69 Bible Verses About Hope
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
-
1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
-
18 A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. 19 Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. 20 Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege 21 cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah.
22 Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. 23 Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. 24 Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? 25 Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
-
12 Kuma Ishaya ya ce,
“Tushen Yesse zai tsiro,
wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai;
al’ummai za su sa bege a gare shi.”
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
-
5 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,
wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi
wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.
6 Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;
ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.
Za su zauna a busassun wuraren hamada,
a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.
7 “Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,
wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.
8 Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa
wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.
Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;
ganyayensa kullum kore suke.
Ba shi da damuwa a shekarar fări
ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
-
18 Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, “Haka zuriyarka za tă zama.” 19 Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. 20 Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, 21 yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari. 22 Shi ya sa, “aka lissafta adalci a gare shi.”
-
3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4 da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5 ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.
-
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa,
a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
19 don yă cece su daga mutuwa
ya bar su da rai a lokacin yunwa.
20 Muna jiran Ubangiji da bege;
shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki,
gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji,
ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
-
11 Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu ce, “A’a” ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13 yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi, 14 wanda ya ba da kansa dominmu don yă fanshe mu daga dukan mugunta yă kuma tsarkake wa kansa mutanen da suke nasa, waɗanda suke marmarin yin abin da yake nagari.
-
15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
-
2 Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. 3 Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
-
17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa. 18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu. 19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule, 20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.
-
16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.
-
8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
-
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu.
-
23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
-
5 Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. 6 Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.
-
13 Yanzu kam abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, bege, da kuma ƙauna. Sai dai mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
-
4 Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.
-
28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki,
amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
-
11 Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. 12 Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.
-
10 Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. 11 In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!
12 Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan. 13 Mu ba kamar Musa ba ne, wanda ya rufe fuskarsa da lulluɓi, don kada Isra’ilawa su ga ƙarewar ɗaukakan nan mai shuɗewa. 14 Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi.
-
4 Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.
-
1 Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. 2 Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan.
-
11 Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12 Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. 13 Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
14 Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15 Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu. 16 A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah.
-
9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi. 10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba. 11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku. 12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.
-
7 Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,
gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa
kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.
8 Shi kansa zai fanshi Isra’ila
daga dukan zunubansu.
-
24 Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa,
dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.
-
3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna,
ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.
4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa;
a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.
-
6 Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.”
-
19 In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.
-
11 Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa?
Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba?
12 Yayinda take girma ba a yanka ta,
takan mutu da sauri fiye da ciyawa.
13 Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah;
waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.
14 Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi;
abin da yake dogara a kai yanar gizo ce.
15 Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi,
sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba.
-
10 Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.
-
18 Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani 19 (gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.
20 Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba, 21 shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa,
“Ubangiji ya rantse,
ba kuwa zai canja zuciyarsa ba,
‘Kai firist ne na har abada.’ ”
22 Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
-
13 Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14 Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.
-
7 “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema?
Begena yana a gare ka.
-
14 Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya;
zan yabe ka sau da sau.
-
17 Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. 18 Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
-
11 Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa,
waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
-
12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
-
5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,
ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
-
17 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi,
amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
18 Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
-
20 An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21 Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
-
18 Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,
ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
-
9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki;
jikina kuma zai zauna lafiya,
10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba,
ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
-
2 A gare ka na dogara, ya Allahna.
Kada ka bari in sha kunya,
ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
3 Ba wanda yake sa bege a gare ka
da zai taɓa shan kunya,
amma za su sha kunya
su da suke tayarwa babu dalili.
-
11 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?
Me ya sa ka damu a cikina?
Ka dogara ga Allah,
gama zai sāke yabe shi,
Mai Cetona da kuma Allahna.
-
5 Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai;
dogarata kan zo daga gare shi ne.
-
5 Zan jira Ubangiji, raina zai jira,
kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.
-
4 Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!
5 Gama rayayyu sun san za su mutu,
amma matattu ba su san kome ba;
ba su da wata lada nan gaba
an manta da su ke nan gaba ɗaya.
6 Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu,
da kuma kishinsu tuni sun ɓace;
ba za su taɓa zama sashen
wani abin da yake faruwa a duniya ba.
-
16 Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona
tsawa kuma daga Urushalima;
duniya da sararin sama za su yi rawan jiki.
Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa,
mafaka ga mutanensa Isra’ila.
-
26 Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna,
jikina kuma zai kasance da bege,
27 gama ba za ka bar ni cikin kabari ba,
ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
-
13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
-
18 Za ka zauna lafiya, domin akwai bege;
za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai.
19 Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro,
da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
-
8 Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi,
lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?
-
24 “In na dogara ga zinariya
ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’
25 in na yi fahariya don yawan dukiyata,
arzikin da hannuwana suka samu.
26 In na dubi rana cikin haskenta,
ko kuma wata yana tafiyarsa,
27 zuciyata ta jarrabtu gare su a ɓoye,
hannuna kuma ya sumbace su.
28 Waɗannan ma za su zama zunubin da za a shari’anta ke nan
don zai zama na yi wa Allah na sama rashin aminci.
-
19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru
da kuma yadda suka ƙara ƙina!
20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni;
kada ka bari in sha kunya,
gama na nemi mafaka daga gare ka.
21 Bari mutunci da adalci su tsare ni,
domin begena yana a kanka.
-
16 Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. 17 Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. 18 Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
-
18 Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki.
I, zan kuwa ci gaba da farin ciki, 19 gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata. 20 Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.
-
15 Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi;
yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
16 Saboda haka matalauta suna da bege,
rashin gaskiya kuma ta yi shiru.
-
13 In kabari ne begen da nake da shi kaɗai,
in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,
14 In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’
tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’
15 To, ina begena yake?
Wane ne zai iya ganin wani bege domina?
-
5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?
Me ya sa ka damu a cikina?
Ka dogara ga Allah,
gama zai sāke yabe shi,
Mai Cetona da kuma Allahna.
-
11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;
Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;
ba ya hana kowane abu mai kyau
wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
-
4 ba zai kāsa ko ya karai ba
sai ya kafa adalci a duniya.
Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
-
13 Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,
duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya.
Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura
domin sun yashe Ubangiji,
maɓulɓular ruwan rai.
-
18 Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare
da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
-
21 Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22 Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23 Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
-
7 Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji,
ina sauraron Allah Mai Cetona;
Allahna kuwa zai ji ni.
-
21 Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
-
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”
Shows Read in context, Share and Copy.