    a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro.

    Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi,

    madawwamiyar alama ce,

    wadda ba za a datse ba.”

  44. 8 Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

    Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

    shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

    ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

  45. 29 Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

    32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama. 33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.

  46. 35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya. 36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”

    37 Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’ 38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40 Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”

  47. 7 Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi

    na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  48. 10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai;

    yakan wofintar da manufofin mutane.

    11 Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada,

    manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.

  49. 28 Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”

    29 Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’ 31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

  50. 6 Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya. 7 Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. 8 Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. 9 Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” 10 Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.

  51. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,

    “Ba idon da ya taɓa gani,

    ba kunnen da ya taɓa ji,

    ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin

    abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

    10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

    Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.

  52. 24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. 25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. 27 Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.

  53. 8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, 9 wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, 10 amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. 11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. 12 Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.

    13 Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. 14 Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.

  54. 3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

  55. 14 Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu.

  56. 11 “Ya Ubangijinmu da Allahnmu,

    ka cancanci ɗaukaka da girma da iko,

    domin ka halicci dukan abubuwa,

    kuma ta wurin nufinka aka halicce su

    suka kuma kasance.”

  57. 20 Kun yi niyya ku yi mini lahani, amma Allah ya nufe wannan ya zama alheri don yă cika abin da yanzu yake faruwa, ceton rayuka masu yawa.

  58. 43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’ 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

  59. 10 Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. 11 Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. 12 Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah 13 ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

  60. 14 Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15 Gama ya ce wa Musa,

    “Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,

    zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”

    16 Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17 Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.” 18 Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.

    19 Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20 Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ” 21 Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?

    22 Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23 Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24 har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai?

  61. 1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,

    2 Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana.

    Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

  62. 5 In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi. 6 Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.

  63. 35 Dukan mutanen duniya

    ba a bakin kome suke ba.

    Yakan yi abin da ya gamshe shi

    da ikokin sama

    da kuma na mutanen duniya.

    Babu mai hana shi

    ko yă ce masa; “Me ka yi?”

  64. 50 Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”

  65. 22 Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’

  66. 17 To, kai, da kake kiran kanka mutumin Yahuda; in kana dogara ga doka kana kuma taƙama da dangantakarka da Allah; 18 in ka san nufinsa ka kuma amince da abin da yake mafifici domin an koyar da kai bisa ga doka; 19 in ka tabbata cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga waɗanda suke cikin duhu, 20 mai koyar da masu wauta, malamin jarirai, domin a cikin dokar ce akwai sani da gaskiya 21 to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata? 22 Kai da kake cewa wa mutane kada su yi zina, kana yin zina? Kai da kake ƙyamar gumaka, kana wa haikali fashi? 23 Kai da kake taƙama da doka, kana nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin karya dokar? 24 Kamar yadda yake a rubuce, “Ana saɓon sunan Allah a cikin Al’ummai saboda ku.”

  67. 1 Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. 2 Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.

    4 Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna. 5 Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,

    “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,

    kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

    6 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

    yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

    7 Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

  68. 2 “Na san cewa za ka iya yin dukan abubuwa;

    ba wanda zai iya ɓata shirinka.

  69. 24 Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji!

    Cikin hikima ka yi su duka;

    duniya ta cika da halittunka.

  70. 23 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

    “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa

    ko mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa

    ko mai arziki ya yi fariya da arzikinsa,

    24 amma bari shi wanda yake taƙama ya yi taƙama da wannan,

    cewa ya fahimci ya kuma san ni,

    cewa ni ne Ubangiji, wanda yake yin alheri,

    gaskiya da kuma adalci a duniya,

    gama a waɗannan ne nake jin daɗi,”

    in ji Ubangiji.

  71. 25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26 I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.

    27 “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.

  72. 16 Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. 17 Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.

  73. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15 Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

  74. 1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2 “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.

  75. 11 Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”

  76. 20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa,

    ku jarumawa masu yi masa aiki,

    waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.

    21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama,

    ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.

  77. 6 Ubangiji yana yin abin da ya ga dama,

    a sammai da kuma a duniya,

    cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.

  78. 24 Ubangiji ne yake bi da matakan mutum,

    Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?

  79. 1 A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne

    wanda yake bi da shi duk inda ya so.

  80. 31 Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.

  81. 34 “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”

  82. 13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. 14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.

  83. 36 “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”

  84. 27 Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. 28 Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.

  85. 48 Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.

  86. 5 Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so.

  87. 14 Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.

  88. 13 Amma dole kullum mu gode wa Allah dominku, ’yan’uwa waɗanda Ubangiji ya ƙaunace, domin daga farko Allah ya zaɓe ku don a cece ku ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu da kuma ta wurin gaskatawa da gaskiya. 14 Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi.